21/09/2017
ANKUSA KAIMU BANGO(HAUSAWA)!
Da dai banyi niyyar cewa komai ba, amma ya zama dole ince wani abu, amatsayi na na dan Hausawa mai kishi.
Jama'a shin ya kamata na yi shiru? A'a ya zama dole mu ce wani abu dangane da abinda ya ke faruwa na cin zarafin hausawa da kabilar Igbo ke yi, a wasu sassa na jihohin Najeriya musamman ma jihar Abia.
Mu muna sauraron magabatan mu, kuma muna bin dokokin addinin mu, da dokin kasa, shi ne yasa bamu maida martani kan yayan kabilar Igbo'n da suke zama a yankunan mu na Arewa.
Amma da alamun kuma wannan ladabi da bin dokin kasar da muke, yana sa ya yan kabilar Igbo nayi mana kallon wawaye, ko kuma matsorata, wallahi ba zasu iya bamu tsoro ba. kabilar Igbo nawa ta ke a Najeriya? Ya kamata shugabanni da mahukunta su sani cewa fa ankusa kaimu bango. Domin hakuri, biyayya da bin dokokin mu, sun kusa karewa idan ba'a gaggauta daukan mataki ba. Wai ku yan kabilar Igbo manyan ku sun mutu ne? Ko kuma dai ku baku da biyayya ne? Ko kuma a'a Ku kawai masu saba dokokin kasa ne, ko kuma ace da ku yan tawaye ne? Ko kuma dai yin ta'addanci ne ke burge ku?
Wani ma abun tambaya ma wai jihohin ku babu gwamnoni ne? Musamman jihar Abia, kodai gwamnan na ku yana tare da ku akan abinda kuke aikatawa ne? Ya kamata a tuhumi gwamnan jihar abia a gaskiya, idan har za'a fito ana kashe mutane da cin zarafin yan kasa amma baya daukar wani mataki. Fafutukar kafa biafara da Nyamurai ke yi, wannan tsakanin su da gwamnati ne, amma kashe mana yan uwa, wallahi ba zamu yi shiru ba.
Muda yake muna bin doka, shine har wasu gwamnoni a jihohin mu suna bada kariya ga yan kabilar igbo, cewa ba wanda ya isa ya taba su, to mu bamu damu ba, amma fa aja kunnen su, kuma a hunkunta su, su bar mana yan uwan mu suyi rayiwar su a ko'ina a Najeriya, sabo da hausawa yan kasa ne kamar kowa, asali ma sune ke da kaso mafi yawa a taswirar Najeriya. Idan ba haka ba wallahi babu wani gwamna a arewa da zaiyi mana barazana idan aka kaimu bango.
Da fatan Allah ya daukaka Najeriya