16/08/2026
An Gudanar Da Zikiran Waki'ar Buhari A Da'irorin 'Yan Uwa
A jiya Asabar 2 ga watan Rabi'ul Awwal 1448, 'yan uwa Musulmi almajiran Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) s**a gudanar da Zikiran Waki'ar Buhari, da juyayin cikarta shekaru 11 da aukuwa, a Da'irori daban-daban a faɗin ƙasar nan da ƙetare.
A daidai irin wannan lokaci na farkon watan Rabi'ul Awwal ne, sojojin Nijeriya bisa umurnin shugaban ƙasa na lokacin, Muhammadu Buhari, s**a dirarwa 'yan uwa Musulmi a Zaria, inda s**a kashe kusan kimanin mutum dubu a cikin kwanaki uku.
A rana mai kamar yau, 3 ga Rabi'ul Auwal ne sojojin s**a harbi Jagoranmu Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) bayan sun kashe daruruwan almajiransa, 'yan uwansa na jini, da kuma 'ya'yansa na cikinsa guda uku da s**a kashe su a gabansa, sannan s**a tafi da shi da matarshi cikin harbin harsasai da nufin ganin bayanshi da kawo karshen Harka Islamiyya bakidaya.
Ko da yake a watan Disamba ne ake gudanar da manyan tarurrukan tunawa da Waki'ar a lissafin Miladiyyah, bisa raya Munasabar a lissafin Hijiriyya ma 'yan uwa a kowace Da'ira sun gudanar da taron Zikira, wanda a mafi yawan wurare Harisawan Harkar Musulunci s**a shirya, inda aka tuna da Waki'ar, da Shahidanta, da kuma darussan dauka daga gare ta, tare da addu'o'i na musamman ga Shahidan Waki'ar masu girma.
Ga hotunan wasu daga tarurrukan.
— Hurrasul Harakatil Islamiyya
3 Rabi'ul Auwal 1448 (16/8/2026)