28/03/2023
Labarin Gamon Katar: Barawo ya Zama Sarki
Wani barawo ne aka yi mashiririci mai suna Katar. Watarana ya shiga Masallaci don ya yi sata a tsakiyar dare. Da shigar sa sai ya ji motsin mutane kusa da Masallacin. Da ya ji sun matso kusa sai ya kabbarta Sallah. Ana haka sai ya ji an bude Masallaci an shigo. Sai ya yanke shawarar tsawaita Sallah saboda jin tsoro. Su kuma kawai sai s**a share wuri s**a zauna suna jiran sa. A tsorace ya sallama ya waiga don ya ga ko su wane ne. Ko da ya juya sai ya ga Sarki da tawagarsa. Kafin ya ce komai sai Sarki ya mika masa hannu s**a gaisa, bai san abinda ke faruwa ba. Aka je da shi fada aka kyautata masa har gari ya waye sannan aka yi yekuwa. Jama’a s**a taru sannan sai Sarki ya yi jawabi. Ya ce, tun da dadewa ina son in aurar da babbar ‘yata. Kuma na rasa wanda zan aura ma ita domin ina neman na kirki mai jin tsoron Allah. Amma Liman ya ba ni shawara kuma na yi aiki da ita. Na samu wannan saurayi a tsakiyar dare shi kadai cikin Masallaci yana sallah a lokacin da duk ire-irensa suna gida suna bacci. Don haka na aura masa da ‘yata kuma na yanka masa wani babban gari daga cikin masarautata.
A nan ne fa gogan naka ya sunkuyar da kansa yana kuka, yana fadi a zuciyarsa, wannan fa sallar karya ce na yi Allah ya ba ni wannan alheri. To, ina ga na yi sallar gaskiya! Ya Allah daga yau na daina duk wani aikin assha, kuma zan rika sallar dare har iya tsawon rayuwata. To, kun ji labarin “Katar” da ake cewa: Allah ya yi muna gamon Katar.
Darussa:
A rana daya Allah kan yi bature.
Duk halin da ka ga mutum a cikin sa kada ka yanke masa kauna, Idan yana da rabo watarana Allah zai shiryar dashi