09/07/2026
An Tambayi Masussuka Cewa Idan Salla Ta Wuce Mutum Zai Rama Yace a'a, Amma an tambayi Professor Bashir Aliyu Irin Tambayar Ga Amsar Da Ya Bayar 👇🏼
"Ya ce hukuncin ramuwar sallah ance lokaci ake sallata idan lokacin sallah ya wuce ba a rama sallah? A'a cew lokaci ake sallata wannan kuskure ne ace in lokacin sallah ya wuce ba a rama sallah, In lokacin sallah ya wuce saboda mutum ya manta ko yayi bacci zai rama sallah. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yace:' Wanda yayi bacci baiyi sallah ba ko kuma ya manta sallar, to ya sallace ta idan ya tuna bata da ramuwa” Wato yayin da ya tuna wannan shine lokacin ta.
Amma cewar ba a rama sallah wannan ga wanda ya ganganta barin sallah ne har lokacin ta ya fita, To shine wadansu malamai suke cewa ko ya rama sallah wannan ramuwar bata yi ba domin ita sallah tunda Allah yace 'Kanat 'alal-mu'minina kitaban mauquta' tana da lokaci iyakkantacce akan muminai, wajibi ce akan muminai a lokaci iyakkantacce. Ma'ana idan lokacin ya fita shikenan takubce wannan shi ne ra'ayin wadansu malamai amma mun sha rinjayar da maganar malaman da take cewa wanda ya bar sallah da ganganci shi ne 'min babil-aula ya rama.' Za'a karba ko baza'a karba ba wannan hukuncin kuma yana wajen Allah Jalla Wa'ala. Amma in an nemi wanda yake bisa kuskure ya rama wanda yaki yi da ganganci min babil-aula a neme shi ya rama.
Saboda ba zai yiwu ba ace wanda ya ganganta barin abinda yake hakki a kansa shi baza'a karba ba bazai yi ba amma wanda yayi bisa mantuwa wanda yake yana da uzuri ance masa ya yi, Shi kuma wancan wanda yake bashi da uzuri baza'a ce masa ya yi ba ai 'nutalibuhu' zamu neme shi ya rama. Amma cewa wannan ramuwar ta wadatar masa ko bata wadatar masa ba wannan hukuncin yana wajen Allah Jalla Wa'ala. Sai dai tunda wannan wajibi ne da yake a kansa zimmarsa nauyin da yake wiyarsa bazai kubuta ba har sai yayi wannan sallah. Wannan karba da rashin karba yana wajen Allah, amma mu a wajen mu zamu nemi kan cewar wajibin nan yana nan a kansa bazai kubuta ba har sai yayi, wannan nauyin yana kansa, bazai sauke shi ba sai yayi. Allah ya karba Allah bai karba ba wannan sai a kyale kuma hukunci yana wajen Allah Jalla Wa'ala. Amma sai yayi ta, wannan shine abinda jumhurun malamai suke a kai."