01/04/2025
ANYA ZAMU TSIRA A HAKA KUWA?
🍎 Naira 200 tayi mana yawa wajen bayar da sadaka, amma kuma tayi kadan wajen yin liki a biki ko gun wata sabga ta duniya!
🍎 Minti 60 na yin zikiri a masallaci ko a gida yayi mana yawa, amma minti 90 yayi mana kadan a wajen kallon kwallo!
🍎 Awa 1 ko 2 sun yi mana yawa a gurin daukar karatu, amma kuma sun yi mana kadan a wajen kallon fina finai!
🍎 Zaman karanta ayoyi 🕌20 na Al-qur'ni yakan yi mana kunci, amma cikin annashuwa mukan shafe kimanin awa 3 ko 4 muna karanta shafukan yanar gizo ko jaridu!⌨
🍎 Aguje mukan gaskata labarin jaridu,📰 amma idan an zo fagen Al-qur'ani da hadisin Manzon Allah (s.a.w) 🕋sai yawan shakka da tuhuma, musamman idan sun ci karo da son zuciyarmu!
🍎 Muna da son karanta labaran ban dariya a facebook ko whatsapp,📱 amma da zarar mun ci karo da "posting" na fadakarwa ko abin da ya shafi addinin musulunci🕌, sai mu tsallake!
🍎 Mukan saka talabijn🚊 a gaba na tsawon awanni muna kallo, amma sai mu kasa tsaiwa minti 15 muna kallon Gabas,🕋 domin yin ibada!
🍎 Haddar wakoki🎧 basa yi mana wuya, amma mukan ga wahalar haddar ayoyin Al-qur'ani mai girma!🕋
ALLAH Yakaramana imani ameen idan ka yarda da wannan tunasarwa to katura zuwa ga wasu Don su amfana.
Allah yasa muga lafiya