Autan nanah Fatima

Autan nanah Fatima Kaugama

Permanently closed.
13/07/2022

Malam naji dadi da wannan taqaitaccen tarihi na
fiyayyan halitta Annabi muhammadu (s.a.w) mlm
Allah yasaka maka da mafificin Alkhairi

13/07/2022

Annabi(saw) ya kansace abin koyi ne; a rikon
amana, ikhlasi, gaskiya, cika al-kawari, kyawawan
halaye, girma, kyawawan dabi’u, baiwa, ilmi, hakuri,
rangawame, afuwa, sadaukantaka, tsentseni,
takawa, zuhudu, baiwa, adalci, kaskan da kai,
jihadi…
Jikinsa(saw) ya kasance kololuwa wajen kyau,
daidaito, dacewa… kuma fuskarsa kamar wata ne
mai haske da ya cika, zuciyarsa da ruhinsa sun kai
matuka wajen kamala, mafi kamalar halaye, ladabi,
dabi’a… sunnarsa tana haske kamar rana a tsaka-
tsakinta.
Atakaice; Annabi(saw) ya tattara dukkan wata dabi’a
mai kyau, girma, daukakada, ilimi, adalci, takawa,
iya tafiyar da al’amuran duniya da na lahira,
wadanda babu wani mahaluki da yake da irinsu.
Wannan shine Annabin musulmi kuma wannan shine
addinin Musulunci, addininsa(saw) shine mafificin
addinai, littafinsa shi ne mafifcin littattafai, domin
shi: “Barna ba ta iya zo masa ta gabansa da ta
bayansa, abin saukarwa ne daga mai hikima abin
yabo”.
Allah(swt) ya karawa Annabi Muhammad(saw)
daraja da dauka, ya samu a cetonsa, ya biya mana
bukatunmu; albarkacinsa(saw) da Ahlul-bayt(as)!!

13/07/2022

Mutuwa Mai Zafin Gaske; Tun lokacin da aka aiko
Annabi(saw) da sako har ya tafi daga duniya wahayi
yana sauka gareshi kuma Jibrilu(as) shi ne ake aiko
masa daga wajen Ubangiji(swt) a hankali a hankali
har littafin Qur’ani ya ciki a cikin shekaru ashirin da
uku, sai Manzo(S.A.W) ya yi umarni da a hada shi
kamar yadda yake a yau din nan.
Manzo(saw) ya kasance yana tsara wa musulmi
duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da
hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada
da biyayya da mu’amala da zamantakewa da siyasa
da tattalin arziki da sauransu.
Bayan cikar addini da na Imam Ali(as) a matsayin
khalifansa na farko, sai Allah ya saukar da ayar: “A
yau ne na kammala mukuaddininku, na cika ni’imata
gareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne
addini”. Sai Annabi(saw) ya yi rashinlafiya mai
sauki, sai dai yayi tsanani har sai da ya hadu da
Ubangijinsa a 28 ga watan safar na 11H.
Kuma Imam Ali(as) shi ne ya yi masa wanka da
sallah da binne shi a dakinsa a Madina inda
kabarinsa yake yanzu.

13/07/2022

Ba wanda s**a yi imani da shi sai mutane kalilan,
na farkonsu Imam Ali(as), sannan sai matarsa
KHadizah(as) sannan sai khalifa Abubakar…
Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi
hijira zuwa Madina, yayin da s**a yi yawa sai
karfinsu ya dadu kuma s**a samu koyarwa daga
Manzon Allah(saw) da shari’arsa mai sauki mai
hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da
mutumtaka da wayewa da cigaba a Madina har
s**afi dukkan duniya da addini na sama da
wadanda ba na sama ba.
An samu yakoki masu yawa a Madina; dukkanninsu
sun zama domin kare kai ne daga makiya mushrikai
da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan
Musulmai, kuma Annabi(saw) a kowne lokaci yana
zabar bangaren sulhu da zaman lafiya ne da
rangwame.
Don haka ne ma adadin wadanda ake kashewa daga
bangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yakokinsa
tamanin da wani abu, wato; wadanda aka kashe na
musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu
daya da dari hudu ba.

13/07/2022

An aiko Annabi Muhammad(saw) da sako a 27 ga
Rajab bayan yana dan shekara 40 yayin da Jibril(as)
ya sauka gareshi daga wurin Allah(swt) yana kogon
Hira wanda yake dutse ne a Makka ya ce masa ka
karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na
surar Alaq.
Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci
mai alfarma na Makka a lokacin akwai jama’a masu
yawa a wurin da ake taruwa ya isar da sakon Allah
na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi; yana
cewa da su: “Ku ce babu abin bauta sai Allah ku
rabauta”.
A lokacin tunda mutanen Makka mushrikai ne, kuma
suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna
tsoron maslaharsu sai s**a rika yi masa isgili suna
yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk lokacin
ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen
cutar da shi har ya ce; “Ba a cutar da wani Annabi
ba kamar yadda aka cutar da ni”.

13/07/2022

Tarihin Shahadarsa (wafatinsa): 28 Safar 11 H.
Wajan da ya yi shahada: Madina.
Inda aka binne shi: Madina a dakinsa madaukaki,
mai alfarma.
Annabi Muhammad(saw) shine karshen Annabawa
(as) kuma addininsa shine Musulunci mai shafe duk
wani addini kuma shari’arsa zata wanzu har zuwa
Qiyama kuma ita kadai ce shari’ar da zata arzuta
mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa
har zuwa karshen rayuwar Duniya da cigaban
rayuwar Lahira.
Annabi Muhammad(saw) abin koyi ne ga dukkan
Duniya baki daya, dukkan mutanen duniya idan suna
son alkhairi ga kawukansu; to dole ne su bi
tarfarkinsa(saw); su yi koyi da kyawawan halyensa
(saw) da kuma sanin tarihinsa da siffofinsa(saw):
Annabi Muhammad(saw) dan Abdullah da Amina,
an haife shi a Makka ranar juma’a goma sha
bakwai ga watan Rabi’ul-awwal, bayan bullowar Al-
fijir a shekarar giwa…

13/07/2022

Matansa: KHadija ‘yar Khuwailid(as) ita ce matarsa
ta farko. Sauran su ne; Saudatu ‘yar Zami’a, A’isha
‘yar Abubakar, Gaziyya ‘yar Dudan(Ummu Sharik),
Hafsa yar Umar, Ramla ‘yar Abu Sufyan (Ummu
Habibia), Ummu Salama ‘yar Abu Umayya, Zainab
‘yar Jahash, Zainab ‘yar Huzaima, Maimuna ‘yar Al-
Haris, Juwairiyya ‘yar Al Haris, Safiyya ‘yar Huyayyi
dan Akhdab.
‘Ya’yansa: Abdullah, Al-Qasim, Ibrahim, Fatima(as).
A wani kaulin akwai Zainab, Ruqayya da Ummu
Kulsum.
Ammominsa maza: 9 ne, su ‘ya’yan Abdul-Mudallib
ne: Al-haris, Zubair, Abu Talib, Hamza, Al-Gaidak,
Dirar Al-muqawwam, Abu Lahab da Abbas…
Ammominsa mata: Su 6 ne daga iyaye mata daban-
daban sune: Amima, Ummu Hakima, Barra, Atika,
Safiyya, Arwa…
Khadiminsa: Anas dan Malik…
Mawakinsa: Hassan dan Sabit, Abdullahi dan
Rawahata, Ka’abu dan Malik…
Ladanansa: Bilal Al- Habashi, Abdullahi dan Ummul-
Maktum da Sa’ad Al-kirdi

13/07/2022

Koyarwar sakonsa: ya zo don daidaito tsakanin
dukkan halitta da ‘yan’uwantaka da rangwame,
sa’annan ya kafa shari’a madaukakiya da dokoki na
adalci da ya karbo daga wajan Allah(swt), su kuma
Musulmi s**a karba daga gare shi.
Mu’ujizozinsa: Mu’ujizarsa madauwamiya ita ce
Qur’ani, amma wadanda s**a faru a farkon
Musulunci suna da yawa; ba zasu kirgu ba, misali,
tsagewar wata.
Kiransa: Ya kira mutane zuwa ga Tauhidi a Makka a
boye shekara 3, ya kuma kira su a bayyane shekara
10.
Hijirarsa: ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a
farkon watan Rabi’ul Auwal, bayan shekara 13 daga
aikosa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga
kafirai; gare shi da kuma Sahabbansa.
Yakokinsa: Allah ya yi wa Manzo(saw) izinin yakar
mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi dauki
ba dadi da su a wurare da yawa da mafi girmansu
sune: Badar, Uhud, Al-khandak(Ahzab), Khaibar,
Hunaini…

13/07/2022

NASABARSA TA BANGAREN MAHAIFIN SA:
Muhammad(saw) dan Abdullahi, dan Abdul-
Mutallib, dan Hashim dan Abdul-Manaf, dan
Kusayyi dan Kilabi… nasabarsa(saw) madaukakiya
tana tukewa zuwa ga Annabi Adam(as) a tsatson
masu sujadah da tsarki.
Nasabarsa ta bangaren Mahaifiyarsa: Ita ce Aminah
‘yar Wahabi, dan Abdul-Manaf dan Zuhrata dan
Kilabi… nasabarsa ta fuskar mahaifinsa da
mahaifiyar tahadu wajen Kilab zuwaga Annabi Adam
da Hauwa(as).
Wadanda s**a reneshi: Abdul-Mulib, Halimah As-
Sa’adiyya, da Abu Talib.
Alkunyarsa: Abul-Qasim, Abu Ibrahim.
Lakabinsa: Al-amin, Al-mustafah…
Sunayensa da s**a zo a cikin Kur’ani mai girma:
Khatamin-nabiyyin, Al-ummi, Al-muzzammil, Al-
muddassir, An-nazir, Al-mubin, Al-karim, An-nur,
Anni’ima, Ar-rahma, Al-abdu, Ar-ra’uf, Ar-rahim, As-
shahid, Al-mubasshir, An-nazir, Ad’da’i…
Tarihin haihuwarsa: An haifi Monzon Allah(saw) a
Ranar Jumu’ah, 17 Rabi’ul Auwal Shekarar Giwa
(571 M) (bisa mash’hurin zance daga Ahlul-Bayt
(as) (amma a wata ruwayar an haifeshi(saw) ranar
Litinin 12 Rabi’u-auwal).
Inda aka haifesa: Makka.
Tambarin zobensa: Muhammadur-Rasulullah!
Tsawon rayuwarsa: shekaru 63.
Tsawon lokacin Annabtarsa: shekaru 23.
Aikoshi: An aiko shi a Makka, 27 Rajab; yana dan
shekara 40.

13/07/2022

TAKAITACCEN TARIHIN ANNABI MUHAMMAD
(SAW):
-----------------------------
Cikin shirin: MU SAN ADDINI
Darasi kan : TARIHIN ANNABI MUHAMMADU
(s.a.w)
Mako na: (30)
-----------------------
Tare da Mal Aliyu Muhammad Bajoga
Masu bibiyan wannan kafa mai albarka Labarai Daga
Bauchi, ina mana sallama irin ta addinin musulunci
Aslamu alaikum, a wannan mako muna dauke muku
da takaitaccen tarihin Annabi Muhammadu (s.a.w)
ne.

11/07/2022

AN KARBO
DAGA ABU HURAIRATA R.A.WATA RANA YA
SHIGA KASUWA...YACE WA MUTANE YA
AKAI NA GANKU NAN BAYAN GASHI CAN
ANA RABON GADON MANZAN ALLAH
S.A.W.A MASALLACI.???SAI JAMAA S**A
WATSE DAGA KASUWA S**A NUFI
MASALLACI...S**A JE BASU GA ANA RABA
KOMAI BA...SAI S**A CE YA ABA
HURAIRATA MUFA BA WANI KAYAN GADO
DA MUKA GA ANA RABAWA A
MASALLACI...SAI YACE MUSU TO ME KUKA
GANI..??? SAI S**A CE...MUN DAI GA WASU
MUTANE SUNA ZIKIRIN ALLAH DA KARATUN
ALQURANI....SAI YACE...TO AI SHI NE
GADON NASA DA AKE RABAWA.....WANNAN
NE YASA NA MAQALEWA SHEHU TIJJANI
R.A.DOMIN GADON ANNABI YA KOYA
MIN.....KUMA BA A MAKANCE NAKE BINSA
BA... NASAN DAGA INDA YA
DAKKONI...NASAN INDA MUKE A YANZU
KUMA NASAN INDA ZAI KAINI....DAN HAKA
IN BAKAYI BAN GURI....BA GUDU BA JA DA
BAYA....

11/07/2022

KARBO
DAGA ABU HURAIRATA R.A.WATA RANA YA
SHIGA KASUWA...YACE WA MUTANE YA
AKAI NA GANKU NAN BAYAN GASHI CAN
ANA RABON GADON MANZAN ALLAH
S.A.W.A MASALLACI.???SAI JAMAA S**A
WATSE DAGA KASUWA S**A NUFI
MASALLACI...S**A JE BASU GA ANA RABA
KOMAI BA...SAI S**A CE YA ABA
HURAIRATA MUFA BA WANI KAYAN...
More

Address

Jigawa
Abuja
JIGAWA

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Autan nanah Fatima posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Autan nanah Fatima:

Share