Yusuf sani

Yusuf sani Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Yusuf sani, Business service, GWALE LGA, Kano.

14/05/2026

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai. Sa’o’i kadan da s**a gabata, Shugaban Majalisar Wakilai ta 10, Mai Girma Tajudeen Abbas (GCON), ya karanta wasikar murabus dina daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma komawa ta jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a hukumance yayin zaman majalisa.

A yanzu ni mamba ne a jam’iyyar ADC, kuma zan nemi sake tsayawa takara domin ci gaba da wakiltar mutanen kirki na mazabar Kaduna ta Arewa a karkashin wannan jam’iyya. Ina tare a wannan sabon shafi da babban dattijonmu, Hon. Engr. Suleiman Richifa, mai wakiltar Soba, da kuma dan uwana, Hon. Umar Ajilo, mai wakiltar Makarfi/Kudan, wadanda duka s**a sauya sheka daga tsoffin jam’iyyunsu zuwa jam’iyyar ADC. Tare, muna gina gida domin hidima ga mutane da ci gaba.

Wannan shawara ba abu ne mai sauki ba. A matsayina na kishin dan Mallam Nasir El-Rufai, ina yin aiki ne da gaba ga-adi, kwarin gwiwa, da kuma tabbacin cewa mutanenmu sun cancanci mafi kyawun wakilci. Zuwa ga mutanen Kaduna ta Arewa: aikinmu yana nan yana ci gaba, kuma ba zai tsaya ba. Ba za mu taba yin kasa a gwiwa ba wajen samar da wakilci na gari. Akwai sauran ayyuka da dama a gaba.

Da yardar Allah, nan ba da dadewa ba zan sanar da kwamitin wucin gadi na shirin inganta cibiyoyin kiwon lafiya (Primary Health Care) da na kaddamar a makon jiya. Za mu samar wa cibiyoyin kiwon lafiyar kayayyakin magani, inda za mu fara da allurai (syringes) guda 1,000 ga kowace cibiya da sauran muhimman kayayyaki. Kashi na farko zai fara ne da cibiyoyi guda biyu: mazabar Unguwar Sarki da mazabar Badarawa/Malali.

Allah Madaukakin Sarki Ya ci gaba da yi mana jagora yayin da muke yi wa jama’a hidima. Kuma Allah Ya albarkaci Najeriya da shugabanni nagari.

Sa hannu/Signed:
Hon. Mohammed Bello El-Rufai
Dan Majalisa, Mazabar Kaduna ta Arewa
Shugaban Kwamitin Ka'idojin Bankuna.
Mayu 7, 2026.

14/05/2026

Allah ya kyauta

゚viralシ

07/05/2026
Allah ya jaddada rahama
07/05/2026

Allah ya jaddada rahama

Address

GWALE LGA
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yusuf sani posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share