Albarka Feed Mill Nig

Albarka Feed Mill Nig For Quality and Professional Services on Poultry Feeds, Fish Feed, Ruminant Feeds

17/08/2025

Big shout-out to my newest top fans! Sani Abdulwahab

20/07/2025

Big shout out to my new rising fans! Shamsu Mustapha Akilu

20/07/2025

I'm on the weekly engagement list for Albarka Poultry Services.

09/07/2025
*Ko kun san tsarin abincin kaza mai kwai?*✔️ Chick Ration:Kaza tana fara cin chick ration daga rana ta farko (Day 1) har...
06/07/2025

*Ko kun san tsarin abincin kaza mai kwai?*

✔️ Chick Ration:
Kaza tana fara cin chick ration daga rana ta farko (Day 1) har zuwa sati na 8. Wannan abinci yana taimakawa wajen girma da gina jiki a farkon rayuwarta.

✔️ Grower Ration:
Daga sati na 9 zuwa lokacin da kaza ta fara kwai, ana ba da grower ration. Wannan nau’in abinci yana karfafa jiki da bunkasa tsarin haihuwa.

✔️ Layer Ration:
Ana fara ba kaza layer ration daga lokacin da ta fara kwai (5-10% production), wanda yawanci ke faruwa daga sati na 18, idan an ba ta kulawa mai kyau da abinci mai gina jiki.

🔍 Lura:
Kaza zata fara kwai ne idan:

Nauyinta ya kai matsayin da ake bukata.

Kwayoyin haihuwarta sun girma yadda ya kamata.

Ta ci abinci mai inganci kamar Albarka Feed.

Ingantaccen kiwo da ciyar da kaji da Abincin Albarka Feed yana taimakawa wajen samun kazar da zata fara kwai da wuri kuma tana dabbaka kwai mai yawa.

Dr. Abdulaziz Musa Kwalli
07031856257
Veterinary Consultant
Albarka POULTRY Services

02/07/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Abdul Bello Ayema, Usman Mustapha, Mannira Badamasi, Abubakar Yahya Hassan, Baffa Sulaiman, Auwal Abubakar Auwal, Abdulganiiyu Umar Farouq

*ALBARKA POULTRY SERVICES*🐥 YADDA AKE HADA CONCENTRATE NA ABINCIN KAJI📝 Fahimtar “30%” da “40%” Concentrate a Kiwo*Menen...
01/07/2025

*ALBARKA POULTRY SERVICES*

🐥 YADDA AKE HADA CONCENTRATE NA ABINCIN KAJI

📝 Fahimtar “30%” da “40%” Concentrate a Kiwo

*Menene “Concentrate*”?
Concentrate wani nau’in abinci ne da aka rigada aka cika da:

1. Protein sources (soybean meal, groundnut cake, fish meal e.t.c)
2. Premix (bitamin da ma’adanai)
3. Methionine & Lysine
4. Salt
5. Limestone & Dicalcium phosphate

> Ba ya ƙunsar masara da wheat offal sosai, shi yasa sai mai kiwo ya ƙara su don Samar da cikakken abinci.

Me ake nufi da "Concentrate 30%"?

Idan ana amfani da 30% concentrate, yana nufin:

Za ka yi amfani da 30% na concentrate

Kuma 70% na kayan energy sources

🧪 Misalin cakuda (100kg complete feed):

30 kg Concentrate
45 kg Masara
25 kg Wheat offal
= 100 kg Complete Feed

Yaya ake hada "40% Concentrate"?
40 kg Concentrate
60 kg na masara (energy sources)
= 100 kg cikakken abinci

Abin Lura:

1. Kada a haɗa da ruwa kafin a cakuda

2. A tabbatar da ingancin kayan haɗawa (masara, wheat offal)

3. A duba umarnin masana'anta ko shawarar likitan dabbobi domin Kada a gaza cika nutritional requirements na kaji

Prepared by:
Dr. Abdulaziz Musa Kwalli
07031856257
CEO & Founder – Vetsline Konsult
Veterinary Consultant – Albarka Poultry Services

Address

NO 173 Sabon Titi Sani Mainagge
Kano
700234

Opening Hours

Monday 08:15 - 17:30
Tuesday 08:15 - 17:30
Wednesday 08:15 - 17:30
Thursday 08:15 - 17:30
Friday 08:15 - 17:30
Saturday 08:15 - 17:30

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Albarka Feed Mill Nig posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share