Tata Trade and Innovation

Tata Trade and Innovation We are a forward-thinking company dedicated to delivering smart trade solutions, innovative business ideas, and growth opportunities.

Our mission is to connect people, empower businesses, and create lasting value through excellence, trust, and innovation.

27/04/2026
Assalamu Alaikum masoyanmu,Akwai ƙalubale, amma babu wani zaɓi face mu ci gaba. Alhamdulillah, mun samar da sabon offici...
27/04/2026

Assalamu Alaikum masoyanmu,

Akwai ƙalubale, amma babu wani zaɓi face mu ci gaba. Alhamdulillah, mun samar da sabon official personal account na Company ɗinmu, Muryar Arewa TV.

Muna roƙonku da ku ci gaba da bibiyarmu a wannan sabon account ɗin:
👇👇👇👇
https://www.facebook.com/muryararewatv01

Mun sabunta ayyukanmu tare da shirye-shirye masu kayatarwa da nishadantarwa domin faranta muku rai a gidan talabijin ɗinmu na Muryar Arewa TV.

Mun gode da irin goyon baya da ƙaunar da kuke nuna mana. Allah Ya saka da alheri.

FARASHIN KAYAN GONA A KASUWAR MANIGI (MASHEGU LGA, JAHAR NIGER)📅 Alhamis, 09/04/2026🌾 Farashin Kaya:1.Buhun Masara — ₦24...
09/04/2026

FARASHIN KAYAN GONA A KASUWAR MANIGI (MASHEGU LGA, JAHAR NIGER)
📅 Alhamis, 09/04/2026

🌾 Farashin Kaya:
1.Buhun Masara — ₦24,000 zuwa ₦25,000
2.Buhun Gero — ₦30,000 zuwa ₦31,000
3.Buhun Gyaɗa — ₦23,000 zuwa ₦25,000
4.Buhun Agushi — ₦60,000 zuwa ₦65,000
5.Buhun Dawa — ₦24,000 zuwa ₦25,000
6.Buhun Waken Suya — ₦65,000 zuwa ₦67,000
7.Buhun Jan Wake — ₦75,000 zuwa ₦78,000
8.Buhun Farin Wake — ₦75,000 zuwa ₦77,000
9.Buhun Ƙwara (Ɗiyan Kaɗe) — ₦32,000 zuwa ₦36,000
10.Buhun Ƙwaruru — ₦103,000 zuwa ₦105,000
11.Mudun Shinkafa — ₦1,500 zuwa ₦1,600
12.Buhun Rogo Busasshe — ₦6,500 zuwa ₦7,000
13. Mudun Garin Rogo — ₦500 zuwa ₦600

⛽ Farashin Mai:
• Litan Man Fetur (Gidajen Mai) — ₦1,380 zuwa ₦1,400
• Litan Man Fetur (Black Market) — ₦2,000

✍️ Daga: NURUDDEEN ALHASSAN JIGAWA

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa:“Fiye da ‘yan Iran miliyan 14 masu kishin ƙasa sun riga sun nuna ...
07/04/2026

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa:

“Fiye da ‘yan Iran miliyan 14 masu kishin ƙasa sun riga sun nuna shirinsu na sadaukar da rayukansu domin kare ƙasarsu. Ni ma na kasance, ina, kuma zan ci gaba da kasancewa cikin masu sadaukarwa domin Iran.”

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake fuskantar ƙarin tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

DA ƊUMI-ƊUMI: Bankin Duniya ya amince zai bai wa Najeriya rancen dala miliyan 500 domin bunƙasa harkar noma.Rahotanni su...
02/04/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Bankin Duniya ya amince zai bai wa Najeriya rancen dala miliyan 500 domin bunƙasa harkar noma.

Rahotanni sun nuna cewa wannan rance zai taimaka wajen inganta noman zamani, ƙara yawan abinci, da kuma samar da ayyukan yi ga matasa a faɗin ƙasar. Ana sa ran shirin zai ƙarfafa tattalin arziki musamman a yankunan karkara.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke ƙoƙarin rage dogaro da shigo da abinci daga ƙasashen waje.

Address

NH3, IBIBIO Road
Kaduna North
800283

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tata Trade and Innovation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Tata Trade and Innovation:

Share