Rayyan Alhassan Gumel

Rayyan Alhassan Gumel Seasoned Politician|| Reputable Businessman|| Renowned Journalist|| Peace & Social Advocate

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yanzu nake samun labarin mutuwar tsohon Shugaban karamar hukuma Sule Tankarkar Malam...
30/05/2026

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yanzu nake samun labarin mutuwar tsohon Shugaban karamar hukuma Sule Tankarkar Malam Jafaru Muhammad Danzomo.

Allah ya gafarta masa, ameen.

Ina amfani da wannan dama wajen taya Sanata Sabo Nakudu  murna ya samu nasara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ADC domin...
27/05/2026

Ina amfani da wannan dama wajen taya Sanata Sabo Nakudu murna ya samu nasara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ADC domin tsayawa takarar gwamnan Jihar Jigawa a shekarar 2027. Wannan nasara tana nuna irin amincewa, ƙwarewa, da jajircewar da ya nuna tsawon shekarunsa na hidimtawa al’umma da jihar baki ɗaya.

Sanata Sabo Nakudu mutum ne mai kishin jama’a, kusanci da al’umma, da hangen nesa wajen kawo ci gaba mai ɗorewa. Fitowarsa a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani ya sake ƙarfafa kwarin gwiwa ga matasa, magoya baya, da duk masu burin ganin Jigawa ta samu shugabanci nagari, haɗin kai, da cigaba mai anfani ga kowa.

Ina bayyana cikakken goyon baya na gare shi da tafiyarsa zuwa 2027 ƙarƙashin tutar ADC. Ina addu’ar Allah Ya ba shi nasara, hikima, da ƙarfin jagoranci domin cika burin al’ummar Jigawa.

27/05/2026

Assalamu Alaikum wa Rahmatullah.

Ina miƙa godiyata ta musamman ga ɗaukacin al’ummar Gumel/Gagarawa/Maigatari da Sule Tankarkar, musamman wakilai, magoya baya, matasa, mata, dattawa, da duk wanda ya tsaya tare da ni a wannan tafiya ta neman tikitin takarar kujerar Tarayya ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress.

Hakika, sakamakon zaɓen fidda gwani bai kasance yadda muka yi fata ba, amma muna karɓar hakan da zuciya ɗaya a matsayin ƙaddarar Allah Maɗaukakin Sarki. Ina alfahari da irin soyayya, goyon baya, addu’o’i, da jajircewar da kuka nuna tun daga farko har ƙarshe.

Ina kuma godewa jam’iyyarmu mai albarka, shugabanni, da dukkan masu ruwa da tsaki bisa damar da aka ba ni da kuma yadda aka gudanar da wannan tsari. Siyasa ba ta ƙare da sakamakon zaɓe ba siyasa hidima ce da haɗin kai domin cigaban al’umma.

Ina tabbatar muku cewa zan ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyarmu tare da bada gudunmawa, haɗa kai, da ci gaba da gwagwarmayar ganin mun samu nasara a babban zaɓe mai zuwa. Burinmu shi ne cigaban al’umma da tabbatar da ingantaccen wakilci ga jama’armu.

Ga magoya bayana da matasa masu kishin wannan tafiya, ina roƙonku da ku kwantar da hankalinku, ku ci gaba da zama masu biyayya da kishin jam’iyya. Wannan tafiya ba ta tsaya a nan ba, kuma In Sha Allah alheri na gaba ya fi wanda ya gabata.

Nagode ƙwarai da gaske, Allah Ya saka muku da alheri.

🌙✨ Eid Mubarak ✨🌙As we celebrate this blessed season of Eid, I pray that Almighty Allah fills our hearts with peace, our...
27/05/2026

🌙✨ Eid Mubarak ✨🌙

As we celebrate this blessed season of Eid, I pray that Almighty Allah fills our hearts with peace, our homes with happiness, and our lives with endless blessings.

May this Sallah bring unity, progress, good health, and success to us all. Let us continue to show love, kindness, and gratitude to one another, because the true beauty of Eid is not only in celebration, but in togetherness and compassion.

Wishing you and your family a joyful and memorable Sallah celebration. May Allah accept our prayers, sacrifices, and good deeds. 🤲🏽

Eid Mubarak!

Gagarawa ba baƙon wuri ba ne a gare mu, Gagarawa gida ne da ya kasance tare da mu a kowane mataki na tafiyarmu ta siyasa...
24/05/2026

Gagarawa ba baƙon wuri ba ne a gare mu, Gagarawa gida ne da ya kasance tare da mu a kowane mataki na tafiyarmu ta siyasa da hidima ga al’umma.

Ziyararmu ta jiya kafin zaɓen fidda gwani na gobe ta sake tabbatar mana da irin ƙauna, karɓuwa da goyon bayan da al’ummar Gagarawa suke nunawa koyaushe.

Mun zo ne domin gaisawa da jama’a, sauraron shawarwari, da ƙara ƙarfafa haɗin kanmu domin cimma buri ɗaya na cigaba da kyakkyawan wakilci.

Gagarawa ta nuna cewa haɗin kai, aminci da siyasar ci gaba su ne ginshiƙin nasara.

Allah ya albarkaci Gagarawa, Allah ya albarkaci al’ummarmu.

My heart is filled with gratitude after the overwhelming reception I received from the good people of Sule-tankarkar. Wh...
24/05/2026

My heart is filled with gratitude after the overwhelming reception I received from the good people of Sule-tankarkar. What I witnessed yesterday was not just a political gathering, but a powerful demonstration of unity, hope, and the collective desire for a better future.

The massive turnout, the warmth, the prayers, the encouragement, and the show of love were truly humbling. I remain deeply honoured by the confidence and trust you continue to place in me and in our shared vision for progress under the African Democratic Congress (ADC).

Your support has strengthened my resolve to continue this journey with sincerity, courage, and total commitment to the welfare of our people. Together, we shall build a constituency where the voices of the people matter, where opportunities are created for our youth, and where development reaches every community.

I sincerely appreciate our elders, youths, women groups, party stakeholders, supporters, and every single person who came out to welcome us. Your solidarity sends a clear message that the time for purposeful and people-oriented representation has come.

This movement belongs to all of us, and by the grace of God, victory shall be ours.

Thank you for the unforgettable reception. The journey to a better future has truly begun.
Alhassan



A yau mun dawo gida, Sule Tankarkar domin sake kusantar al’umma, sauraron ra’ayoyinsu, da ƙarfafa alaƙar da ta daɗe tana...
24/05/2026

A yau mun dawo gida, Sule Tankarkar domin sake kusantar al’umma, sauraron ra’ayoyinsu, da ƙarfafa alaƙar da ta daɗe tana haɗa mu da jama’a.

Yayin da ake shirin gudanar da zaɓen fidda gwani gobe, irin tarba, addu’o’i da goyon bayan da muka samu daga al’ummar mu na nuna mana cewa shugabanci na gaskiya yana farawa ne daga tushe.

Sule Tankarkar a shirye take, a haɗe take, kuma muna da fata ga makoma mai kyau.

Tare za mu ci gaba da tafiya zuwa nasara.
Rayyan Alhassan
23rd May 2026

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!Munyi rashin Alhaji Hon. Abba Anas Adamu Laushi bayan an sace shi a hanyar Kaduna zu...
11/05/2026

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!

Munyi rashin Alhaji Hon. Abba Anas Adamu Laushi bayan an sace shi a hanyar Kaduna zuwa Abuja abin tausayi ne matuƙa, kuma yana ƙara nuna irin matsalar rashin tsaro da ƙasar nan ke fuskanta.

Tsohon ɗan Majalisar Wakilai ne kuma ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, wanda ya rasa ransa yayin da yake ƙoƙarin cika burinsa na yi wa al’ummar Jigawa hidima. Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya sanya shi a Aljannatul Firdaus, Ya ba iyalansa da masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi. Amin.

-Honourable Rayyan Alhassan Gumel

Jiya, na samu damar karɓar baƙi daga abokai, masu ruwa da tsaki, shugabancin matasa, da magoya baya masu kishin cigaban ...
11/05/2026

Jiya, na samu damar karɓar baƙi daga abokai, masu ruwa da tsaki, shugabancin matasa, da magoya baya masu kishin cigaban al’umma domin tattauna muhimman batutuwan siyasa da na ƙasa da s**a shafi jama’armu da makomarmu.

Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan haɗin kai, shugabanci nagari, ƙarfafa matasa, da hanyoyin da za mu haɗa kai wajen tabbatar da tsaron ƙasa da cigaban al’umma.

Ina matuƙar godiya ga duk wanda ya ware lokaci domin bayar da shawarwari, nuna goyon baya, da jajircewa wajen ganin an samu cigaba ga al’ummarmu. Tare, za mu ci gaba da gina tafiya mai cike da hangen nesa, hidima, da kishin jama’a na gaskiya.

Wannan tafiya ta cigaba ce, kuma da yardar Allah tare da goyon bayan al’umma, makoma mai kyau tana yiwuwa.

— Hon. Rayyan Alhassan Gumel

Bismillah tawakkaltu alal-lahJagoranci hidima ce, hangen nesa, da jajircewa wajen yi wa al’umma aiki.A yau, muna farin c...
07/05/2026

Bismillah tawakkaltu alal-lah

Jagoranci hidima ce, hangen nesa, da jajircewa wajen yi wa al’umma aiki.

A yau, muna farin cikin bayyana aniyar tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai, tare da sabunta alkawarin yin aiki da gaskiya, ƙwarewa, da tausayi. Tare, za mu gina mazaba mafi ƙarfi da ci gaba, insha Allah.

Address

Africa
Africa

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Rayyan Alhassan Gumel posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Rayyan Alhassan Gumel:

Share