03/03/2026
MAKOMAN TAFSIRIN RAMADANA NA BANA (1447-2026) WANDA SHEIKH SHEIKH ALKALI ABUBAKAR SALIHU ZARIA YAKE GABATARWA A MASALLACIN MOKAS DAKE GARIN DAMATURU.
Sanin Kowane an Turo Mana Mallam ne Daga National Headquarters,(Jibwis Jos). Kamar yadda aka Saba Turowa Mallamai daban-daban tsawon Shekaru Talatin da biyar (35yrs).
Sanin kowane bana Alkali Mallam Abubakar Salihu Zaria Yafara Tafsiri har tsawon kwanaki Goma sha Daya (11 days). Daga bisani aka Dakatar dashi Ranar 12 ga Ramadana. Bisa Umarnin Shugaban Majalisar Mallamai na Kasa Fadilatussheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, Saboda Dalilai na tsaro.
Sakamakon.....
1.Khudba da Nasiha da Mallamin yayi a Yobe state
Police Headquarters Ranar Juma'ar da ta Gabata,
2.Haka Kuma da Nasihan da Yayi da Asuba a Masallacin Alimarami Ranar Asabar.
3.Haka Kuma Tafsirin da Yayi Ranar Juma'a da daddare sanye da kayan Agaji, a Nan Masallacin Mokas inda yake Gabatar da Tafsiri. Lalle hakika wadannan Abubuwa ya Shafi Al umma da yawa, cikin akwai Jami'an tsaro, Gwamnoni, harda Shugaban Kasa.
Wanda irin wannan Salon da Mallam Yayi amfani dashi na Kiran Sunayen Mutane , da tsinuwa da Jafa'i, Ya Sabawa karantarwar Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'a wa Iqamatissunnah.
Sakamakon Haka ne yau 14 Ramadan 1447 Fadilatussheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya Kira Shi Mallam Alkali Abubakar Salihu Zaria, da Matai makin Shugaban Majalisar Mallamai na jihar Yobe, da wakilan Qaramar hukumar Damaturu mutum uku, inda Mallam ya Gabatar da Jawabi Sannan ya Umurci kowa Yayi Jawabi, Sannan daga Karshe ya fahimci cewa Cigaba da Tafsirin Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria a Damaturu ba Alkhairi Bane, ya zartar da Janye posting nashi daga Damaturu.
A Karshe Mallam Alkali Abubakar Salihu Zaria ya Fahimci Hakika Yayi Kuskure, Kuma ya amsa cewa Yayi Kuskure.
Sannan Yana Mai Bada Hakuri Ga Shugaban kungiyar da kuma Daukacin Al umma da dukkanin Wanda Abun ya shafa.
Da Fatan Allah ya gafarta Mana Kura kuren mu ya dauramu akan Dai-dai...
Copied
Jibwis damaturu