The Emerald Law Firm

The Emerald Law Firm Legal Practitioners and Barriers and Solicitors of the Supreme Courts Of Nigeria.

Law Firm specialized
1.Human Rights Protection:
2.​Expert Advocacy:
3.​Strategic Consultancy:
4.​Real Estate Excellence:

ZAROTA/002: FITA TA BIYU​Dokar Ababen Hawa Ta Jihar Zamfara (Zamfara Road Traffic Law, 2015)Acikin ​Jadawali na Biyu (Se...
11/06/2026

ZAROTA/002: FITA TA BIYU

​Dokar Ababen Hawa Ta Jihar Zamfara (Zamfara Road Traffic Law, 2015)

Acikin ​Jadawali na Biyu (Second Schedule) na wannan dokar ya lissafa laifuka guda t 94 tare da takamaiman hukunci ko tara da aka tanada ga duk wanda ya saba musu.

​Domin wayar da kan al'umma dangane da dokokin Jihar Zamfara, yau za mu duba tushen iko da iyakokin Hukumar Kula da Tuki da Ababen Hawa ta Jiha (ZAROTA).

Duk wanda aka ci tara da ta saba wa abin da wannan kundi ya tanada, lallai an keta doka kuma an zalunce shi. Saboda haka, duk lokacin da jami'ai s**a ce ka yi laifi, yana da kyau ka san takamaiman laifin da kuma ainihin abin da doka ta tanada a kansa....domin nazari ga dokokin da hukunce hukunce da doka ta tanada domin amfanin Ku.

​Kiranmu Ga Bangarori Biyu:

1) ​Hukumar ZAROTA Su tsaya tsayin daka ga abin da kundin doka ya ba su iko akai, su guji wuce gona da iri ko karbar abin da doka ba ta amince da shi ba.

​2) Al'umma Su kasance masu bin doka da oda domin kiyaye zaman lafiya da samun ci gaba mai dorewa.

​Bin doka shi ne babban gishirin zaman tare.

​Mu hadu a rubutu na gaba domin jin irin hakkoki, nauyi, da kuma abubuwan da wannan doka ta dora wa masu tuki da masu ababen hawa...

​M. Umar, Esq.,
Mahmud Sani Kaura, Esq.
(Public interest & Human rights lawyers)
11.06.2026

Muna sanar da jama’a cewa mu, Lauyoyi Masu Kare Hakkin Jama’a, mun shigar da kara gaban Babbar Kotun Jihar Zamfara da ke...
15/05/2026

Muna sanar da jama’a cewa mu, Lauyoyi Masu Kare Hakkin Jama’a, mun shigar da kara gaban Babbar Kotun Jihar Zamfara da ke Gusau don kalubalantar cin zarafi da take hakkin bil’adama da jami’an hukumar ZAROTA ke yi wa mutane.

​Wannan mataki ya biyo bayan wani lamari da ya faru ranar 28 ga Fabrairu, 2026, a Sabon Gari, Gusau, inda jami’an hukumar s**a ci zarafin lauya sannan s**a kwace masa waya saboda kawai yana daukar hoton yadda suke take hakkin jama’a a fili.

​Abubuwan da muke bukata a gaban Kotu:
​Hakin Daukar Hoto: Kotu ta tabbatar da cewa dan kasa yana da ikon daukar hoton ma’aikacin gwamnati yayin da yake gudanar da aiki a fili.

​Hana Kwace Kaya: Kotu ta bayyana cewa ZAROTA ba ta da ikon kwace kadarorin mutane (kamar waya) ba tare da umarnin kotu ba.

​Daina Cin Zarafi: A dakatar da duka, tsoratarwa, da gudanar da aiki ba tare da katin shaida ko kakin sani ba.

​Neman Hakki: Muna neman kotu ta tilasta wa ZAROTA ba da hakuri a fili, sannan ta biya diyya kan keta haddin da ta yi.

​"Hakkin dan adam ba ihisani ba ne; rantsattsen tanadi ne na kundin tsarin mulki wanda kowace hukuma dole ne ta girmama shi."

​Wannan karar mataki ne na tabbatar da cewa babu wata hukuma a Jihar Zamfara da ta isa ta kasance sama da doka.

​Sa hannu:
M. Umar, Esq. & M. Sani Kaura, Esq.
(Lauyoyi Masu Kare Hakkin Jama’a)
​14.05.2026
======================

We filed LAW Suit Against the ZAROTA

We the Public Interest Lawyers have formally filed a Fundamental Rights Enforcement Suit at the High Court of Zamfara State (Gusau Judicial Division) against ZAROTA

This legal action targets the systemic abuse of power and persistent unlawful conduct by officers of the **Zamfara State Road Traffic Agency (ZAROTA)*.

The suit originated from an incident of **February 28, 2026, at Sabon Gari, Gusau* wherein ZAROTA officers harassed me and forcibly seized my mobile phone for documenting their act of Human rights violation activities in a public space.

The case would serve as a judicial challenge to a broader pattern of human rights violations of ZAROTA's marshals during road operations especially in Gusau the state capital.

We equally invite the court to affirm and declare the following:
1- Constitutional Right to Record:That citizens have a protected right to document public officers performing their duties in public spaces.

2- Prohibition of Illegal Seizures:That ZAROTA lacks the statutory authority power to seize private property, including mobile phones, without a valid court order.
*3- Cessation of Abuse:* That acts of assault, threats, and intimidation constitute direct violations of the 1999 Constitution (as amended).

4- Mandatory Identification: That operating without visible uniforms or identification tags violates the *Zamfara State Road Traffic Agency Law, 2015, and undermines public accountability.

*We further also demand the following Reliefs: to include Perpetual Injunction:* A court order permanently restraining ZAROTA from future harassment or unlawful seizure of citizenaproperty.and seek for Public Apology formal from the Agency. While urging the court also for Exemplary Damages by way of Financial compensation for the gross violation of the Applicant’s fundamental Rights.

"Fundamental Rights are not privileges granted by the state; they are constitutional guarantees that every authority is bound to respect."

This suit is a commitment to ensuring that no agency in Zamfara State operates above the law. We remain dedicated to reinforcing transparency and the Rule of Law for a better Zamfara and beyond.

Signed:
M. Umar, Esq.
M. Sani Kaura, Esq.
*(Public Interest Lawyers & Human Rights Advocates)*
[email protected]
14.05.2025






Taqabalallahu Minna Wa min-kum!
20/03/2026

Taqabalallahu Minna Wa min-kum!

Munsamu Korafe Korafe gameda abinda kenfaruwa a Sambo Secondary school na Zalunci da akeyi wurin rabon Katin ATMWanda Ba...
06/03/2026

Munsamu Korafe Korafe gameda abinda kenfaruwa a Sambo Secondary school na Zalunci da akeyi wurin rabon Katin ATM
Wanda Babban aikinsu shine suyi activation na Kati kuma subwa Wadan da aka ayyana katinsu suje su cire kudinsu inda sukeso.

Abubuwan da akeyi a wurin sun hada da:

1.Kowane beneficiary ana debemasa daga dubu Daya zuwa dubu goma.

2.Ana Sanyawa kowane beneficiary ATM PIN batareda Neman izininsuba KO Neman abinda sukeso asakamasu a Matsayin pins nasu.

3.Ana boyewa beneficiary PINs na ATM CARD batareda wani daliliba.

4.Suna Cilastawa Kowane beneficiary Yaje wurinsu yadebe kudin da aka turamasa.

5..Ana Debe kudi batare da angayama mai account ainihin abinda aka debeba.

6.Ana barazana GA Wadanda s**ace su Basu yardaba sai anbasu kudinsu cikakku tahanyar anfani da gurbatattun Jami'an tsaro domin cinma burinsu.

7.Ana cilasta karban rashawa dasunan taimakon beneficiary.

8.Sun halasta haram, domin jingina kudin da Suke karba Matsayin tsararren tsarine daga federal government

9.Suna karyar da cewa suna amfani da kudin da s**a karba domin biyan Security da Ad-hoc staff das**a dauka.

Lallai bazamu zura Ido muna ganin ana cigaba da Zalunci ba, Tuni munfara daukar matakin Daya dace kuma muna Kira GA duk Wadanda aka debewa kudi su kwantar da hankinsu, insha'Allah zamu dau matakin Shari'a dai dai da abinda Suke aikatawa.

Congratulations to all UDUS graduates for their CALL TO THE BAR ceremony.
12/07/2025

Congratulations to all UDUS graduates for their CALL TO THE BAR ceremony.

14/11/2022
25/08/2022

Welcom to Faculty of Law Usumanu Danfodiyo University Sokoto

Address

DAZA VILLAGE
Sokoto

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when The Emerald Law Firm posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to The Emerald Law Firm:

Share