23/08/2026
An Horas da ’Yan Jarida Kan Rahoton Rikice-Rikice a Sokoto
Daga Hadiza Haliru Muhammad, Sokoto
An gudanar da horo ga ’yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta a Jihar Sokoto, kan yadda za su riƙa rahoton rikice-rikice cikin taka-tsantsan tare da tabbatar da sahihancin bayanan da suke yaɗawa.
Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU), da ƙungiyoyin jin ƙai na Action Against Hunger, International Alert da Save the Children Initiative (STCI), tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Sokoto, ne s**a shirya horon.
An mayar da hankali ne kan yadda kafafen yaɗa labarai za su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya, musamman a rahotannin da s**a shafi tsaro, rikice-rikice da sauran abubuwan da ka iya haifar da tashin hankali a tsakanin al’umma.
Shugaban NUJ na Jihar Sokoto, Comrade Usman Muhammad Binji, ya ce horon zai taimaka wa ’yan jarida wajen inganta aikin da suke yi, musamman wajen rahoton matsalolin tsaro cikin ƙwarewa da sanin ya kamata.
Shi ma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, wanda ya wakilci Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya yaba da shirin, yana mai cewa irin wannan horo na da muhimmanci wajen ƙara wa ’yan jarida da masu amfani da kafafen sada zumunta fahimta kan nauyin da ke kansu.
A nasa ɓangaren, Alhaji Sidi A. Sidi, Shugaban Majalisar Ulama ta Jihar Sokoto, ya jaddada cewa sahihin bayani da yadda ake yaɗa shi na da matuƙar tasiri wajen kare zaman lafiya.
Farfesa Tukur Muhammad Baba, wanda ya gabatar da kasida a wajen horon, ya ce ɗan jarida ya kamata ya kasance mai gaskiya, adalci da rashin son rai, tare da tabbatar da sahihancin labari kafin ya watsa shi.
Ya kuma yi gargaɗin cewa karkatar da ma’anar magana ko yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba na iya haifar da mummunan sakamako, musamman idan batun ya shafi rikici ko tsaro.
Shi ma Dr. Abdullahi Muhammad ya yi bayani kan illolin fake news, misinformation da malinformation, yana mai cewa yaɗuwar bayanan ƙarya na iya ƙara ruruta rikici da raba kan al’umma.
A yayin taron, wasu daga cikin manyan kafafen yaɗa labarai da s**a haɗa da Blueprint, NAN, Channels TV da VON, sun kuma bayyana dabarun da suke amfani da su wajen tantance sahihancin bayanai da isar da ingantattun labarai ga jama’a.
Mahalarta taron sun bayyana muhimmancin ci gaba da irin waɗannan horo domin ƙara wa ’yan jarida da masu amfani da kafafen sada zumunta ƙwarewa wajen yaɗa bayanai cikin gaskiya da taka-tsantsan, musamman a jihohin da ke fuskantar matsalolin tsaro.
Me kuke ganin ya kamata ’yan jarida da masu amfani da kafafen sada zumunta su fi mayar da hankali a kai yayin rahoton rikice-rikice domin kada labari ya ƙara ruruta tashin hankali?
Ku ci gaba da bibiyar shafin AGC-HAUSA domin samun sahihan labarai da muhimman bayanai daga Najeriya da sauran sassan duniya.