Alhaji Abbas Ansarus Sunnah

Call Website Contact the business

Alhaji Abbas Ansarus Sunnah Astagfurullahi

Na yi farin ciki sosai da gwamnatin Saudiyya ta hana wannan mutumin samun bizar zuwa Umrah.Wannan ya nuna cewa gwamnatin...
24/09/2026

Na yi farin ciki sosai da gwamnatin Saudiyya ta hana wannan mutumin samun bizar zuwa Umrah.

Wannan ya nuna cewa gwamnatin Saudiyya ta san darajar Masallaci Mai Tsarki.

Na san wasu za su ce ba a shiga tsakanin Allah da bawansa. Eh, tabbas haka ne. Amma yana da kyau ya gyara halayensa da farko, tare da tuba ta gaskiya, kafin samun damar shiga ƙasa mai tsarki

Bayan haka, wannan hukuncin zai koyar da wasu mutane da ke yaɗa ɓarna a kafafen sada zumunta darasi.

Yana da kyau gwamnatin Nigeria tayi koyi da wannan matakin wurin hana mutanen banza damar samun fasfo ko tsallakawa ƙasashen waje.

Bayan iyaye, akwai haƙƙi kan masu mulki wurin kare tarbiyyar al'umma.

For you Muslims only
27/07/2026

For you Muslims only

YADDA AKE WARWARE SIHIRITambaya :*Assalamu alaikum Dan Allah malam a fitar dani cikin duhu game da abin da yake damuna M...
17/07/2026

YADDA AKE WARWARE SIHIRI

Tambaya :*
Assalamu alaikum Dan Allah malam a fitar dani cikin duhu game da abin da yake damuna Mahaifiya ta ce ta je gurin malami ai mata naganin ciwon mara dz yake damunta, tace tana da ciki yakai shekara, amma likitoci sun yi scanning sunce ba komai to sai malamin ya ce mata asiri aka yi mata, kuma zai yi mata magani nan take ta haife abinda yake cikinta amma za ta kawo tunkiya da dubu bakwai, sai take min magana in kawo kudi a sayi tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya malam zuciyata ba ta aminta da malaman ba ne shi yasa ! Na keso ka bani fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a addini? Idan bata halatta ba wacce hanya zan bi wajen qin biyan kudin da kuma sanar da ita, saboda ina da matsala , ta bangaren aqeeda mun banbanta? Wassalam na gode malam Allah ya qara basira.

*Amsa :*

Wa alaikum assalamu To 'yar'uwa tabbas ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur'ani, wasu malaman sun yi bayani cewa : ana iya warware sihiri ta hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta : 117 zuwa ta 122, na suratul A'araf, sai kuma aya ta : 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da aya ta : 65-70 a suratu Dhaha, za'a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai.
Amma bai halatta ki taimaka mata ba, wajan bada wadannan kayan da boka ya nema, saboda ba'a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah.
Ya wajaba ki yi mata nasiha cikin hikima, ki sanar da ita cewa : Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa :" "Duk wanda ya je wajan boka, ya tambaye shi wani abu, Allah ba zai amshi sallarsa ba, ta kawana arba'in" kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2230. Kin ga in mutum ya mutu a wadannan kwanaki akwai matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari'a ta yarda da ita, a wani hadisin kuma yana cewa : "Duk wanda ya je wajan boka ya gaskata abin da ya fada, to tabbas ya kafurce da abin da annabi Muhammad ya zo da shi" kamar yadda ya zo a Sunanu-abi-dawud hadisi mai lamba ta : 3904, kuma Albani ya inganta shi .
INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZA KI IYA GANAR DA ITA, TA DAWO KAN HANYA.

Allah ne mafi sani.

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
08062954596

\2026

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

MATA KAR KUYI WASA DA WANAN SUNADA  KYAU SOSAI KUMA GASU MAGUNGUNAN  Topface 08062954596TopFans The FollowingFacebook
15/07/2026

MATA KAR KUYI WASA DA WANAN
SUNADA KYAU SOSAI
KUMA GASU MAGUNGUNAN
Topface 08062954596

TopFans



The Following

Facebook

LAHAULA'WALA QUWWATA ILLA'BILLAH...Rayuwa ba tsawonta ne abin alfahari ba, kyawun karshenta ne. Mutum na iya rayuwa shek...
07/07/2026

LAHAULA'WALA QUWWATA ILLA'BILLAH...

Rayuwa ba tsawonta ne abin alfahari ba, kyawun karshenta ne. Mutum na iya rayuwa shekaru kaɗan, amma ya bar tarihin da zai sa a cigaba da tuna shi har bayan rasuwarsa. Haka kuma wani na iya rayuwa shekaru masu yawa, amma da zarar ya mutu sai a manta da shi, mafi girman abin da ya kamata mu nema shi ne, Allah Ya ba mu rayuwa mai albarka, Ya sa mu yi aikin da zai amfani addininsa da al'umma, sannan Ya kyautata ƙarshenmu.

Lallai, idan mutum ya kyautata rayuwarsa, ya kasance mai hidima ga addini, mai koyar da alheri, mai kira zuwa ga Sunnah, mai taimakon bayin Allah, to bayan rasuwarsa ba za'a daina ambatonsa da alheri ba. Za'a cigaba da yi masa addu'a, ana amfana da iliminsa da ayyukansa, kuma wannan yana daga cikin manyan ni'imomin da Allah ke yi wa bawansa.

Ka dubi irin malamai kamar Sheikh Ahmed BUK, Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, Sheikh Auwal Albani Zaria, Sheikh Abubakar Gero Argungu, da Sheikh Abdul'aziz Dutsen Tanshi. Duk sun riga mu gidan gaskiya, amma har yau ana sauraron karatuttukansu, ana karanta littattafansu, ana yada wa'azinsu, kuma miliyoyin mutane suna cigaba da yi musu addu'ar Allah Ya jikansu, Ya gafarta musu, Ya saka musu da Aljannatul Firdausi.

Wannan yana nuna cewa mutuwa ba ita ce ƙarshen rayuwar mutum ba idan ya bar kyakkyawan tarihi da ayyukan alheri. Kyakkyawan suna da amfanin da mutum ya bari suna cigaba da rayuwa a cikin zukatan mutane.

Ya Allah, Ka gafarta mana zunubanmu. Ka sa mu kasance cikin bayinka nagari. Ka ba mu ikon kyautata rayuwarmu, ka sa mu bar abin alheri da za a cigaba da amfana da shi bayan mutuwarmu. Ka sa idan aka ambace mu, a ambace mu da alheri, kuma idan muka koma gare Ka, Ka karɓe mu cikin rahamarka da gafararka. Ka sa mafi alherin farin cikin kwanakinmu shine ranar da za mu haɗu da Kai.

Alhaji Abbas Ansar
Abdussamad Tijani Sani...✍️

Shin kana tunanin akwai wata dukiya da zata hana a saka ka a cikin rami idan lokacinka yayi?Mutum zai iya mallakar Trili...
06/07/2026

Shin kana tunanin akwai wata dukiya da zata hana a saka ka a cikin rami idan lokacinka yayi?

Mutum zai iya mallakar Triliyoyin nairori, ya gina gidaje sama da 800 a ciki da wajen ƙasa, ya mallaki motoci 400 har da jiragen sama na kashin kansa. Wannan shine kololuwar arziƙi da burin kowane ɗan adam.

Amma ga wata gaskiya mai ɗaci da ke tattare da tara duniyar:

NA FARKO
Gidajen nan sama da 800, babu guda ɗaya da zai bi ka zuwa ƙabarinka idan numfashinka ya ɗauke.

NA BIYU:
Cikin motocin nan 400 na alfarma, babu wacce zata ɗauke ka zuwa makabarta face makara ta katako

NA UKU:
Triliyoyin nairorin nan zasu koma hannun magada ne su ci gaba da raba su a kyauta, wataƙila ma su fara rikici a kansu tun kafin a gama makokinka

Babban kuskuren da matasa suke yi a yau shine, muna ƙulla gaba, muna yanke zumunta, kuma muna barin sallah domin mu tara abin da wani zai zo ya gada a banza.

1. Kana kashe kanka kana zaluntar mutane don ka mallaki filaye, alhali ramin da zaka kwanta a ƙarshe bai wuce tsawon ƙafafunka ba

2. Idan ka mutu a yau, koda kana da bilyoyi a banki, ba za a yanke aljihu a jikin likkafaninka don a zuba maka koda naira hamsin ba.

Duk wata dukiya da ka tara ba zata amfane ka ba a gobe, sai dai wadda ka bayar da hannunka kafin idonka ya rufe
Neman na kai wajibi ne domin rufin asiri a duniyar yau. Amma mayar da neman kuɗi ta hanyar haramun tamkar zaka wanzu a duniya har abada, ɓatan basira ne.

Arziƙin duniya a duniya yake ƙarewa.
Allah ya Jikan Magabatanmu..
UMAR ALIYU DAHIRU ✍️

06/07/2026

Address

Manawachi Quarter's Gombe
Gombe
2999

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alhaji Abbas Ansarus Sunnah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Alhaji Abbas Ansarus Sunnah:

Shortcuts

Share