18/05/2026
BABBAR MAGANA : Wata budurwa ta rasa aikin da ake biyanta sama da naira dubu 200 a wata bayan ta ki amincewa da cire hijabinta kamar yadda kamfanin da take aiki ya bukata.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama ke yabawa matashiyar bisa tsayawa kan addininta da mutuncinta duk da rasa damar aikin.
Yayin da wasu ke ganin ya kamata a mutunta ‘yancin addini a wuraren aiki, wasu kuma sun bayyana cewa kamfanoni na da dokoki da ma’aikata ke bi.
Mutane da dama sun yi mata addu’ar Allah Ya maye mata da aikin da ya fi wannan alheri da albarka. 🤲
Wanne fata za ku yi mata?
Ku shiga shafin jaridar ANNUR-Hausa domin samun Sahihan Labarai.