31/12/2025
DA DUMI-DUMI: Daga gobe 1 Jan 2026, Bankuna zasu fara cire Naira 50 daga duk wanda zai tura Naira dubu 10,000 zuwa account din wanda basa Banki daya dashi. Za'a dinga cire Naira 50 din ne daga account din mai turawa ba mai karba ba k**ar yadda ake yi a yanzu.
Idan transfer din tsakanin Banki daya ne k**ar Taj Bank zuwa wani account na Taj ba za'a dauki Naira 50 din ba, sai in Bankunan sun saba, k**ar Ja'iz zuwa Taj, misali.
Sannan ba za'a dinga cire kudin daga albashin ma'aikata ba. Wannan Naira 50 din sunce wai kudin Hatimi ne, kudin sa hannu, Stamp.... Hmmmm
Wani bincike da aka yi a farkon 2025 din nan ya nuna akwai active bank accounts guda miliyan 320 a Nigeria. Misali ace transfer guda miliyan 30 kadai za'a yi a kullum a Nigeria tsakanin Bankuna wanda za'a karbi Naira 50, hakan yana nufin a kowace rana za'a karbi Naira biliyan 1.5 kenan.
Duk sati za'a karbi Naira biliyan goma da rabi (10.5b Naira), idan anyi transfer sau miliyan 30 a kowace rana kenan. Wato duk wata (monthly ) Naira biliyan 42,000,000,000 ko kuma a duk shekara Naira biliyan dari 504.
Wato rabin tiriliyan.
A shekara biyu za'a tatsi Naira tiriliyan 1 biliyan 8 kenan.
Sai dai, daga karshe me za'a yi dasu? sai Allah kadai ya sani, sai wadanda iko da kudaden ke hannun su.
Daga Abdulhadee Isah Ibrahim.