15/12/2025
Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'oon
Akwai aiki 😭
Wani bidiyo da attajirin Afirka, Aliko Ɗangote, ya bayyana kwanan nan ya ja hankalin jama’a, inda ya yi bayani kan irin kuɗin da wani babban jami’in gwamnati ya kashe wajen karatun ’ya’yansa.
A cewar bayanin da Ɗangote ya yi, an nuna cewa Faruk Ahmed Maishanu Ɗanmadamin Sakkwato ya kashe kimanin dala miliyan biyar ($5m) wajen karantar da ’ya’yansa guda huɗu a wata makarantar sakandare da ke ƙasar Swaziland. Adadin kuɗin, a bisa lissafin Naira, ya kai kusan Naira biliyan 7.4.
Faruk Ahmed Maishanu Ɗanmadamin Sakkwato shi ne Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Midstream da Downstream ta Najeriya (NMDPRA), wata muhimmiyar hukuma da ke da alhakin sa ido kan harkokin man fetur a ƙasar.
Lamarin ya haifar da muhawara a tsakanin jama’a, musamman kan batun yawan kuɗin da ake kashewa wajen karatun ’ya’ya a ƙasashen waje, a yayin da ’yan Najeriya da dama ke fuskantar matsaloli a ɓangaren ilimi da tattalin arziƙi.
Lahira akwai aiki,Allah ya sa mudace.
✍️ DDistinguish Mubarak Idris Mbk