28/10/2025
Abubuwan dakesa yaro kaifin basira da haddar karatu:
1. Cin abinci mai gina jiki
2. Samun isashshen bacci (awa 8 zuwa 10)
3. Motsa jiki (ƙwallo, gudu, tseren keke)
4. Samun kulawar iyaye da soyayya
-------------------------
Bugu da ƙari:
5. Iyaye su kasance masu duba littafan karatu da rubutun yaro tare da kulawa
- Shin yaro yana mayarda hankali gurin abunda ake koyar dashi a makaranta?
- Shin yaro yana rubuta abunda malami ke koyar dashi a makaranta?
- Shin yaro yana cin kyakkyawan sakamakon jarabawa?
6. Ka nemi wani wanda zai koyarda yaronka "extra lesson" a gida (English da Mathematics) da dare misalin ƙarfe 8:30 zuwa 9:30pm
⚠️ Babu wani maganin bature, ko na gargajiya da ake baiwa yaro domin samun kaifin hadda da basirar karatu a makaranta
Saboda haka kar ku kashe kuɗinku a banza, ku jarraba wannan tsarin Insha Allah zakuyi farinciki.
Alhassan Mai Lafia