Arewa Traders Associations

Arewa Traders Associations Arewa Traders Associations is an umbrella of all legitimate traders in the 19 State Northern Nigeria.

03/08/2026

Akuya ta kira ruwa

Ta cinye Naira ₦500, Mai Akuya dai tace ba ruwan ta, yanzu wa zai raba wannan rikicin tsakanin Yaron nan da Akuya? 😂

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN. Cikin alhini da jimami, muna sanar da rasuwar Alhaji Muhammad Hassan, wadda ya rasu...
30/07/2026

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN.

Cikin alhini da jimami, muna sanar da rasuwar Alhaji Muhammad Hassan, wadda ya rasu yanzu nan a Asibitin Koyarwa na University of Maiduguri Teaching Hospital (UMTH), Maiduguri.
Marigayin yaya ne ga Alhaji Adamu Hassan Ibrahim, National President na Arewa Traders Association.

Za a gudanar da sallar jana'izarsa gobe Jumma'a da misalin karfe 2:00 na rana, a Masallacin Umar bin Khattab, Bulumkutu, Maiduguri, In shaa Allah.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya yalwata masa rahama, Ya sa kabarinsa ya zama daga cikin lambunan Aljanna, Ya kuma sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Allah Ya bai wa iyalansa da 'yan uwansa haƙurin jure wannan babban rashi.

Ameen Ya Rabbal 'Alameen.

29/07/2026

The Arewa Traders Association visited Rt. Hon. James Abiodun Faleke at the TSG Headquarters in Abuja to present the concerns of Northern traders over what they described as inadequate attention and support from the Federal Government, despite the significant role they played in supporting the APC and President Bola Ahmed Tinubu during the 2023 general elections.

The delegation urged the government to prioritize policies and interventions that would improve the welfare of Northern traders and address the challenges affecting their businesses, rather than allowing their contributions and sacrifices to go unrecognized.

27/07/2026

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!

Cikin alhini da jimami ne muke sanar da rasuwar matar Malam Kamalu, ɗan'uwa ga Alhaji Adamu Hassan Ibrahim.

Za a gudanar da sallar jana'izarta a yau da misalin ƙarfe 1:00 na rana a birnin Maiduguri, in shaa Allah.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta mata, Ya jiƙanta da rahamarsa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarta. Allah Ya albarkaci zuriyarta da duk abin alherin da ta bari a baya.

Haka kuma muna roƙon Allah Ya ba mijinta, iyalanta, 'yan uwanta da duk masu alhini haƙuri da juriya na wannan babban rashi.

Allah Ya gafarta mata, Ya rahamsheta, Ya sa ƙarshenmu ya zama mai kyau. Ameen Ya Rabbal Alameen.

27/07/2026

Mu ɗan shaƙata da waƙar Arewa Traders Association, a taron horas da yan Kasuwa da aka gudanar a Women Development Centre Abuja.

26/07/2026

Bayanin wakilin Taj Bank a kan tsarin kasuwanci ta yaya riba ke ƙaruwa kuma yadda za a kiyaye asara da kuma ta'amuli da Banki mara Riba, a taron horas da yan Kasuwa da aka gudanar a Women Development Centre Abuja.

26/07/2026

Bayani a kan tsarin Jaiz Takaful Insurance daga Manajan Bankin a taron horas da yan Kasuwa da aka gudanar a Women Development Centre dake Abuja.

SHUGABANIN ƘUNGIYAR ƳAN KASUWAN AREWA TA ƘASA SUN KAI ZIYARA OFISHIN HON. JAMES ABIODUN FALEKEA jiya ne shugabannin Ƙung...
25/07/2026

SHUGABANIN ƘUNGIYAR ƳAN KASUWAN AREWA TA ƘASA SUN KAI ZIYARA OFISHIN HON. JAMES ABIODUN FALEKE

A jiya ne shugabannin Ƙungiyar Ƴan Kasuwan Arewa ta Ƙasa s**a kai ziyarar girmamawa zuwa ofishin Hon. James Abiodun Faleke, Shugaban Kwamitin Kuɗi na Majalisar Wakilai ta Tarayya (Chairman, House of Representatives Committee on Finance).

A yayin ziyarar, shugabannin ƙungiyar sun gabatar da muhimman ƙorafe-ƙorafe da s**a shafi harkokin kasuwanci da kuma ƙalubalen da ƴan kasuwa ke fuskanta. Sun bayyana cewa, duk lokacin da gwamnati ke tsara manufofi ko yanke muhimman shawarwari da s**a shafi tattalin arziƙi, ba a cika bai wa ƴan kasuwa damar ba da gudummawar ra'ayoyinsu ba, duk da kasancewarsu cikin manyan masu bayar da gudummawa wajen bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.

Har ila yau, shugabannin ƙungiyar sun jaddada cewa Ƙungiyar Ƴan Kasuwan Arewa ta Ƙasa na daga cikin ƙungiyoyin da s**a ba gwamnatin wannan ƙasa cikakken goyon baya da gudummawa, amma duk da haka ba a ba ta kulawa da muhimmancin da ta dace ba.

Da yake mayar da martani, Hon. James Abiodun Faleke ya yaba da ziyarar shugabannin ƙungiyar tare da gode musu bisa yadda suke fafutukar bunƙasa harkokin kasuwanci da ci gaban tattalin arziƙin ƙasa. Ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin inganta yanayin kasuwanci, kare muradun ƴan kasuwa, da samar da tsare-tsaren da za su amfani al'umma baki ɗaya.

Address

Utako By Abraham Plaza Beside ABC Park
Abuja
900108

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Traders Associations posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa Traders Associations:

Shortcuts

Share