Guibi-Hausa Consultancy Services

Guibi-Hausa Consultancy Services Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Guibi-Hausa Consultancy Services, Consulting Agency, We are located at Q. 1. Adamawa Road Kinkinau Kaduna, Kaduna.

We translate books into Hausa language,Edit Hausa books,Organise Seminar/Workshops for Media Houses on Standard Hausa,Translate speeches and review books in Hausa language.

14/02/2025

CELEBRATING DR. ISHAQ IDRIS GUIBI, (PhD)
By:
Nurudeen Dauda
13th February, 2025
[email protected]
[email protected]
nurudeendauda.blogspot.com

Permit me to congratulate Dr. Ishaq Idris Guibi; PhD Language Arts (Hausa); M.A Nigerian African languages (Hausa); Postgraduate Diploma in Education (PGDE) ; and B.A (Hausa) for obtaining his long overdue terminal degree after many years of hard -work, commitment, dedication, doggedness, perseverance, and patience. Your hard -work has finally really paid off. What a great feat Dr! Yours is indeed a product of hard -work, perseverance, and patience! Please accept my best wishes!

Dr. Guibi is a Lecturer in the Department of Languages of the Colleges of Administrative Studies and Social Sciences of Kaduna Polytechnic from 2014 to date. As a Lecturer in the serving Department of the great Kaduna Polytechnic is equally a highly sought after Lecturer in the Department of Mass Communication Kaduna Polytechnic from 2017 to date. He is a highly resource facilitator in the National Open University of Nigeria (NOUN) from 2024 to date.

Dr. Guibi transited from being a highly committed classroom teacher to a veteran journalist, a highly skilled lecturer, a highly sought after media consultant of reckoning, an educationist per excellence, and a Translator with distinctions. In addition, as a versatile scholar with distinctions he is a working encyclopedia of Language Arts with specialization in Hausa education. A highly revered pundit in Hausa Language. A precious asset as well as highly sought after scholar of journalism.

His is a mentor with uncountable mentees. As an academic he published several articles in several academic journals. As a reviewer he reviewed several academic journals and Magazines. As an editor he edited several books and Magazines. As an author he authored several books. As an expert in translation he translated several books. He a

THE CONSTRUCTION OF NEW MILITARY BARRACKS BEGINS IN SOUTHERN KADUNA: THE MURDER OF LATE HON.(MAJOR) IBRAHIM ABDULLAHI ALONE GONIN GORA IN MY MIND! Get link Facebook X Pinterest Email Other Apps February 05, 2025 THE CONSTRUCTION OF NEW MILITARY BARRACKS BEGINS IN SOUTHERN KADUNA: THE MURDER OF LATE....

28/01/2025

**Commendation for Dr. Ishaq Idris Guibi**

It is with great pride and admiration that we commend Dr. Ishaq Idris Guibi for his remarkable achievement in successfully completing his PhD in Hausa Education. His journey has been one of resilience and determination, particularly in the face of challenges posed by other departments that initially refused to accommodate him.

Through his unwavering commitment to education and his passion for the Hausa language, Dr. Guibi found a home in the Education Department, where his intelligence, honesty, and hard work shone brightly. His contributions to the field of Hausa education are not just a testament to his academic prowess but also to his dedication to fostering a deeper understanding and appreciation of the language among students and educators alike.

As he celebrates this significant milestone in his academic career, we recognize Dr. Guibi not only for his scholarly accomplishments but also for the integrity and perseverance he has exhibited throughout this journey. We are confident that he will continue to make meaningful contributions to education and inspire future generations.

Congratulations, Dr. Ishaq Idris Guibi, on your successful convocation! Your achievements reflect not only your hard work but also your potential to make a lasting impact in the field of Hausa education.

Prof Sadiq Mohammed

https://selar.co/h3k26l
31/12/2024

https://selar.co/h3k26l

Wannan littafi an soma buga shi a 2022, sannan aka sabunta shi a 2025. Harshen Hausa ya yi sa'ar gaske saboda yadda ya samu kujera ya hakimce a duniyar aikin jarida Aikin jarida a nan yana nufin jarida, da mujalla, da rediyo, da talabijin, da intanet. Sai dai inda gizo ke saƙar shin ana yi wa ...

08/09/2022

DAGA DANDALIN IS'HAQ IDRIS GUIƁI

Jama'a Assalamu Alaikum baekanmu da asubahin Alhamus, goma sha ɗaya ga watan Safar, shekarar 1444 bayan hijirar cik**akin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da takwas ga watan Satumba, shekarar 2022.

1. Labarin da ya fi ɗaukar hankali jiya a soshiyal midiya, shi ne tsare Tukur Mamu da hukumar tsaro ta DSS ta yi domin yi masa tambayoyi a kan lamuran tsaro. Mamu ya ce tun a Masar aka so k**a shi.

2. Gwamnatin Tarayya, ta yi barazanar sanya ƙafar wando guda, da kamfanonin jiragen sama na ƙasashen waje, da suke ƙin sayar da tikitinsu a Nijeriya da Naira, sai da Dala.

3. Ƙuɗin da suke hannun jama'a da suke jujjuya su, sun ragu zuwa Naira Tiriliyan 3.24 cikin watanni uku.

4. Hukumar Gidajen Rediyo Da Talabijin NBC, ta haranta wa gidajen sa waƙar da Gwanja ya yi mai suna 'WARR'

5. An koka a kan yadda a yanzun a jihar Kaduna, ba a ɗaukar waɗanda s**a karanta aikin kula da lafiya matakin farko wato Community Health Extension Workers CHEW ko JCHEW a asibitoci na ƙananan hukumomi, sai Nas-Nas waɗanda su ba ma zama suke yi a yankunan karkara da aka tura su ba, kuma ba gurabensu ba ne.

6. Ƙungiyar manyan ma'aikatan fetur da gas ta ƙasa PENGASSAN a taƙaice, ta ce za ta yi gagarumar zanga-zanga saboda ƙaruwar satar mai a Nijeriya

7. Sojoji suna kora 'yan Boko Haram, 'yan ISWAP suna bindige su 'yan Boko Haram da sojojin s**a tarwatsa.

8. A jihar Zamfara, an sako masallata su 43 da masu fashin jama'a s**a bi har masallaci suna cikin sallah s**a yi fashinsu.

9. Gwamnatin Tarayya ta ce ta ƙara wa malaman jami'a albashi da kashi ashirin da wani abu cikin ɗari, su kuma s**a ce a kai kasuwa ba sa so.

10. Can na tsinci wata fosta ta Peter Obi, da aka rubuta PETER OBI ZATA KAWO MANA CINGABA. Shi ya sa nake ta sanar da cewa duk wanda yake so in tallata masa ɗan takaransa na siyasa a rubutuna, ko fassara masa fosta, ko littafin manufofi na ɗan takara ko jam'iyya, ko gyara masa Hausar da ya rubuta, ya neme ni a 08023703754.

11. Ma'aikatan hukumar yaɗa labaru ta jihar Kaduna KSMC, da aka sallama aiki tun wuraren farkon shekarar da ta gabata, ba tare da an musu abin da ya dace ba, suna ci gaba da godon a biya su haƙƙoƙinsu.

12. Malaman jami'ar jihar Kaduna KASU, sun ce sun fi ƙarfin dukkan wata barazana da za a musu don su janye yajin aiki.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ina godiya da waɗanda s**a yi tsokaci da kuma addu'a a hotonmu da uwargida na cika shekara talatin da yin aure a jiya. Muna godiya ƙwarai da gaske.

Is'haq Idris Guiɓi
Kaduna Nijeriya.

07/09/2022

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Laraba, goma ga watan Safar, shekarar 1444 bayan hijirar cik**akin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da bakwai ga watan Satumba, shekarar 2022.

1. Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya taya sabuwar Firaministar Birtaniya Liz Truss murna.

2. Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a wata yarjejeniya ta fahimtar juna da ƙasar Poland/Folan bangaren bunƙasa aikin gona da tattalin arziki.

3. Gwamnatin Tarayya, ta kafa wani kwamiti mai mutum goma sha huɗu, da zai sake duba buƙatun malaman jami'a da ke yajin aiki. Sannan an ji gwamnatin tarayya tana cewa ta ƙara wa malaman na jami'a kashi 23.5 na albashinsu.

4. Saboda yawaitar satan man Nijeriya, hukumar tsaron farin kaya da aka fi sani da NSCDC ta rushe sashinta na yaƙi da ɓarnata bututun mai da sauran kayayyaki na man.

6. Cikin mako uku, bankunan kasuwanci sun ci bashin Naira Tiriliyan 4.4 a hannun Babban Bankin Nijeriya.

7. A mako shida, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira Tiriliyan 1.19 daga harajin tamanin kaya wato VAT.

8. An k**a likitan ƙarya a Babban Asibitin Ƙasa da ke Abuja.

9. Duk mai son in tallata masa ɗan takaransa na siyasa ko wata haja tasa a rubutuna na yau da kullum, ko a masa fassara, ko tace rubutu, sai a tintiɓe ni a 08023703754.

10. Ma'aikatan hukumar yaɗa labaru ta jihar Kaduna KSMC, da aka sallama aiki tun wuraren farkon shekarar da ta gabata, ba tare da an biya su haƙƙinsu na sallamar mutum daga aiki rana tsaka ba, suna ci gaba da godon a biya su haƙƙoƙinsu.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga wata tsintuwa da na yi a dandalina k**ar haka:

'WANNAN shi ne asalin karatun BAHAUSHE.
Allah yasa baku manta ba.

أ Alu baki
ب Ba guje
ت Ta guje
ث Cha
ها Ha babba
ج Jin karami
ح Ha karami
خ Ha karami mai ruwa
د Dal
ذ Zal
ر Ra
ز Zai ra
ع An baki
غ An g*i baki
س Sin ara
ش Shin mai ruwa
ص Sadi
ض Radi
ط Damusa hannu
ظ Zwadi
ف Fiy fa iya
ق Qaf waw
ك Kaulasan
ل Lan ara
لاLam tsage
م Min jaye ko mi ara

ن Nu ara
ه Ha kuri
و Waw
ي Ya ara ko Ya zawaidi

Kowa ya karanto
Muji🙏🏻'

Is'haq Idris Guiɓi
Kaduna Nijeriya

06/09/2022

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Talata, tara ga watan Safar, shekarar 1444 bayan hijirar cik**akin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da shida ga watan Satumba, shekarar 2022.

1. Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ba da umarnin dakatar da yunƙurin da ake yi na ƙarin kuɗin kiran waya.

2. Lai da Magashi, sun ce kwanan matsalar taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya ya ƙare sai dai uwarta ta haifi wata.

3. Gwamnatin Tarayya, ta ƙwace wasu kaddarori goma sha huɗu, da suke da nasaba da dakataccen ɗan sanda Abba Kyari, ta kuma tsara tuhume-tuhume kusan 24 da take masa.

4. Yau ministan ilimi da shugabannin jami'o'i da iyayen jami'o'i da hukumomin gudanarwa na jami'o'i, za su taru domin tattauna yajin aikin da malaman jami'a suke kan yi. A dai jihar Kaduna, mahukuntan jami'ar jihar Kaduna, sun ba malaman jami'ar zuwa jiya, ko su koma aiki, ko malaman su gani a ƙwaryar cin su ko ta shan su.

5. Kamfanin mai na ƙasa NNPC, ya ce Allah kuwa da gaske ne a kullum ana shan man fetur lita miliyan sittin da takwas a ƙasar nan. A ta ɗaya ɓangaren kuma da alamu za a kuma aukawa matsalar man fetur saboda dillalan man na shirin daka barkono su yi yaji.

6. Ana ta yabon kwamishinan tsara birane da raya su na jihar Legas Idris, saboda sauka da ya yi daga kan muƙaminsa, saboda rushewar da wani bene da ake kan gina shi a Lekki ya yi da zuwa yanzun an ciro gawar mutum shida daga ɓaraguzan ginin.

7. Mutanen yankin Kinkinau da na Unguwar Mu'azu da ke cikin garin Kaduna, sun yaba wa ɗan takaran majalisar dokoki ta jihar Kaduna na jam'iyyar APGA na mazaɓar Tudun Wadar Kaduna, Aminu Soja Gida Gida, saboda ƙoƙarin da yake yi ɓangaren tsaro har ya kafa JTF ta Unguwar Mu'azu da Kinkinau. Ya kuma koya wa yara da mata sana'o'i na dogaro da kai, da ci gaba da taimaka wa marasa galihu.

8. Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP da Boko Haram su biyar, da mayaƙansu fiye da ɗari biyu a jihar Barno.

9. Ma'aikatan hukumar yaɗa labaru ta jihar Kaduna KSMC, da aka sallama aiki tun wuraren farkon shekarar da ta gabata, ba tare da an biya su abin da akan ba ma'aikacin da aka sallama rana tsaka ba, suna ci gaba da godon a biya su haƙƙoƙinsu.

10. Ina sake tunatarwa cewa, duk mai son a tallata masa ɗan takaransa na siyasa, ko wata haja tasa a rubutuna, ya tintiɓe ni. Haka ma idan mutum yana so a fassara masa takarda ko jawabi ko talla da sauransu. Lambar da za a tintiɓe ni ita ce 08023703754.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga wata tsintuwa da na yi a fesbuk k**ar haka:

'GARAB'ASAR DA KE A CIKIN AUREN BAK'AUYIYA

Bincike ya tabbatar kuma duniya ta sheda cewa matan kauye sun fi kowace mace dadin zama, domin su da gaske suke zaman auren, babu son kudi ko son kyale kyaletun duniya, babu bani-bani b***e a ji kansu da miji, ga aurensu babu wani lefe😂

Bugu da qari duk abin da ka kawo gidanka shi zata dafa maka ko da dawa ce, miya in dai taji daddawa da farin magi ta isheta ba dole sai da naman miya ba, kuma a haka zaka ji girkinta akwai dadin d'and'ano 😋

Da ita ake zuwa noma ko kiwo, ita ke yo itace, tayi surfe tayo nik'a, tayi bakace kuma ita zata dafa ta kai gona mijinta da 'ya'yanta su ci, wanki da zuwa rafi duka ita ce😭

Wata fa'ida da alfanun auren bak'auyiya shine sam bata san wani abu wai shi 'yanci ba, ita kawai ta tashi ta ga gyatumarta tana ta bautawa gyatuminta bilhakki da gaskiya, kuma suna ji malamai suna cewa aljannar mace tana a qasan tafin qafar mijinta, saboda haka ido rufe suke neman aljannarsu a gidan aure 🙏

Malam auren bak'auyiya duniya ne, idan har kana son ka rayu a gidanka k**ar wani sarki to ka tafi kauye ka auro bak'auyiya abinka, idan ka aurota ka koya mata ABC da Alifun-ba'un da karatun sallah, ka dai karkad'e mata duhun jahilcinta🤣

Sai dai kai kuma kaji tsoron Allah kada ka danne mata hakki kuma ka rage mata wahalhalun aikin cikin gida, kuma watarana ka zagaya da ita ta ga birni, ka dan saya mata shawarma da Rufaidah Drinks , yoghurt 🏃

Duk wanda ya shirya auren bak'auyiya to ya bini inbox nayi masa rijista 😝

Alameen Kowa Naka 🖊️'

Is'haq Idris Guiɓi
Kaduna Nijeriya.

05/09/2022

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Litinin, takwas ga watan Safar, shekarar 1444 bayan hijirar cik**akin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu S. A. W. Daidai da biyar ga watan Satumba, shekarar 2022.

1. Shugaban Hukumar Kwastam Hamid Ali, ya sake jaddada cewa duk wani batu da ake yi na cewa ana tallafi ga man fetur, damfara ce kawai ake yi, take ƙarewa a kan tallaka.

2. Ƙungiyar SERAP mai rajin kare haƙƙin talaka, ta nemi shugaban ƙasa Buhari, ya janye sunayen mutanen da ya aike wa Majalisar Dattawa ta amince da su a matsayin kwamishinonin zaɓe, waɗanda 'yan jam'iyyar APC ne, domin ba za su yi adalci ba a zaɓukan shekara mai zuwa.

3. Shugaban 'yan sandan Nijeriya, ya ba da tabbacin babu wata barazana da za ta hana gudanar da zaɓukan shekara mai zuwa.

4. A wata ɗaya kacal, Nijeriya ta samu giɓin kuɗi Naira Biliyan 524 da 'yan kai.

5. 'Yan Boko Haram sun kutsa wani masallaci s**a kashe limamin da ke limancin sallah da sauran masallata da ke bin limamin sallah a jihar Barno.

6. Ambaliya tana neman raba jihar Gwambe da sauran jihohi da take maƙwabtaka da su.

7. Waɗanda s**a yi fashin wani shugaban gundumar raya ƙasa a jihar Zamfara, sun masa kuɗi Naira Miliyan Ashirin.

8. Makarantar horar da ƙananan hafsoshin 'yan sanda da ke Wudil, ta koka a game da yadda jaridar Sahara Reporters, ta tasa makarantar a gaba tana neman sai ta ga bayanta.

9. A jihar Kaduna, an k**a masu yi wa mutane cinne ga masu fashin jama'a a unguwa, su uku da aka fi sani da INFORMANTS a yankin ƙaramar hukumar Igabi.

10. Ma'aikatan hukumar yaɗa labaru ta jihar Kaduna KSMC, da aka sallama aiki tun wuraren farkon shekarar da ta gabata, ba tare da an biya su haƙƙoƙin da ake ba ma'aikacin da za a sallama rana tsaka ba, suna ci gaba da godon a biya su haƙƙoƙinsu.

11. Ina sake sanar da jama'a duk mai son tallata masa ɗan takaransa na siyasa a rubutuna, ko wata haja da yake da ita, ko yake buƙatar fassara ko tace jawabi ko littafi, ya tintiɓe ni a 08023703754.

Mu wayi gari lafiya. 'Yan naziri da firamare da sakandare da suke shirin komawa makaranta a yau, a koma lafiya.

Af! Ga wata tsintuwa da na yi a dandalina na wasaf da na ga Muhammad Shehu Samaru ya sa. k**ar haka:

'A DAURE KARANTA: KARANCIN MAZAJEN AURE!!!

Karancin mazajen aure na daga cikin manyan qalubale da yanmata ke fuskanta a wannan zamanin.

Idan zamu waiwaya watan Ramadan daya gabata, yawancin addu'a da yanmata s**a gabatar kuma s**a nema ayi musu shine samun abokin zama na aure.

Hakan kuma zai sanya zukatanmu tunanin lokacin iyayenmu shin akwai irin wannan qarancin mazajen auren? Ko kuma lokacin nasu akwai yawaitan mazaje sama da mata ne? Ko kuma yawaitan mazajen da matan suna kunnen doki? Kada muyi tunanin hakan. Wataqila wancaan lokacin mata sunada qima da kuma daraja yadda aka tarbiyan tar dasu domin a gina gida dasu bawai a shiga ginanne gida dasu ba.

A wancaan lokacin, da zarar matashi ya kai aure kuma zai iya ciyarda kanshi da matar shi, sai yafara neman aure, kuma tabbass macen dayake aura takan taimaka mishi gaya wajen gina future dinshi.

Abinda nake qoqarin isarwa anan shine: yanmata da kansu s**a kirkiri "KARANCIN MAZAJEN AURE".

Yau abun ya canja zani ya rikide yazama wani abun daban. Kasamu yarinya matashiya 13-16 years ka tambayeta wani irin Miji takeso ta aura? Zakaji abubuwa k**ar haka: "Dole yazama dogo ne mai fadin kirgi, kyakkyawa mai kudi kalan zuwa unguwa, yanada motar hawa da kuma gida, wanda zai iya nuna shi a ko ina nace shine mijina. Sannan daga bisani kaje ta hada da: "Kuma mai tsoron Allah" wai don kada ace tanason duniya.

Idan kayi wannan bincike ka samu wannan amsar, saika duba unguwarku kaga samari nawa ne s**a cika wadannan sharuda, anan zakaga matsalar.

Zakaji yanmata suna cewa: "bazai yiyu nasha wahala a gidan Ubana ba kuma naje gidan wani gardi inashan wahala". Hankali irin na tinkiya kenan.

Yake Yar'uwa! Idan daga farko kinyi auren komai na tafiya daidai sannan daga bisani kuma duniya tawa Mijin naki daurin tomtom?🤔, guduwa zakiyi kenan?.

Babu wanda ke fatan shan wahala, ammana zaifi dadi a fara da wuya daga bisani aji dadi, sai yazamana anyi karshe mai kyau.

Matsalar kuma shine: irin yadda yara mata ke kwatanta irin mazajen da zasu aura kusan duk daya ne.

Idan yanmata 50 suna muradin auren irin wannan miji daya cika sharuda, sannan kuma namijin daya cika wadannan sharuda nasu 1 ne kacaal, kuma namijin mace 1 zai dauka a cikinsu, toh sauran yanmata 49 din yaya kenan?

Nanfa zakaji sunfara lamenting: "KARANCIN MAZAJEN AURE".

Wani abun dubawa kuma a wannan zamanin namu shine: zaiyi matuqar wahala saboda yanayin tattalin arzikin kasarmu kasamu matashi mai matsakaitan shekaru da baiyi aure ba da wadannan sharudan da yanmatan yanxu ke so..

Idan zaka lura, yawancin yanmata masu niyyar aure sunyi aure domin basuda buri illa miji nagari dazasu aura su gina gida tare dashi.

Hanya daya da zakibi kisamu mijin aure shine cikin wassu sharuda dakika gindaya na irin Mijin dakike so.

Shifa Mijin aure, mutum ne da Allah Ya halitta kuma aka halicci mace daga gareshi domin tallafa mishi da cik**ar martabar shi.

Yak**ata Yanmatan zamani su gane cewa: "AURE BAWANI SHIRI BANE NA RAGE RADADIN FATARA".

Aure ibada ce, hanyace ta bautar Ubangiji. Wadanda s**a dauki aure a matsayin wata hanyar ficewa daga talauci, suke shiga damuwa.

Mata sune masu gina gidaje, bawai masu duma gidaje ba............

Yar'uwa kada ki rude ki dauka hanyar da namiji ke kai yanxu yatace qaddararsa, a'a wannan hanyar dakika ganshi a kai yau wataqila hanyace da Ubangiji Ya nufa zaibi kafin ya kai ga qaddararshi.

Wani abun kuma shine baki san ko cewa qaddar tashi tare zaku isa wajen ba, meye zai hana duk wanda kika aminta dashi da dabi'unsa da addininshi ki dauke shi a matsayin mijin auren ki?

Ya Ubangiji Ka ganar da yanmata sune ke janyowa kansu karancin mazajen aure ba wassu ba, Ka kuma hada maso buqatar auren da mazajen nagartattu.

Fatan alkairee gakowa🙏'

Is'haq Idris Guiɓi
Kaduna Nijeriya.

04/09/2022

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Lahadi, bakwai ga watan Safar, shekarar 1444 bayan hijirar cik**akin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da huɗu ga watan Satumba, shekarar 2022.

1. Gwamnatin Tarayya ta nanata cewa no work no pay ga malaman jami'a da ke yajin aiki. Wata dai na bakwai ke nan da gwamnati ta dakatar da albashin malaman da ke yajin aikin. Malaman sun ce ba gudu ba ja da baya. Yajin aiki ya ci gaba.

2. Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani rumbun tattara bayanai da adana su, na dukkan wanda wata hukuma ta tsaro ta k**a.

3. Hukumomin 'yan sanda suna nan suna bincikar wani ɗan sanda, da ake zargin ya nemi ya yi lalata da wata budurwa mai shekara 17 da aka tsare ta a ofishin 'yan sanda.

4. Gwamnatin Tarayya, ta ƙara wa ministoci da manyan sakatarori da sauransu, yawan kuɗin alawus na tafiye-tafiye.

5. Hukumomin soja, sun ɓullo da wata horarwa ta soja ta dole ta mako shida, ga yara da s**a kammala makarantar 'ya'yan sojoji da aka fi sani da Military School.

6. Kotu ta wanke tsohon gwamnan jihar Filato Jonah Jang, daga zargin da ake masa na ya wawuri wata Naira Biliyan shida da kusan rabi.

7. A jihar Zamfara masu fashin jama'a sun yi fashin liman da masallata masu yawan gaske a lokacin sallar Jumu'a.

8. A jihar Katsina masu fashin jama'a, sun je rugar fulani, s**a yi fashin fulani da dabbobinsu. Haka nan masu bin jama'a har gida su yi fashinsu sun addabi mutanen Funtuwa.

9. Ƙungiyar Makira Waya ta jihar Kaduna, za ta gudanar da wani babban taronta a Lahadin nan a Kaduna, inda aka gayyaci malamanmu da mu ɗalibai, mu gabatar da maƙaloli. Tawa maƙalar ita ce Dangantar Makira Waya Da Kafofin Watsa Labaru.

10. Ma'aikatan hukumar yaɗa labaru ta jihar Kaduna KSMC, da aka sallama aiki tun wuraren farkon shekarar da ta gabata, ba tare da an biya su abin da ya k**ata a biya su idan za a sallami ma'aikaci rana tsaka ba, suna ci gaba da godon a biya su haƙƙoƙinsu.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga wata tsintuwar da na yi a fesbuk. Tsintuwa ce kashi ta biyu domin kuwa na taɓa kawo muku kashinta na farko. Ga ta k**ar haka:

'Daga Waziri Aku
ASALIN TAGUWA 2

Kamar yadda na ce idan Allah ya kai mu amaryar wata zan koma ƙauye wurin Kaka Tasalla domin jin tarihin asalin taguwa. To, da ranar ta zo sai na haye babur ɗina na nufin ƙauyen. A kan hanya na ga gonakin da aka noma an fara girbe gero, waɗanda kuma aka bari saura saboda matsalar 'yan ta'adda, duk hambama ta cika su. A nan na gane lallai damina ta tsufa.

Da na isa gidan sai na tarar da matan wan mahaifina a gindin murhu suna gasa tumu, yara kuma sun samo taure a gona suna sha, wasu kuma na shan takanɗa. Na kafe mashin kusa da dabin tumaki, muka g*isa da matan gidan na nufi ɗakin Kaka, na same ta a kan karauni tana taɓa ƙailula. Na yi sallama, ta yi zumut, k**ar wadda aka tsikara da allura, ta tashi zaune tana murje idanu.

Ta dube ni ta ce, "Garbati, kai ne tafe da yamman nan?"

Na ce mata, "I, ni ne Kaka." Na zauna a gefen gado, na fara raba idanu k**ar yadda na saba, ina kallon tarkacen da ke cikin ɗakin. Bayan mun g*isa sai ta jawo gidauniya ta yi mini idon kwaɗi ta ba ni. Na karɓa na shanye. Ita kuma ta ɓalli goro ta jefa baka. Ta kalli kayan da ke jikina ta ce, "ko kai fa ɗan nan, ka ga yau dai ka yi shiga irin tamu ta Hausawa, ba k**ar kwanaki da ka zo da shigar Nasaru ba."

Na ce, "to, da ma zuwa na yi ki faɗa mini tarihin asalin taguwa tun da kin ce ba daga Turawa muka kwaikwaye ta ba."

Ta ce, "af, an kuwa yi haka. Ai na gaya maka tun kan a haifi uwar mai sabulu balbela take da farinta. Ko da Nasaru s**a zo sun iske mu da suturunmu."

Ta zubar da yawu kana ta ci gaba, "Tun can tale-tale Bahaushe bai da wata sutura da ta wuce mayafin saƙi, shi yake ɗaurawa a ƙugu sannan ya yafa shi saman kafaɗa har ya sauka bisa gadon bayansa. Ana kiran wannan shiga da suna lage. To akwai wani mutum wai shi Guwa wanda mayafi ɗaya kurum gare shi, ko datti mayafin nan nasa ya yi, idan zai wanke shi, sai dai ya yi ƙato-gulbi.

Ana nan har mayafin nan ya kai ga hujewa a tsakiyarsa. Da Guwa ya ga haka, ya rasa yadda zai yi, sai wata dabara ta faɗo masa a rai. Ya ƙuga kansa inda mayafin ya huje, sai ko ya ga ya sauka ya rufe masa jiki kaf. Ya samu ɓawon ice ya yi ɗamara don kada iska ya riƙa ɗage shi. Da ya fita waje mutane s**a gan shi, sai s**a yi sha'awar shigar da ya yi. S**a riƙa huje mayafinsu a tsakiya suna cewa bari mu yi ta-Guwa, watau irin dabarar Guwa."

Kaka ta dube ni ta ce, "to ka ji asalin taguwa. Daga bisani kuma aka samu dabarar ɗinke gefe da gefe na mayafin aka daina yin ɗamara. Don haka rigar Bahaushe ta farko ita ce 'yar shara, wacce ake fid da wuya kawai babu hannuwa. Daga nan Nasaru s**a gani su ma s**a kwaikwaya."

Na yi dariya na ce, "ikon Allah, lallai Bahaushe akwai hikima."

Ta riƙe baki ta ce, "kai ɗan nan, me ka ɗauki Bahaushe hala? Ba ka san cewa asalinsa daga Misira yake ba? Ko ba ka san cewa Misira ce tushen ilmi da wayewar kai a duniya ba? Don haka ba abin mamaki ba ne don Bahaushe ya daɗe da wayewa a duniya."

Na ce, "toh, ai ni ban sani ba. Amma wata rana zan so na ji wannan tarihi." Na miƙe tsaye ganin hantsin gwauro ya fara kawo jiki. Muka yi sallama da Kaka, na ba ta na goro na fita. Na bar matan gidan na ɗibar garafuni a jikin damfami, na haye mashin ɗina na nufi gida.
..

Ga ƙarin wasu kalmomin da muke so a gano mana ma'anarsu k**ar yadda s**a fito a cikin labarin:

1. Saura.
2. Hambama.
3. Tumu.
4. Taure.
5. Takanɗa.
6. Dabi.
7. Karauni.
8. Ƙailula.
9. Idon kwaɗi.
10. Ƙato-gulbi.
11. Hantsin gwauro.
12. Garafuni.
13. Damfami.

Bukar Mada
03/09/2022

'

Is'haq Idris Guiɓi
Kaduna Nijeriya

03/09/2022

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Asabar, shida ga watan Safar, shekarar 1444 bayan hijirar cik**akin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da uku ga watan Satumba, shekarar 2022.

Da fatan yau za a gafarce ni saboda matsala ra wutar lantarki ban iya kalato muku labari ko ɗaya ba. A 'yan kwanakin nan wutar sai ci gaba da raɓarɓarewa take yi. A yini da ƙyar a samu wutar minti talatin. Talaka zai ci gaba da biyan kuɗin zama a duhu a zamanin mulkin masu gaskiya. Ga Hamid Ali ma ya ce damfarar talakan Nijeriya ake yi da ake cewa wai ana biyan kuɗin tallafin mai.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ga wata tsintuwa da na yi a dandalina da na ga Muhammad Kakuri ya sa. Ina kyautata zaton shi ya rubuta k**ar haka:

'MAƊIGO (LE***AN) NA NEMAN CIN ƳAN MATAN AREWA DA YAƘI!

Koda yake ba yau na soma yin sharhi akan wannan lamari na Maɗigo ba, saidai a wannan karon nazo muku da wani ƙwarya-ƙwaryan bincike da muka yi haɗaka wajen gudanar dashi tare da yin sharhi na bai ɗaya dangane da wannan lamari daya yaɗu tsakanin Matan Arewa.

Mun gudanar da wani zuzzurfan bincike da nazari na musamman akan Matan Arewa ƴan Mata, Zaurawa da Matan Aure fiye da guda dubu biyu da ɗari huɗu da sittin da biyu (2,462).

Mun gudanar da wannan bincike ne ta dandalin sadarwa daban-daban na Yanar Gizo k**a daga kan What'sapp, Facebook da Instagram inda muka gano fiye da kaso arba’in 40% cikin ɗari 100% na Matan da muka bibiya Hausawa ne kuma mafi yawanci ƴan Mata ne da basu taɓa Aure ba wanda aka yaudari tunanin su s**a shiga cikin wannan harka ta Maɗigo (Le***an).

Bayan bin diddigi da nazarin rayuwar waɗan nan ƴan Mata munyi fargabar cewa akwai yiwuwar Jihar Kano ta zamo ta ɗaya (1st) dake da kaso mafi yawa na ƴan Mata da Matan Aure ƴan Maɗigo a faɗin Arewacin Najeriya duba da yawan Matan ƴan asalin Jihar Kano da muka ci karo dasu suna wannan harkar.

Shin menene musabbabin yaɗuwar Maɗigo a yankin Arewacin Najeriya?

Gaskiyar magana akwai hanyoyi da dama dake da nasaba da yaɗuwar harkokin Maɗigo a yankin Arewacin ƙasar nan, saidai mun fi karkata hankalin mu akan wasu abubuwa da muke ganin sune ummul aba’isin yaɗuwar wannan Fasiƙanci a yankin Arewa.

NA FARKO! SHAGULGULAN BIKI KO PARTY..

Yana daga cikin manya-manyan hanyoyin da ƙungiyoyin Maɗigo na Duniya ke bi wajen yaɗa ayyukan su a faɗin Duniya wato shirya shagulgula da sharholiyar sheɗanci.

Haƙiƙa wannan ɗabi’a da aka bijiro da ita cikin al’ummar Hausawa na shagulgulan biki da casun Party mafi yawancin lokuta a cikin ɗakunan taron bukukuwa na Event Center a turance suna da nasaba wajen buɗewa Mata ƴan Maɗigo ƙofar shiga jikin ƴaƴan Hausawa su koyar dasu wannan mummunar ta’ada tasu.

Ko ban faɗa ba dani daku muna ganin yadda taruka a gidajen casu (Event Center) yake sauya salo da tunanin ƴan Matan Hausawa daga Al’adu da shiga irin ta Malam Bahaushe zuwa shiga irin na rashin tarbiyya da zubewar kima da Mutuncin al’ummar Hausawa.

Abin lura shine ganin yadda yayin gabatar da ire-iren waɗancen shagulgulan ƴan Matan Hausawa ke yin ɗinke-ɗinke na rashin Ɗa’a tare da yin raye-raye na rashin kima a gaban Iyaye da dangi da sauran mahalarta taron batare da nuna kunya irin ta Hausa Fulani ba.

To a irin wannan lokutan na shagulgulan biki ko Party Mata ƴan Maɗigo kan samu dama wajen ƙulla ƙawance da ƴan Matan da s**a lura ruwan su isa wanka inda daga bisani suke amfani da ƙwarewa wajen shawo kansu har su kai ga shiga wannan harka ta Fasiƙanci.

NA BIYU! SHAFUKAN YANAR GIZO (INTERNET)..

Har’ila yau a cikin jerin binciken mu, a iya Manhajar Facebook kaɗai mun gano Mata guda dubu biyu da ɗari ɗaya da sha takwas (2,118) dake da alaƙa da harkokin Maɗigo kuma kusan dukkan su Hausawa ne daga Jihohin Arewacin Najeriya.

Daga cikin su guda ɗari shida da tamanin da huɗu (684) Matan Aure ne, sai guda ɗari huɗu da takwas (408) Zaurawa, sai ragowar guda dubu ɗaya da ishirin da shida (1,026) wanda sun kasance ƴan Mata ne k**ar yadda kowacce ta bayyana a Profile Info ɗin ta, da kuma waƴanda muka bi diddigi muka tabbatar da haka.

Domin kore shakku akwai ƴan Mata sama da guda ɗari (100+) da Matan Aure sama da guda ishirin (20+) daga cikin waɗanda muka bibiya yanzu haka a cikin jerin Firends ɗina na facebook kuma muna da cikakkiyar shedar cewa suna da alaƙa da harkar Maɗigo.

Koda yake hakan bazai shafi alaƙa ta dasu ba domin yanzu haka ina zantawa da wasu daga cikin su kuma ina samun wasu bayanan sirri, harma nakan leƙa Groups ɗin su a wasu lokutan domin samun bayanan da nake nema.

Daga cikin bayanan da nake samu a wajen wasu ƴan Mata wanda s**a tsinci kansu cikin wannan harka kuma suke neman hanyoyin da zasu bi domin barin ta, na samu bayanai akan shafukan sirri na ƴan Maɗigo sama da guda arba’in (40+) a wannan dandalin na Facebook.

Kuma hakan ya sake tabbatar min da nagartar binciken mu wanda muka yi ƙiyasin cewa akwai shafukan sirri na ƴan Maɗigo mai tarin yawa a Facebook inda wasu da dama ke fakewa da tallan kayan Mata suna yaudarar su zuwa harkar Maɗigo.

Daga cikin ire-iren waɗan nan shafuka kusan kaso sittin 60% cikin ɗari 100% mallakin ƴan Maɗigo ne, haka nan mabiyan su kusan duk ƴan matan Arewa ne da Samari Kawalai wato masu haɗa Kasuwanci na Zinace-Zinace ta Yanar Gizo (S*x Connection).

NA UKU! AMFANI DA KAYAN MATA..

Idan aka ce kayan Mata ana nufin magungunan gargajiya ko (Herbal Medicine) da Matan Aure ke amfani dasu na gyaran Jiki a wasu lokutan harda mallake Mazajen su.

To a wannan Zamanin ba kawai Matan Aure ne ke amfani da kayan Mata ba, binciken mu ya gano yadda da yawa ƴan Matan Arewa ke amfani da ire-iren waɗan nan magunguna batare da sunyi koda Auren fari ba.

Saidai hakan nada nasaba da Iyayen su Mata domin da zarar ƴaƴan su sun Balaga sai su yaye musu Hijabi su dinga bayyana musu wasu sirrika na Auratayya tare da ɗora su akan magungunan Mata batare da tunanin irin hatsarin dake tattare da amfani da magungunan ga Macen da batayi Aure ba alhali tana Balagaggiya.

To da zarar Yarinya ta sha wancan tayi matsi da wancan sai tunani daban-daban na buƙata su dinga bijiro Mata wanda a irin wannan yanayi da dama Yan Mata basu fiye jurewa ba har hakan kansa su soma jarraba ɗabi’ar nan ta biya wa kai buƙata wato Istimna’i (Ma********on) da hannu ko wani abu mak**ancin haka domin samun biyan buƙata.

Wannan bincike ne da muka gudanar akan Mata da yawa musamman ƴan Mata kuma tabbas muna da tabbaci da yawa yan Mata a wannan Zamanin suna aikata Istimna’i (Ma********on) harma s**an kira Samarin su a waya domin suyi musu zantuttukan Batsa (S*x Chat) ta yadda zasu samu nishaɗi yayin da suke yin Istimna’in domin hakan rage wa kai raɗaɗin sha’awa ne a wajen su.

Saidai a nazarin binciken mu mun gano yin Istimna’i (Ma********on) ga ƴa Mace na ɗaya daga cikin somi-somin shiga harkar Maɗigo gareta kasancewar duk wadda ke wasa da kanta bata fiye bijirewa yayin da ƴar uwar ta Mace ta nemi yin wasa da ita domin biyan buƙata ba.

Dan haka amfani da kayan Mata ga Mace Budurwa ba daidai bane matuƙar idan zai iya tara Mata sha’awa a marar ta da sunan ƙarin Ni’imah, dan haka Iyaye Mata ku kiyaye da irin magungunan da kuke shayar da ƴaƴan ku.

NA HUƊU! MAKARANTUN ZAMANI..

Mu lura ƴan Mata kanyi ƙawaye daban-daban a Makaranta saidai mafi yawanci ƴan Matan suna ƙulla ƙawance da ƴan Maɗigo a Makarantun kwana ko manyan Makarantu na Jami’a batare da sun fahimci hakan ba.

Koda yake da yawa ƴan Matan dake Makarantun kwana s**an yi harkokin Maɗigon su ne a cikin Makaranta kodai a ɗakunan kwanan su ko banɗaki ko a wasu keɓantattun waje na cikin Makaranta domin yana wahala su haɗu idan ba’a cikin Makaranta ba.

Su kuwa ƴan Matan Jami’a kan ƙulla ƙawance har s**ai ga ziyartar gidajen juna tare da fice-ficen zuwa unguwa, yau ana gidan su wance gobe a nufi gidan su wance.

Girman ƙawancen su kansa su ƙirƙiri wasu Groups na Chatting mafi yawanci a manhajar What'sapp inda a ciki suke tattaunawa da juna tare da nishaɗantar da juna a wasu lokutan s**an haɗa casu (Party) ko Get Together cikin salo na abota.

A lokutan gudanar da Shagulgulan s**an bayyana irin kayan da suke buƙatar kowacce tasa wanda a mafi yawanci riga ƴar kanti ce (T-shirt) da wando ɗan kanti ko buje (Jeans - Skirt) wanda mafi yawanci suke matse jikin su dukkan Diri da Surar su ta bayyana.

To saidai masu yin Maɗigo a cikin su kanyi amfani da wannan dama wajen jan hankalin wasu daga cikin ƴan Matan zuwa Group ɗin su na zallar ƴan Mata masu harkar Maɗigo domin a duk lokacin da Mace ƴar Maɗigo taga Mace mai kyakkyawan Diri hankalin ta kan tashi harma taji Sha’awar haɗa mu'amula da ita.

Dan haka a ɓangaren Makarantu musamman Makarantun kwana akwai matuƙar wahala shawo kan lamarin, saidai muna kira ga Iyaye ya zamo wajibi garesu susa ido akan irin ƙawayen dake ziyartar ƴaƴan su da kuma irin fice-ficen da s**a dace su dinga yi tare da ƙawayen su.

Idan bai zama wajibi ba zaifi k**ata ƴaƴan ku Mata suyi Karatu a gaban ku, a ɓangaren Karatun Jami’a kuwa zaifi kyau kuyi musu Aure, idan Mijin su na da ra’ayi suyi Karatun Jami’ar a gidan shi yafi.

NA BIYAR! SHAFAR AL’JANNU..

A wani abu mai k**a da ban mamaki game da Mata ƴan Maɗigo shine, da yawan su suna da matsalar shafar baƙin Al’jani mai hana ƴaƴa Mata Aure.

Wannan ne yasa mafi rinjaye na ƴan Maɗigo Mata ne wanda basu taɓa yin Aure ba (Ƴan Mata) kasancewar Al’janin yana cire musu Sha’awar yin Aure amma fa idan sun kwanta bacci suna yin mafarki ana Saduwa dasu inda a wasu lokutan tunanin irin wancen mafarkin kanzo musu a rai har Sha’awar su kan motsa wanda hakan kan jefa su aikata Zina ko Maɗigo ko Istimna’i domin samun sauƙin sha’awa, amma fa duk da haka idan wani yazo musu da batun Aure ba zasu amince ba.

A wasu lokutan kuma Al’janin kan haddasa musu sha’awa mai ƙarfi ta yadda zasu buƙaci Aure amma da zarar sun samu wanda ya tsaya da gaske zai Aure su sai maganar ta lalace, to suma irin waɗan nan ƴan Matan s**an kasa jurewa har s**ai ga shiga harkar Maɗigo ko Zinace-Zinace da Samari domin samun sassauci.

Da dama daga cikin ire-iren waɗan nan Matan dake jimawa babu Aure ƙawayen su ƴan Maɗigo kan yaudare su suna faɗa musu cewa zasu samu biyan buƙata cikin sirri batare da ansan me suke aikatawa ba, kuma babu fargabar ɗaukar ciki tunda bada Maza suke Saduwa ba wanda hakan kanyi tasiri a zukatan su har s**ai ga shiga harkar.

Abin lura shine koda babu shafar Al’jani mafi yawanci na ƴan Matan dake harkar Maɗigo suna da tsananin Sha’awa, hakan yasa suke gwammacewa suyi Maɗigo da ƴan uwan su Mata fiye da yin Zina da Maza domin gudun ɗaukar Ciki kuma hakan kan samar musu cikakken sirri kasancewar ba’a fiye zargin Mata idan suna shige da ficen su ba.

Gaskiyar lamari shine a halin yanzu muna cikin fargabar a cikin kowane rukunin ƴan Mata guda goma (10) akan iya samun ƴan Mata guda huɗu (4) wanda basu taba yin zina da namiji ba amma suna yin Maɗigo (Le***an).

Yawancin Mata ƴan Maɗigo suna da kyawun fuska sannan suna da Diri da yalwar Sura kasancewar suna amfani da kayan Mata na gyaran Jiki kodan saboda su zamo abin sha’awa ga sauran abokan harkar su.

Har yanzu muna kan nazari da bincike akan wannan lamari na Maɗigo kasancewar kullum sabbin hanyoyi suke daɗa ɓullo dasu.

Alhamdulillahi wasu daga cikin waɗanda nake zantawa dasu s**an faɗa min cewa a shirye suke dasu daina wannan harka muddin s**a samu Mijin Aure.

Anan zan dasa aya da fatan Allah ya dubi lamarin ƴan uwan mu Mata musamman na nan Arewacin Najeriya, ya yaye musu wannan masifar data ɓullo cikin su.

Ya Allah ka shirya masu yin wannan harka ka ganar dasu gaskiya, ka kare waɗanda basu shiga cikin ta ba, mu kuma da muke ƙoƙarin ceto al’ummar Annabi ya Allah ka bamu kariya da ƙarfin gwuiwar cigaba da yaƙar duk wani abu daya saɓa da Addinin ka.

Allah ka gafarta mana baki ɗayan mu!'

Is'haq Idris Guɓi
Kaduna Nijeriya

Address

We Are Located At Q. 1. Adamawa Road Kinkinau Kaduna
Kaduna

Telephone

+2348023703754

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Guibi-Hausa Consultancy Services posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Guibi-Hausa Consultancy Services:

Share