Marafa, Mai Unguwa, Haruna, Kayarda Media Forum.

Marafa, Mai Unguwa, Haruna, Kayarda Media Forum. An bude wannan shafi dan tallata 'yan takarar majalissar jiha da na tarayya na kananan hukumomin Jahun da Miga a inuwar jamiyar APC a zabe mai zuwa na 2027.

Hon. Umar Imam, Marafan Jahun. Haruna Amadu Jabanna. Haruna Aliyu dangyatin kayardan Du

08/08/2026

Marafa mai masoya da yawa

INEC/ UMAR IMAM MARAFAN JAHUN.Hukumar zabe mai zaman Kanta ta kasa INEC. Ta wallafa sunan HON. UMAR IMAM MARAFAN JAHUN. ...
03/08/2026

INEC/ UMAR IMAM MARAFAN JAHUN.

Hukumar zabe mai zaman Kanta ta kasa INEC. Ta wallafa sunan HON. UMAR IMAM MARAFAN JAHUN. A matsayin Dan takarar majalissar wakilai ta kasa da zai wakilci kananan hukumomin Jahun da Miga a inuwar jamiyar APC a babban zabe mai zuwa na 2027.

Fitar Wannan suna ya kawo karshen kace nace, da ake yadawa kan chanjin 'yan takara.

Muna Kara godewa Alummar kananan hukumomin Jahun da Miga bisa soyayya, kauna, Addu'o'i, gami da kyakkyawan zato da kuke akan HON UMAR IMAM, MARAFAN JAHUN.

Muna Addu'ar Allah ya kaimu lokacin zabe da Rai da lafiya.

Allah ka bamu Nasara Ameeen.

Alhamdulillah.
Alhamdulillah.
Alhamdulillah.

Ismail Salisu Bature Jahun.
Mataimaki na musamman kan harkokin Yada Labarai da Kafofin Sada zumunta na zamani ga Hon Umar Imam marafan Jahun.
03-08-2026.

01/08/2026
28/07/2026

Hon. Umar Imam marafan Jahun, a gwada musu tsafta, sannan a rabamusu data.

Jahun da Miga, marafa is coming.

Wish you All the best.
17/07/2026

Wish you All the best.

JAN HANKALI GA MAGOYA BAYAN TAFIYAR SIYASAR HON. UMAR IMAM, MARAFAN JAHUN. Mai girma Dan takarar majalissar wakilai da w...
16/07/2026

JAN HANKALI GA MAGOYA BAYAN TAFIYAR SIYASAR HON. UMAR IMAM, MARAFAN JAHUN.

Mai girma Dan takarar majalissar wakilai da wakilci kananan hukumomin Jahun da Miga a zauren majalissar wakilai ta kasa HON. UMAR IMAM, MARAFAN JAHUN. Yana mai kira ga magoya bayansa musamman matasa da sauran masoya da cewa.

Na fara shiga hrkokin tsayawa takarar siyasa tun a shekarar 1996. A lokacin 0 Parry. Yayin da Alummar karamar Hukumar Jahun s**a yarda Dani har s**a zabeni a matsayin shugaban karamar Hukumar Jahun.

Tun daga wannan lokaci nake ta samun nasara a Al'amuran rayuwa.

1. Na zama shugaban karamar Hukumar sau 3. Uku.
2. Na rike muqanin na Adviser a matakai daban daban.
3. Na zama Dan majalissar dokokin jihar jigawa.
4. Dama sauran muqamai da dama.

Abin danake so na haskawa matasa na wannan lokaci shine.

Ba komaine yasa na sami wadannan nasarori ba, face bin wasu matakai da s**a hadar da.
1. Hakuri.
2. Biyayya ga shugabanni.
3. Jajircewa akan duk wata hidima data shafi Alumma.
4. Tabbatar da rike Amanar Alummar das**a amince mana.
5. Addu'a da neman zabin Ubangiji.

Inaso duk mai goyon bayan tafiyar siyasata da cewa ku dauki irin wadancan matakai da nabi ku gwadasu a kawunanku zakuga yanda rayuwa zata chanzamu da izinin Allah.

A wannan lokaci na tsaya takara a matakin DAN MAJALISAR WAKILAI na kananan hukumomin JAHUN da MIGA. Muna rokonku daku sakamu a cikin addu'o'inku na Yau da kullun, Dan neman Nasara daga Allah madaukakin sarki.

Ina mai Jan hankalinku matasa da ku guji
1. Tsokanar abokan adawaba.
2. Ku kauracewa duk wata hanya daza tasa ku bata da 'yan uwanku.
3. Ku kiyaye cin mutuncin juna.
4. Ku tabbatar da kun samar da ci hadin kai a tsakanin matasa.
5. Ku mai da hankali wajen shiga lungu da sako Dan tallata kyawawan
manufofinmu.

Idan Allah ya yarda zamuci zabe.

Kuma zamu rike muku Amana.

Na gode kwarai da gaske da irin gudunmawar dakuke bamu.

Allah ya taimaki gwamnatin tarayya da jihar jigawa dama Jamiyar APC. Baki daya.

HON. UMAR IMAM, MARAFAN JAHUN NE YA GABATAR DA KUDURIN DOKAR KAFA JAMI'AR SULE LAMIDO UNIVERSITY KAFIN HAUSA.A shekar 20...
14/07/2026

HON. UMAR IMAM, MARAFAN JAHUN NE YA GABATAR DA KUDURIN DOKAR KAFA JAMI'AR SULE LAMIDO UNIVERSITY KAFIN HAUSA.

A shekar 2013. Hon. Umar Imam, Marafan Jahun, yana a matsayin Dan majalissar dokokin jihar jigawa mai wakiltar karamar Hukumar Jahun, ya kafa tarihin da Alumma bazasu manta dashiba.

A yayin zaman majalissar dokokin jihar jigawa ne a shekarar 2013. Marafan Jahun ya gabatar da wani QUDURIN DOKA a zauren majalissar, dsya bukaci majalissar data Kafa dokar samar da Sabuwar JAMI'A a jihar jigawa wato STATE UNIVERSITY.

Yayin daya sami amincewar mafi yawancin mambobin majalissar kan wanna kudurin nasa.

Hakan ya baiwa shugaban majalissar dokokin jihar jigawa na wancen lokaci Rt. Hon. Adamu Atmos Sarawa. Damar Kafa kwamati da zai duba bukatar da Dan majalissar na jahun ya gabatar na neman a Kafa Sabuwar JAMI'A JIHA.

Bayan kwamatin Harkokin Ilimi na majalissa Wanda Hon. Umar Imam, Marafan Jahun yake ciki ya kammala aikinsa gami da gabatar da rahoton kwamatin ga majalissa, kana majalissar ta karbi rahoton kwamatin.

Hon. Umar Imam marafan Jahun ya sake tashi a zauren majalissar inda ya sake gabatar da kudurin neman a tabbatar da Sabuwar JAMI'AR JIHAR JIGAWA, a matakin doka. Wato ( JIGAWA STATE UNIVERSITY KAFIN HAUSA) Kafin daga bisani ta koma (Sule Lamido University Kafin Hausa) a yanzu.

Babu shakka irin wadannan mutane kamar su Hon Umar Imam marafan Jahun. mutane masu ilimi da tunani gami da hangen nesa sun dace da zama wakilan jama'a. Duba da yanda suke wakilcin da Alumma suke anfana ba Wai aljihunsuba.

A yanzu haka Sule Lamido University Kafin Hausa tana ci gaba da yaye kwararru dalibai da ake alfahari dasu a kasarnan.

Wannan ma wata babbar nasarace da dakuma iya wakilci na gari.

Wannan tasa Alummar kananan hukumomin Jahun da Miga s**ace Hon. Umar Imam marafan Jahun shine ya dace ya ya wakilcemu a zauren majalissar wakilai ta kasa.

Allah ya bamu Nasara Ameeen.

MATASAN NASARAWA DAKE K/H. MIGA SUN ZIYARCI HON. MARAFAN JAHUN.Matasan masu ra'ayin jamiyar APC. Sunce sun kawowa Dan ta...
14/07/2026

MATASAN NASARAWA DAKE K/H. MIGA SUN ZIYARCI HON. MARAFAN JAHUN.

Matasan masu ra'ayin jamiyar APC. Sunce sun kawowa Dan takarar majalissar wakilai Hon. Umar Imam marafan Jahun ziyarar ne gami da yima Albishir na lashe zabe da yaddar Allah.

Inda s**ace a karamar Hukumar miga bamu da babu wata jamiya idan ba APC ba, sauran duk Yan neman abinci ne.

Yayin da Hon. Umar Imam marafan Jahun ya kara karfafawa musu guiwa kan su dage da kokarin tallata kyawawan manufofin Yan takarar da jamiyar APC ta tabbatar Dan samun nasarar lashe babban zaben dake gabanmu.

Address

Jahun Local Government
Jahun

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Marafa, Mai Unguwa, Haruna, Kayarda Media Forum. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share