18/05/2026
KWANAKI MAFI SOYUWA GA ALLAH SUN ISO — KAR KA BARI SU WUCE KA.
Wata ‘yar uwa ta tambaya cewa:
Assalamu Alaikum…
Ina son yin azumin goman farko na Zulhijjah
Amma Allah bai bani ikon farawa yau ba.
Zan iya farawa gobe?
Kuma ina da bashin azumin haihuwa…
zan iya yin wannan azumin nafila kafin na biya bashin?
Wallahi wannan tambaya tana da muhimmanci sosai…
musamman yanzu da muka shiga kwanaki mafi falala a duniya.
Dan uwa…
Kwanaki goma na farkon Zulhijjah
Ba kwanaki bane irin sauran kwanaki.
Annabi ﷺ yace:
Babu wasu kwanaki da aiki na kwarai ya fi soyuwa ga Allah
Kamar wadannan kwanaki goma.
Wato:
sallah…
azumi…
sadaka…
zikiri…
karatun Alkur’ani…
duk sun fi falala sosai a wadannan kwanaki.
🤲 Game da tambayarki:
Eh… idan baki samu damar fara azumi daga ranar farko ba,
zaki iya farawa daga gobe.
Kar ki ce:
Tunda ban fara daga farko ba shikenan na bari.
A’a…
duk ranar da kika yi cikin wadannan kwanaki
Kina cikin babban alheri In Shaa Allah.
Ko mutum yayi rana daya…
ko biyu…
ko tara…
duk akwai lada mai girma a ciki.
🤲 Amma maganar bashin azumi fa?
Malamai sun yi bayani cewa:
Idan mutum yana da bashin Ramadan ko na haihuwa,
yana da kyau ya fara biyan bashin.
Saboda bashi wajibine.
Azumin Zulhijjah kuma nafila ne.
Amma idan lokaci yana da yawa kafin Ramadan mai zuwa,
kuma mutum yana son hada niyyar biyan bashi a cikin wadannan kwanaki,
akwai fata zai samu ladan biyun In Shaa Allah.
Misali: ki yi niyyar biyan bashinki a cikin kwanakin Zulhijjah.
Da haka: kin biya wajibi
kuma kina fatan samun falalar kwanakin goma.
Allah Mai rahama ne…
kuma baya tozarta aikin bawansa.
Dan uwa…
Kar mu bari wadannan kwanaki su wuce mana cikin sakaci.
Wasu suna ta neman duniya…
alhali akwai kwanaki da aiki kadan yake zama babban rabo a wajen Allah.
Ka yawaita:
🤲 istigfari
🤲 salati ga Annabi ﷺ
🤲 karatun Alkur’ani
🤲 sadaka
🤲 taimakon mutane
🤲 da yawan ambaton Allah.
Musamman ranar Arafah…
rana ce mai girman gaske.
Azuminta yana kankare zunuban shekara biyu In Shaa Allah.
🤲 Ya Allah…
Ka bamu ikon anfani da wadannan kwanaki yadda ya dace.
🤲 Ka gafarta mana zunubanmu.
🤲 Ka karbi ibadunmu da addu’o’inmu.
🤲 Ka sanya mu cikin bayinKa da zaka ‘yanta daga wuta a wadannan kwanaki masu albarka.
Ameen Ya Rabbal Alameen.
Addinu Annasiha