02/06/2022
Labari da dumi duminshi
Kwamitin APC ta gano Takardun Bogi na Tinubu
....​Kwamitiin tantance dantakara karkashin jam'iyar APC, ta gano ashe takardan kammala karatun tinubu na bogi ne!
A wata sanarwa da daya daga cikin masu kula da tantance dantakaran shugaban kasa na jam'iyyar APC, wato Sagir Mai Iyali. Ya yi kira sauran 'Yayan kwamitin jam'iyyar da lallai ta dakatar da Bola Ahmad Tinubu daga fitowa dantakaransu karkashin jam'iyyar APC din."
Bugu da kari majiyar ta ALFIJIR HAUSA ta jiyo cewa, an iya samun wasu 'Yayan kwamitin tantance dantakaran da su ma sun goyi bayan hakan, koba komai saboda jin kunya a nan gaba."
Shugaban kwamitin masu tantance dantakaran shugaban kasan a jam'iyyar APC, mista. John Odigie Oyegun, tare da mataimakinsa mai iyali sun ce Bola tinubu bai kammala karatu a makaranta na gaba da sakandiriba, kamar yadda aka ce tinubun wai ya kammala karatunsa a jami'ar Chicago, shugaban tantance dantakaran shugaban kasar yace farfagandace kawai, sakamakon kammala makarantan ta karyace.
Bisani dai Yayan kungiyar kwamitin na jam'iyyar APC, sun nemi da tinubu da ya janye aniyarsa na shiga jerin wadanda zasu fito a domim goge raini a zaben fidda gwani da zai gudana 7/June/2022.
A cigaba da Cewar masu ruwa da tsaki a tafiyar tantancewa, sunce duk da sun San tinubu din ya sayi tikitin tsayawa takaran shugaban kasa a baya, a don haka suna kiransa da babban murya daya janye.