18/07/2024
LABARI CIKIN HOTUNA
A yau aka gudanar da taron social media na gidan Hon. Rabi'u Sahabi Liman Danmasanin Kaura domin tattauna mahimman abubuwa.
Anyi wannan taro domin kara wayar da kai ga marubuta na gidan Hon. Rabi'u Sahabi Liman domin cigaban wannan tafiya inda DG SALMANU SANI HAIDARA yayi jan hankali ga matasa su rike gaskiya da amana kuma su zama masu biyayya ga dokoki da ka'idodi domin nasarar wannan tafiya.
Daga karshe Shugaban marubutan gidan Hon. Rabi'u wato Nura Kabiru Dan Auta shima yayi jan hankali garesu su cigaba da wayar dakai ga matasa domin zaben shugaba nagari domin samun ingantattar rayuwa.
By Assadiq Kaura