06/10/2023
NEMAN AGAJIN GOMNATI AKAN TITIN MAKODA ZUWA DANBATTA.
____________________________________
A madadin Al,ummar karamar hukumar makoda muke neman agajin mahukunta akan titinmu da yatashi daga cikin garin Makoda zuwa Dambatta duba da yadda ya lala ce,lala cewar da takai ake yawan samin haddura sosai akan hanyar ta MAKODA zuwa DAMBATTA a takaicedai titin yazama tamkar tarkon mutuwa da raunika ga Al,ummar da ke zirga zirga akan hanyar,wan nan dalilin ne yasa muke kira ga mahukunta Wanda abin ya shafa dasu kawo mana agajin gaggawa ga duk wanda yake da burin taimakon al'umar wan nan yanki namu.
Muna kira ga 'yan kasuwa da masu halin da suke wan nan yanki da sutai maka wajan magan ce wan nan matsala.
A karshe muna roko tare da kira ga shuwa gabannin siyasa dasu duba wan nan koke namu.
1-His Ex.Abba Kabir Yusuf (AKY)
2-DSP. Barau I.Jibrin Maliya (Senator Kano North)
3-Engr.Hamisu Ibrahim chidari (member house of Representatives DBT/MKK)
4-Muhammad Ahmad Tomas(Member makoda l.g)