AYola Data

AYola Data ALHAMDULLAH 🤲🙏

💞ALƘAWURAN ALLAH GUDA HUƊU:*-"Allah yayi wasu alƙawura acikin Alƙur'ani ga bayinsa, wanda kuma haƙiƙa munsan alƙawarin A...
11/05/2026

💞ALƘAWURAN ALLAH GUDA HUƊU:*
-
"Allah yayi wasu alƙawura acikin Alƙur'ani ga bayinsa, wanda kuma haƙiƙa munsan alƙawarin Allah baya tashi, kuma Allah bai kasance yana saɓa alƙawari ba"
-
*ALLAH BUWAYI YACE:*
-
💧"Sabõda haka, ku tuna Ni, nima sai In tunã ku"
Quran-2:152
-
💧"Kuma lallai ne, idan kun gõde ina ƙara muku"
Quran-14:7
-
💧"Kuma Ubangijinku ya ce: "Ku kira Ni in karɓa muku"
Quran-40:60
-
💧"kuma lallai Allah bai kasance Mai yi musu azãba ba alhãli kuwa sunã yin istigfãri."
Quran-8:33
-
-
"Dukkanin waɗannan, wasu alƙawura ne waɗanda Allah maɗaukakin sarki ya ɗaukarwa kansa su matuƙar muma mun cika namu gareshi.

💞Idan kana da wata bukata a wajen Allah duk girman ta, duk yawan ta ka tashi bayan biyu bisa uku na dare ya wuce, kayi I...
11/05/2026

💞Idan kana da wata bukata a wajen Allah duk girman ta, duk yawan ta ka tashi bayan biyu bisa uku na dare ya wuce, kayi Ibada a lokacin ka roki duk abinda kake nema zaka ga ikon Allah.

Manzon Allah (S.A.W) yana yawan fadawa Sahabban sa cewa su dinga tashi idan biyu bisa uku na dare ya shude...

Wani zai ce yaushe ne biyu bisa uku na dare yake karewa? Ga yadda zaka gane:

Zaka raba Awannin da ake yi a cikin dare kashi uku ne, misali:
A yanzu (May 2026) dare yana farawa ne da karfe 6:40 na yamma a Northeastern Nigeria (ina lissafi da inda nake ne), wato Borno, Bauchi, Gombe, Yobe, Adamawa da Taraba.

Kuma daren yana karewa karfe 6:00am na safe. So, idan ka kirga zaka ga akwai Awanni 12, sai ka raba su kashi uku, zai baka 4 hourly.

Karfe 7 na Magriba, da karfe 8, 9 zuwa 10:40 na dare shine daya bisa uku na dare, da zaran karfe 10:40 tayi an shiga biyu bisa uku na dare.

Karfe 11 na dare, da karfe 12, 1 har zuwa karfe 2:40 shine biyu bisa uku na dare.

Da zaran karfe 2 tayi toh two over three na daren ya kare, saura kaso daya, kuma shine mafi tsada da muhimmanci. Shi kuma zai fara daga karfe 2, 3, 4 har zuwa karfe 5:40 na Asubah.

Lokaci mafi tsada kenan daga karfe 2:40 na dare. Zai yi wahala ka dauki wasu kwanaki kana tashi kana yin Ibada kana rokon Allah a wannan lokacin baka ga abinda zai faranta maka rai ba, abu ne mai wahalan gaske kaga shiru.

Also, hatta macen da bata da damar yin Sallah zata iya tashi a wannan lokacin, tayi Zikirori, tayi Salati, Karatun Al-Qur'ani, Hailala, Hauqala, Hamdala da saura su, sai tayi addu'ar da duk take so, kada kice ai baki Sallah ba zaki tashi ba, a'a ba'a yin haka.

Abu na karshe, lissafi Awannin dare yakan canza daga lokaci zuwa lokaci, daga wuri zuwa wuri. Misali, lokacin zai iya canzawa idan an shiga lokacin sanyi, Damina, Raani da sauran su.

Sannan zai iya shan banban daga wannan kasar zuwa wancan, hatta a Nigeria akwai sabanin lokaci na wasu Mintoci tsakanin jihohi saboda nisan dake tsakanin su, kamar lokacin da ake fara kiran Sallar Magriba a Maiduguri da Lagos akwai banbanci.

Hatta mu da muke North East, akwai tazarar kusan Minti 10 tsakanin Bauchi da Maiduguri. Dan haka zaka lissafa Awannin dare da wajen da kake zaune.

Allah ya datar damu, ya amsa mana.
Kada a manta dani idan an tashi yin addu'a, nagode.

💞KANA LAIFI, ALLAH YA RUFA MAKA ASIRI…😭* *Kai laifi…*_Amma Allah ya rufa maka asiri._*Ka yi kuskure…*Amma Allah bai tona...
09/05/2026

💞KANA LAIFI, ALLAH YA RUFA MAKA ASIRI…😭*

*Kai laifi…*
_Amma Allah ya rufa maka asiri._

*Ka yi kuskure…*
Amma Allah bai tona ka a bainar jama’a ba.💔

*Ka saba wa umarninsa…*
Amma har yanzu yana baka numfashi.

*❓To yanzu idan ka tuba, za a wulaƙanta ka ne ?*

_Ka tuna da abin da Allah ya faɗa_

> قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِن رَّحْمَةِ اللَّهِ

*Ka ce: Ya ku bayina waɗanda kuka yi zalunci ga kanku, kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah…”*
— Al-Qur'an 39:53

_Allah bai ce: “Ya ku masu tsarki” ba._
_Ya ce: “Ya ku waɗanda kuka yi zalunci ga kanku.”_

_Wato maƙasudin rahama shi ne mai laifi._

*🌧 Tuba ba wulaƙanci ba ne*

Shin ka taɓa jin labarin mutumin da ya kashe mutum 100 ?
Sai ya tuba, Allah ya gafarta masa.

Hadisin yana cikin Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim.

Idan wanda ya kashe 100 ya samu gafara,
to me yasa kai za ka ji tsoron tuba ?

*Wulaƙanci shi ne…*

Ka ci gaba da laifi duk da Allah ya rufa maka asiri.

Ka mutu kana ɓoye zunubi ba tare da tuba ba.

*Amma tuba ?
Tuba daraja ce.

Manzon Allah ﷺ ya ce:

> “Mai tuba daga zunubi kamar wanda bai taɓa yin sa ba.”

Allah yana farin ciki da tubar bawa fiye da farin cikin mutum da ya sami abin da ya ɓace masa a hamada.

💔 Ka ji wannan da kyau_

Idan Allah ya rufe maka asiri lokacin da kake laifi,
me yasa zai wulaƙanta ka idan ka koma gare Shi ?

Allah ba ya neman kunyarka,
yana neman dawowarka.

*Kar ka bari shaidan ya ruɗe ka da cewa*
“Idan ka tuba mutane za su yi maka dariya.”

💞INA KUKE MASOYA MANZON ALLAH (ﷺ)?Manzon Allah ﷺ ya ce: "Ku yawaita salati a gareni a daren Juma'a da ranar Juma'a, wand...
08/05/2026

💞INA KUKE MASOYA MANZON ALLAH (ﷺ)?

Manzon Allah ﷺ ya ce: "Ku yawaita salati a gareni a daren Juma'a da ranar Juma'a, wanda yayi salati daya a gareni, Allah zai yi salati goma a gareshi" Baihaqiy, Albaniy ya ingantashi

اللهمَّ صلِّ على محمَّد وعلى آل محمَّد، كما صليتَ على إبراهيم وعلى آل إبراهيم؛ إنَّك حميدٌ مجيد. اللهمَّ بارِك على محمَّد وعلى آل محمَّد، كما باركتَ على إبراهيم وعلى آل إبراهيم؛ إنَّك حميدٌ مجيد [البخاري ومسلم]

ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA ALA ALI MUHAMMAD, KAMAA SALLAITA ALA IBRAHEEM WA ALA ALI IBRAHEEM, INNAKA HAMEEDUN MAJEED, ALLAHUMMA BAARIK ALA MUHAMMAD WA ALA ALI MUHAMMAD, KAMAA BAARAKTA ALA IBARAHEEM WA ALA ALI IBRAHEEM, INNAKA HAMEEDUN MAJEED.

Wanda ya lizimci yawaita salati ga Manzon Allah damuwanshi da bakinciki za su kwaranye🌹

06/05/2026
💞ZIKIRIN SAFIYA DA MARAICE.-"Kada ka rafkana daga zikirori a rayuwarka, musamman ma irin zikirorin safiya da maraice, da...
06/05/2026

💞ZIKIRIN SAFIYA DA MARAICE.
-
"Kada ka rafkana daga zikirori a rayuwarka, musamman ma irin zikirorin safiya da maraice, da makamantansu, domin haƙiƙa shaiɗan yakanyi galaba kan duk wanda yake gafala daga yin addu'oi a rayuwarsa"
-
"Sau nawa wata musiba take shirin afkuwa gareka amma a dalilin addu'oin da ka kasance kana yi yau da kullum sai Allah ta'ala ya karkatar da wannan musibar izuwa wani gurin, sau nawa wani bala'in yake tunkaroka amma dalilin zikirorin da ka kasance kana yi sai Allah ya taƙaita wannan bala'i ya sauka a kan kayanka a maimakon ya sauka a karan-kanka"
-
"Haƙiƙa akwai falala a cikin yin zikirori a rayuwa, domin haƙiƙa shi zikiri kariya ne kuma garkuwa ne ga bawa, sannan kuma haƙiƙa Allah yana bawa bawansa lada idan ya kasance yana kiyaye yin zikiri musamman irin zikirin da ya tabbata a sunnah"
-
❝Duk wanda yace SubhanAllahi Wa bi Hamdi سبحان الله وبحمده Sau ɗari a rana, za a kankare masa zunubansa koda kuwa sun kai misalin yawan kumfar kogi❞

💞Herbeeberh Bala Abdullahi Abdullahi Bin Buraidah yace Baban sa ya bashi labarin wani abu da ya faru wata rana a kusa da...
05/05/2026

💞Herbeeberh Bala Abdullahi Abdullahi Bin Buraidah yace Baban sa ya bashi labarin wani abu da ya faru wata rana a kusa da Manzon Allah (S.A.W). Yace wata rana Manzon Allah (S.A.W) yaji wani mutum yana addu'a, lokacin da zai yi addu'ar sai yace:

"Allahumma inni as'aluka bi anni ash-hadu annaka antal Lah, allazi Laa ilaha illah ant, al-ahadus samad, Allazi lam yalid walam yuwlad, walam yakun lahu kufwan Ahad".

Sai Manzon Allah (S.A.W) yace "Tabbas wannan mutumin ya roki Allah da sunayen da idan an roke shi yana bayarwa, idan an kira shi dasu yana amsawa".

Tun daga lokacin Sahabbai da wadanda s**a zo bayan su idan zasu yi addu'a zasu roki Allah ya basu wani abu na duniya ko Lahira s**an ambaci wadannan sunaye da siffofi.

اللهم إني أسألك بأني أشهد أنك أنت الله الذي لا إله إلا أنت، الأحد الصمد الذي لم يلد ولم يولد، ولم يكن له كفوا أحد

Wadannan suna daga cikin kalmomin da hatta Ni da ba kowa ba na shaida tasirin su da karfin su, musamman idan nayi Sujuda cikin Sallah ko bayan na Idda Sallar Nafila zanyi addu'a.

Allah ya karba mana ya amsa mana.

04/05/2026
💞KANA SON SAMUN LADA DUBU?"Idan kana so ka sami lada dubu, kuma sannan a kankare maka zunubanka dubu, to ka yawaita yin ...
03/05/2026

💞KANA SON SAMUN LADA DUBU?

"Idan kana so ka sami lada dubu, kuma sannan a kankare maka zunubanka dubu, to ka yawaita yin tasbihi, wato faɗin (subhanallah,) sau ɗari za a rubuta maka kyawawan lada dubu, sannan kuma a kankare maka zunubai dubu dominta"

"Ka faɗeta kana mai ƙudurce ma'anarta acikin zuciyarka, sa'annan kuma ka tsarkake zuciyarka a lokacin faɗin nata, duk faɗin Subhanallahi sau ɗari, lallai inshaa Allahu zaka sami kyakkyawan lada guda dubu, da kuma karkaɗe zunubai dubu"

"Manzon Allah ﷺ, yace: shin yanzu ɗayanku zai gajiya wajen samun kyawawan lada guda dubu, sai wani mai tambaya yace: to yanzu ta yaya ɗayan mu zai sami kyawawan lada dubu?, sai (annabi ﷺ,) yace: idan ɗayanku yayi tasbihi (subhanallah) guda ɗari, za'a rubuta masa lada guda dubu, kuma za'a kankare masa zunubai guda dubu"

Jami'i At-tirmiziy (3463)

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AYola Data posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share