Gaskiya Dokin Karfe Baure L.G.A

Gaskiya Dokin Karfe Baure L.G.A Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gaskiya Dokin Karfe Baure L.G.A, Business service, BAURE L. G. A, Daura.

Takardar tsohon kudi t N200 ce kadai za’a ci gaba da amfani da ita daga yanzu zuwa kwanaki 60.Dari 5 da dubu 1 kuma sun ...
16/02/2023

Takardar tsohon kudi t N200 ce kadai za’a ci gaba da amfani da ita daga yanzu zuwa kwanaki 60.

Dari 5 da dubu 1 kuma sun tashi daga aiki a cewar shugaba Muhammadu Buhari.

Wanda hakan yanuna cewa Shugaba Buhari ya fashimci Duk wasu daga cikin manyan Barayin Gwamnonin da s**a Saci kudi bay wuce su Saci #1000 da #500 da Sauran manyan Barayin ma'aikatan Gwamnaty mu munsani wannan itace Hanya Mafi sauki ta karyasu.

Kadan daga mafar Canjin kudu

1. Farfado da Tattalin Arzikin kasa
2.Fafardo da martabar Naira
3.Faduwar kayan masarufu
4.Sakin Fashi da makami
5.Samin sauki cinhaci da Rashawa
6.Gano manyan Barayin Kasa
7.Sayen Kuru'un Talakka wajen Have
8.Wayar da mutanen Karkara mushimmancin Bude Asusu banjo
9. Dadai Sauran su.

Wanda hakan Aboye ne sbd Tuntura Talakkawa Nigeria

Abu na biyu mudama Talakkawa mumfi Amfani da Takardar kudi ta #200 #100 #50 #20 #10 #5 #2 #1 Dan kuwa sune Matsalar Talakkawa ko Asaye da sayarwar da mukeyi ta yau da kullum kuwa.

Inajan hankalin Talakkawan Nigeria da mukara hakuri Dan kusan idan akace Gwara za'ayi to Dolene a takura idan mukakayi La'akari karaya ta Hannu ko Takafa wajen Dori Dolene aji zafi hakan bazaisa kace abarma kafarka ba ko hannun ka

Kalma ta karshe da Zance Anan shine Karaya da Zafi Dori da Ciyo.

15/02/2023
Ka'idojin yadda ake kai tsofaffin takardun kudi a babban bankin CBN1. Idan ka kai kudin ba za a chanza maka da sababbi b...
14/02/2023

Ka'idojin yadda ake kai tsofaffin takardun kudi a babban bankin CBN

1. Idan ka kai kudin ba za a chanza maka da sababbi ba, sai dai a saka maka acikin asusun ajiyarka na banki (Account)

2. Hukuma zata bincika ta tabbatar da cewa asusun ajiyarka baya da wata matsala, kamin asaka maka kudin, idan aka fahimci akwai damuwa ga asusunka na banki, to za a dawo maka da kudinka.

3. Wani ba zai kai kudin wani ba. Kowa shi zai kai kudinsa da kansa kuma asusun ajiyarsa na banki zai bayar a saka kudin aciki.

4. Kamin ka tafi bankin CBN domin kai kudi, akwai bukatar ka ziyarci shafin yanar gizo na bankin domin cike form na saka kudin, domin ka samu reference number da zaka yi amfani da ita. (Wanda ya kasa yin wannan, za a bashi form din ya cike a can)

5. Wanna aiki za a gudanar da shi daga nan zuwa 17 February (wato 17 ga wannan wata da muke ciki) kuma zai a rufe daga wannan lokaci.

A gobe Laraba kotun koli za ta yanke hukuncin karshe game da cigaba da karbar tsoffin kudi ko kuma akasin haka. Daya dag...
14/02/2023

A gobe Laraba kotun koli za ta yanke hukuncin karshe game da cigaba da karbar tsoffin kudi ko kuma akasin haka.

Daya daga cikin abubuwa Uku da zai iya faruwa gobe a kotun;

Na farko kodai kotun ta yanke hukuncin CBN da Bankuna su cigaba da karbar tsoffin kudaden tare da cigaba da hada-hada dasu a tsakanin al-umma har zuwa lokacin da za su kare. Wannan hukuncin na iya faruwa duba da yadda wasu gwamnoni da dama s**a tada hankalin su akan lallai sai an cigaba da karbar tsoffin kudaden domin siyen kuri'un talakawa da tsoffin kudaden a zabe mai zuwa.

Na biyu kodai kotun ta yanke hukuncin CBN da Bankuna su kara wasu kwanaki domin duk wani mai tsohon kudin ya samu ya kai Banki amma ba za'a cigaba da hada-hada da kudaden a tsakanin al-umma ba.

Na Uku kodai kotun ta yanke hukuncin CBN da Bankuna su daina karbar tsoffin kudaden wanda hakan zai jawo muguwar asara musamman ga 'yan siyasa da 'yan Kasuwar da har yanzu s**a boye tsoffin kudaden wasu da niyyar su raba a lokutan zabe wasu kuma don gujewa fadawa tsadar rayuwa na rashin wadatattun sabbin kudaden.

Tun jiya Litinin wasu Bankuna da dama a Najeriya s**a daina karbar tsoffin kudi saboda sunce CBN ba ta basu sanarwar su cigaba da karba ba.

Yanzu haka masu tsoffin kudade suna ta zuwa Bankunan da ake karbar tsoffin kudaden suna maidawa wanda matukar aka ce a cigaba da karbar tsoffin kudaden kuma ba'a wadata al-umma da sabbin kudin ba to tabbas wahalar da za'a kara sha sai tafi ta baya.
Toh me karatu meye ra'ayinka akan hakan wata shawara zaka'iya bayarwa.?

✍️ Zaharaddeen Lawal Baure

14/02/2023
Allah Ubangiji ya Jikanka da Rahama Ramat Murtala Allah yasa kwanciya Hutuce.
14/02/2023

Allah Ubangiji ya Jikanka da Rahama Ramat Murtala Allah yasa kwanciya Hutuce.

Address

BAURE L. G. A
Daura

Telephone

+2347046346062

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gaskiya Dokin Karfe Baure L.G.A posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share