22/08/2026
🕋 خُطْبَةُ حَجَّةِ الْوَدَاعِ — Hudubar Hajjin Bankwana
أَيُّهَا النَّاسُ، اسْمَعُوا قَوْلِي، فَإِنِّي لَا أَدْرِي لَعَلِّي لَا أَلْقَاكُمْ بَعْدَ عَامِي هَذَا فِي مَوْقِفِي هَذَا.
Ya ku mutane! Ku saurari maganata. Ban sani ba, wataƙila ba zan sake haɗuwa da ku a wannan wuri ba bayan wannan shekarar🥲
أَيُّهَا النَّاسُ، إِنَّ دِمَاءَكُمْ وَأَمْوَالَكُمْ وَأَعْرَاضَكُمْ عَلَيْكُمْ حَرَامٌ، كَحُرْمَةِ يَوْمِكُمْ هَذَا، فِي شَهْرِكُمْ هَذَا، فِي بَلَدِكُمْ هَذَا.
Ya ku mutane! Lallai jininku, dukiyoyinku da mutuncinku haramun ne a tsakaninku, kamar yadda wannan ranarku take mai alfarma, wannan watan naku yake mai alfarma, kuma wannan garinku yake mai alfarma Na Makka
أَلَا كُلُّ شَيْءٍ مِنْ أَمْرِ الْجَاهِلِيَّةِ تَحْتَ قَدَمَيَّ مَوْضُوعٌ.
Ku saurara! Duk wani al’amari na zamanin Jahiliyya an soke shi, ba shi da wani matsayi
🌹 Wasiyyar Annabi ﷺ game da mata
اسْتَوْصُوا بِالنِّسَاءِ خَيْرًا.
Ku yi wa mata wasiyya da kyautata musu
فَإِنَّمَا هُنَّ عَوَانٍ عِنْدَكُمْ، لَيْسَ تَمْلِكُونَ مِنْهُنَّ شَيْئًا غَيْرَ ذَلِكَ.
Lallai mata amana ne a hannunku ba ku da wani iko a kansu sai cikin abin da Allah Ya halatta
وَلَهُنَّ عَلَيْكُمْ رِزْقُهُنَّ وَكِسْوَتُهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ.
Kuma mata suna da hakkin samun abincinsu da tufafinsu cikin kyakkyawar mu’amala
وَلَكُمْ عَلَيْهِنَّ أَنْ لَا يُوطِئْنَ فُرُشَكُمْ مَنْ تَكْرَهُونَ.
Kuma kuna da haƙƙi a kansu cewa kada su bar waɗanda ba ku so su shiga gidanku cikin abin da ya shafi sirrin iyali
وَاسْتَوْصُوا بِالنِّسَاءِ خَيْرًا.
Saboda haka ku yi wa mata wasiyya da kyautatawa
🤲 Wasiyya da Littafin Allah
وَقَدْ تَرَكْتُ فِيكُمْ مَا لَنْ تَضِلُّوا بَعْدَهُ إِنِ اعْتَصَمْتُمْ بِهِ: كِتَابَ اللَّهِ.
Na bar muku abin da idan kuka riƙe shi sosai ba za ku ɓace ba Littafin Allah da sunna ta
🌍 Sakon da ya shafi dukkan Musulmi
أَلَا إِنَّ رَبَّكُمْ وَاحِدٌ، وَإِنَّ أَبَاكُمْ وَاحِدٌ، كُلُّكُمْ لِآدَمَ، وَآدَمُ مِنْ تُرَابٍ.
Ku saurara! Ubangijinku ɗaya ne, kuma ubanku ɗaya ne. Dukkanku daga Adam kuke, Adam kuma daga ƙasa