12/12/2025
Assalamu Alaikum
🌳🌹🎄🪷🌴🌷🍀❤️💚
A ranar 20 ga watan Jimada sani hijiriya duniya ta kuma samin wani haske
da ya haskakata na samun
Alkhairi babba.
Ina nufin a wannan wata ne aka haifi sayyida Fatima (A.S.)
'Ya ga shugaban halitta(S.A.W.W.) Annabin Rahma Muhammad Sallallahu Alaihi Wa'alihi wa sallam.
KO KA SAN WACECE
FATIMA (S.A.)
Daga bakin da bai taba qarya ba baban Fatima yace;
Fatima tsokace daga gare ni.
Fatima Allah yana yadda da yaddar ta yana fushi da fushin ta.
Fatima shugabar matan Aljanna.
Fatima mahaifiyar shuwagabannin samarin Aljanna.
Fatima matar Zakin Allah dan uwan shugaban halitta.
Fatima 'ya ga sayyida khadijatul kubra matar Annabin Rahma ta farko wacce Annabi yake cewa Allah bai bani mata ba kamar khadija kuma ba zai bani kamar ta ba.
Fatima Batul Azzahra Maradhiya Ma'asuma Zakiya Saddiqa Ummu Abiha Kausar sunayen ta suna yawa salamullahi alaiha.
💚 🌹💜🌳❤️🍀🪷🎄🙏 🙏 🙏💌👸🍏🍓✈️
Yau rana ce ta farin ciki da murna domin taya masoyin Allah murna na kyautar da Allah yayi masa ya bashi Fatima (S.A.) lokacin da Allah cikin ikon sa ya karbi 'ya'yan Annabin Rahma suna qanana sai kafiran maka s**a riqa yi masa gori cewa bashi da wanda zai gaje shi har ma suna cewa mai yankakkan baya.
Sai Allah mabuwayi da daukaka ya sau karmar da
INNA A'ADAINAKAL KAUSAR.
Karanta har qarshen sura.
Allah yace mu mun baka KAUSAR wato sayyida Fatima salamullahi alaiha
Kuma aka sanya wani kogi a gidan Aljanna Kausar ba mai shansa sai masoyin sayyida Fatima salamullahi alaiha.
Ya Allah muna son Fatima da Babanta da Mijinta da 'ya'yanta.
Ya Allah bama tare da makiyanta da makiyan Babanta da da makiyan mijin da makiyan 'ya'yan ta da duk wanda ya cutar da su har izuwa ranar qiyama.
🌳🌹🌴🌷🎄🪷🍀💚🍓💜🍏❤️✈️