Saifullahi Rabi'u

Saifullahi Rabi'u I'm invent this pages just because of my un aims and objectives

14/08/2025
Hakika fa salatin annabi makamine na yaqi akan talauci  dasuran bukatu na duniya kai kowacce buqata kakeda idan kayawait...
09/05/2024

Hakika fa salatin annabi makamine na yaqi akan talauci dasuran bukatu na duniya kai kowacce buqata kakeda idan kayawaita salati Allah zai biyamaka Allah humma Salli alah Muhammad wah alihi wah sahabihi wasallimu tasalima

25/08/2023

Happy mould

Allahumma salli wah sallim alah sayyidina Muhammad wah alihi wah wasahabi ajama'in                 SUNAN ALLAH ARRAHAMAN...
25/08/2023

Allahumma salli wah sallim alah sayyidina Muhammad wah alihi wah wasahabi ajama'in

SUNAN ALLAH ARRAHAMAN

Duk wanda yakarantashi bayan sallar jm'a kafa dari 100 manzUn allah s a w yace bazai tashi daga masallacin ba face allah yagafartamai zunubban

23/08/2023

ZAN IYA JAN CARBI, KO KO BIDI'A NE ?

Tambaya
Assalamu Alaikum. Tambaya. Allah ya gafartawa Malam Na kasance ina amfani da charbi (Tasbaha) domin yana tunatar dani wajen ambaton Allah a kowane lokaci. Ina matsayin haka a sharia ?

Amsa:
Wa'alaykumussalam, To dan'uwa jan carbi ba bidi'a ba ne, saboda duk da cewa babu shi a zamanin Annabi s.a.w. hakan ba zai sa ya zama bidi'a ba, saboda wanda yake amfani da shi ba ya nufin cewa ibada ce mai zaman kanta, yana amfani da shi ne, don ya kiyaye adadin zikirinsa.

Yin amfani da 'yan yatsu shi ne yafi, saboda hadisi ya yi nuni cewa : za'a ba su dama su yi magana, ranar alkiyama, kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: 3486, don haka za su yi maka shaidar abin da ka yi na alkairi, sabanin carbi.

Sannan sau da yawa za ka ga mutum yana jan carbi amma hankalisa yana wani wajen, sabanin idan da hannu yake yi.

Jan carbi yakan iya sanya wasu su yi riya, saboda wasu suna ratayawa ne a wuya don a gane su zakirai ne.

Annabi s.aw. yana yin tasbihi da hannunsa na dama kamar yadda ya tabbata a hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 1286, wanda Albani ya inganta, saidai wasu malaman suna cewa in ya yi da hagu ma yayi, tare da cewa yi da dama shi ne yafi.

Saidai duk da dalilan da s**a gabata, mutum zai iya jan carbinsa, tun da jan carbi ba ibada ce mai zaman kanta ba, b***e ace ya zama bidi'a, ga shi kuma ba'a samu wani hadisi da ya hana ba, tare da cewa yi da hannu shi ne yafi.

Don neman Karin bayani duba : Majmu'ul fataawa 22\187. da Lika'ul maftuh na Ibnu-uthaimin 3\30.

Allah ne mafi sani

DR JAMILU YUSUF ZAREWA
24\3\2015

Address

Gwandu Lcg Area
Birnin-Kebbi

Telephone

+2349039195439

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Saifullahi Rabi'u posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share