22/12/2025
Hukumar Kiyaye Hadurran Hanya ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutane tara (9) sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a hanyar Kaltungo–Cham da ke kauyen Kaluwa, a ƙaramar hukumar Kaltungo ta Jihar Gombe.
Shugaban hukumar a Jihar Gombe, Mista Samson Kaura, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da manema labarai.
Kaura ya bayyana cewa, jimillar mutane 18 ne s**a shiga cikin hatsarin, inda biyar daga ciki s**a samu raunuka daban-daban, yayin da huɗu kuma s**a tsira ba tare da rauni ba.
Hatsarin ya haɗa ne da wata babbar mota (trailer) da kuma motar fasinja kirar Sharon. A cewar Kaura, binciken farko da s**a gudanar ya nuna cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudu fiye da ƙima da kuma gazawar birki.
Ya ce, trailer ɗin na saukowa ne daga wani gangare da gudu, sai birkin motar ya gaza aiki, wanda hakan ya sa direban ya rasa ikon sarrafa motar.
Trailer ɗin ya bugi motar Sharon daga baya, wanda hakan ya sa motar ta kife da fasinjoji a ciki.
Bayan faruwar lamarin, jami’an ceto daga hukumar FRSC sun garzaya da waɗanda s**a ji rauni zuwa Asibitin Gwamnati na Kaltungo domin samun kulawa, yayin da aka kai gawarwakin mamatan ɗakin ajiye gawa na asibitin.