Abdulmajeed Almustapha Kwamanda

Abdulmajeed Almustapha Kwamanda Chairman Arewa Media Group Organization Of Nigeria
(1)

31/08/2026

KU SAURARA 👂

Tsaraba daga ƙasar Saudi Arabia zuwa ga ƴan Najeriya masu son ganin gobensu ta yi kyau. 🇸🇦🇳🇬

Gobe mai kyau tana farawa ne da ilimi, jajircewa, aiki tuƙuru da kyakkyawar niyya. Mu matasa mu tashi tsaye, mu nemi ilimi da sana’o’in da za su amfani rayuwarmu da ƙasarmu.

Gobe tamu ce, idan muka shirya mata tun yau.

Irin ƙaunar da talakawa suke nuna min, ba zan taɓa cin amanar su ba, wallahi.Idan da kuɗi nake siyasa ko kuma don kaina ...
31/08/2026

Irin ƙaunar da talakawa suke nuna min, ba zan taɓa cin amanar su ba, wallahi.

Idan da kuɗi nake siyasa ko kuma don kaina kaɗai nake yi, da ban taɓa yaƙar jam’iyyar mu ta APC ba. Amma abinda nake ganin zan iya biyawa talakawa a madadin irin ƙaunar da suke nuna min shi ne tsayawa a inda suke, kare muradunsu da kuma faɗin gaskiya a lokacin da ya dace.

Talakawa sun ba ni amana, kuma ba zan sayar da wannan amanar saboda wata kujera ko wata fa'ida ta kaina ba.

Mutum zai iya rasa matsayi, amma bai kamata ya rasa mutuncinsa da amana ba.

31/08/2026

Roƙon mu ga Comrd Aminu Abdussalam Gwarzo a 2027 .

31/08/2026

Ashe an harbo su, sun shigo kenan. Ba fake alert bane. 😅

Shine baku bani labari ba?

MAKARANTAR ALIKO DANGOTE: WATA DAMA DA GWAMNATIN KANO TA YI WATSI DA ITAGwamnatin Jihar Kano ce ta samar da Aliko Dangot...
31/08/2026

MAKARANTAR ALIKO DANGOTE: WATA DAMA DA GWAMNATIN KANO TA YI WATSI DA ITA

Gwamnatin Jihar Kano ce ta samar da Aliko Dangote Ultra-Modern Skills Acquisition Centre, a zamanin mulkin tsohon Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, Kwanar Gurjiya.

An kashe biliyoyin kuɗi wajen gina wannan makaranta tare da samar da kayan aikin koyo da koyarwa a Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu. Amma abin takaici, saboda rashin kishin al’umma da matasan Jihar Kano, gwamnatin yanzu ta kasa gudanar da ita yadda ya kamata.

Da gwamnati ta damu da makomar ƴaƴan talakawa, wannan makaranta kaɗai za ta iya taimakawa wajen horar da matasa sama da 10,000, ta hanyar koya musu sana’o’i daban-daban tare da ba su jarin fara sana’ar da s**a koya, domin su dogara da kansu.

Saboda wannan gazawa, sai aka bai wa Dangote Foundation makarantar bisa yarjejeniyar shekaru 20. Alhali makarantar ta shafe sama da shekaru biyu a rufe ba tare da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata ba. Kayan aikin da aka zuba a cikinta sun yi ƙura; sai mutum ya je ya ga irin kayayyakin da aka tanada sannan zai fahimci irin aikin da gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta yi. Ko ba ka son Ganduje, dole ne ka yaba masa a kan wannan aiki.

Abin takaici ne matuƙa yadda wata babbar makaranta mai irin wannan muhimmanci, wadda jihohin maƙwabta za su yi fatan samun irinta, za a bar ta tsawon lokaci har ta fara fuskantar lalacewa saboda rashin kulawa.

Insha Allah, idan Comrd. Aminu Abdussalam Gwarzo ya zo, za mu tabbatar mun ba shi shawarar a dawo da wannan makaranta ƙarƙashin kulawar Gwamnatin Jihar Kano, domin ta ci gaba da amfanar ƴaƴan talakawa. Domin na san shi da kishi da son ganin ɗan talaka ya amfana.

A cikin yarjejeniyar da za mu mara masa baya a kanta, wajibi ne ya fifita buƙatar talakawa a kan tasa, kamar yadda muka sanya buƙatar talakawa a gaba kafin tamu.

Insha Allah, muna da kyakkyawan zato cewa za mu ga sabuwar Kano ƙarƙashin jagorancin Comrd. Aminu Abdussalam Gwarzo a 2027, Kano da za ta bambanta da yadda take a yau — domin abin da muke gani a yau abin takaici ne.

Zaɓen 2027 zaɓe ne na cancanta, ba maganar jam’iyya kawai ba. Duk inda ɗan takara na ƙwarai yake, ku zaɓe shi.

Halin da Aliko Dangote Ultra-Modern Skills Acquisition Centre da ke Kano yake ciki.
31/08/2026

Halin da Aliko Dangote Ultra-Modern Skills Acquisition Centre da ke Kano yake ciki.

31/08/2026

Saƙon Yayana Sharu Usman Baban lungu.

31/08/2026

Manufar Professor Isa Ali Pantami a bayyane take Gombe ce a ransa.

30/08/2026

HE. Atiku Abubakar 2027.

Address

Kano

Telephone

+2347042745089

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abdulmajeed Almustapha Kwamanda posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share