25/08/2025
📊 Candlestick Patterns in Trading
Candlestick shi ne hanya mafi sauƙi da traders ke karanta motsin farashi (price action). Yana nuna inda farashi ya fara, inda ya tsaya, mafi tsada da mafi ƙasƙanci a cikin lokaci guda.
🕯️ Muhimman Candlestick Patterns:
1. Doji
Yana nuna rashin tabbas (indecision) a kasuwa.
Yana iya zama alamar sauyin trend.
2. Hammer 🛠️
Idan ya fito a ƙasa, yana nuna yiwuwar reversal daga bearish zuwa bullish.
3. Shooting Star ✨
Idan ya fito a sama, yana nuna yiwuwar reversal daga bullish zuwa bearish.
4. Bullish Engulfing
Candle mai kore ya rufe gaba ɗaya candle ja a baya.
Alama ce mai ƙarfi ta bullish reversal.
5. Bearish Engulfing
Candle mai ja ya rufe gaba ɗaya candle kore a baya.
Alama ce ta bearish reversal.
---
⚡ Dalilin da yasa Candlestick Patterns suke da muhimmanci:
Suna taimaka maka wajen karanta halin traders a kasuwa.
Suna nuna yiwuwar sauyin trend ko ci gaba.
Ana haɗa su da Market Structure don samun tabbacin shigar trade.
👉 Ka tuna: “Candlestick ba wai prediction bane, amma yana nuna maka labarin da kasuwa ta fada.”
Aliyu Yunusa ✍️