Hussain B

Hussain B Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hussain B, Business Supply Service, main market, Gombe.

13/04/2025

Kurakurai 14 Da Ke Iya Rusa Ƙaramin Ɗan Kasuwa:

1- Jari kamar jariri ne, raino da ririta shi ake yi. Ka ɗauki jarinka a matsayin shi ne mutuncinka, ka kula da shi sosai domin shi ne ruhinka a harkokin kasuwanci, domin yanzu sai da kuɗi ake neman kuɗi.

2- Kada ka riƙa kashe kuɗi babu lissafi, za su lalace ba tare da kula ba.

3- Idan ka yi kasuwanci, ka ƙarƙare lissafi, ka fitar da riba, to sai ka ware abin da za ka yi buƙata, da wanda za ka yi alheri, da wanda za ka ƙara a jari.

4- Kada ka bari wani ya jingina da kai idan ba ka tsaya da ƙafarka ba, domin dukanku za ku haɗu ku faɗi. Ba rowa nake koya maka ba, ka samu ka tsaya tukuna, sai ka taimaki wasu. Idan ka tsayu da ƙafarka, to mutumin da ada ka hana shi dubu ɗaya, la'alla yanzu ka ba shi dubu ɗari ba tare da ya nema ba, ka yi haƙuri ka bi komai a sannu.

5- Kada ka riƙa kashe kuɗi sama da wanda kake samu. Idan kasuwa ka tsuke, to kai ma ka tsuke bakin aljihunka, idan ta buɗe, kai ma ka sarara.

6- Kada asara ta kashe maka gwiwa ko ta sanya ka ja da baya, ka tsinci darasi daga kuskurenka na baya ka ci gaba da tafiya.

7- Kada ka riƙa kashe duka ribarka, bisa tunanin gobe ma za ka samu wasu. Babban kuskure ne hakan. Ka riƙa kasa ribarka gida uku: ka ƙara a kan jarinka, ka yi buƙata da wata, ka ajiye wata a reserve. Domin hauhawar farashi tana karya jari in dai ba ya girma, saboda idan kana siyan kayan miliyan ɗaya, sai farashi ya ƙaru, s**a koma miliyan biyu, to jarinka ya lalace, sai dai idan kana ɗan ƙara wa daga ribar da kake samu, sai ta riƙa daidaita shi. Haka nan ranar da ba ka samu kuɗi ba, ko ba ka fita kasuwa ba, daga reserve za ka yi buƙatu ba sai ka taɓa jari ba.

8- Kada ka riƙa gasa musamman da wanda yake sama da kai, daga lokacin da kana rainon jarinka sai ka fara gasa da wanda ya fi ka, to za ka ruguje babu makawa.

9- Ka riƙa sabunta harkokin kasuwancinka da tafiyar da su da zamani, da kula da inganci da packaging da jawo hankalin mutane, domin idan ba ka haka kasuwancinka zai zama tsohon ya yi

Address

Main Market
Gombe

Telephone

+2349061626925

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hussain B posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hussain B:

Share