13/01/2024
ZUWA GA GWAMNA ABBA GIDA-GIDA
An gama Shari'a, yanzu za a shiga mulki. Tunda dama tana hannun gwamna Abba Kabir Yusuf a ganina cikin muhimman abubuwan da zai maida hankali akansu da s**a shafi mulkin jihar Kano, ga guda tara.
Na farko, ya guji ramuwar gayya da daukar fansa da yanke hukunci da gaggawa. Mulki baya bukatar zafin kai da caji. Yana bukatar nutsuwa da hangen nesa da kallo mai zurfi.
Abu na BIYU, yana da kyau matukar gaske, ya dawo da wasu kwamishinoni da advisers da ya sallama musamman saboda matsayar da s**a dauka akan Sharia. Amma ya ja kunnuwansu su canza salonsu. Kotu uwar kowa ce, duk mai korafi ya tanadi hujja, amma banda hayaniya da tunzuri.
Na uku wadansu nade-nade da ya yi barkatai, basu dace ba, babu muhallinsu. Lallai a canza musu fasali, ina nufin a yi garanbawul, a shigar da wasu, a sallami wasu, amma a canza musu inda zasu makale.
Na hudu, ya kamata mai girma gwamna ya sani ba duka zai gama warware matsalar Kano ba, don haka, ya dauki matsaloli masu tasiri da amfani da zasu yi karko, wadanda za a yi son barka. Kada a dauko aiki don siyasa, da burgewa. Haka ko an yi alkawari, idan bukata ta nuna babu dama, a koma a yi bayanai, a yi rarrashi a bada hakuri, sannan a yi abin da ya dace. Yanzu don Allah menene amfanin yin gadar kasa a Kofar Dan Agundi ko Tal'udu ko yin fentin gadar sama ta Kofar Nassarawa, alhali babu abin da aka shirya wa 'yan kasuwa da manoma KO a birni KO a karkara?
Na biyar, a ajiye maganar cire mai martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, amma ba laifi a yi wa sabbin masarautun Bichi da Karaye da Rano da Gaya da fasali daidai da tarihi.
Na shida duk wani mai hakki a mayar masa da kayansa, wanda ke bin bashi a samar da dabarun biyansa. Ma'ana ina nufin dan fansho da dan kwangila da ma'aikata da wadanda kudadensu s**a makale a gwamnati ko kuma wadanda sun cancanci wata dama da doka ta basu, kamar Promotion.
Na bakwai a dakatar da duk wata maganar RUSAU. Amma duk inda aka ci fili da son zuciya, a yi aikin hankali a maida shi yadda yake kuma a inganta shi, KO a yi abin da ya fi shi dacewa don jama'a, Inda kuma babu wata illa a yi kwaskwarima a kyale jama'a su amfana, amfanin mulkin siyasa kenan. A sakata kuma a wala.
Na takwas, Madugu ya maida hankalinsa ga Najeriya baki daya, ya bar wa mai girma gwamna Abba K Yusuf Kano, shi kuma Abba ya nemi sauran Kanawa da danginsu a ko ina SU hada karfi da karfe SU taimaki Kano.
Na tara yanzu gwamna Abba Kabir Yusuf shi ne uban kowa a Kano, Amma ya sani Kano garin Musulunci ne, garin kasuwanci ne, garin tarihi da al'ada da sarauta da ilimi da malunta da dattijanka ne kuma Kanon Dabo garin siyasa ne. Ta hada komai, to a tafi da kowa, kowa da ranarsa.
Sunana MUFTAHU ADAM AHMAD