25/07/2026
BABU MARAYA SAI RAGO.
Allah nagode maka da ka rayamin zuciya na, ka tsaftace ta sannan ka alkintamini ita.
Allah nagode maka da ka dauke mahaifina, kadauke mahaifiya na, kadauke yayata, sannnan kadauke wasu shakikaina, kasanya mini dangana sannan kuma ka hakurkuntar da zuciya na.
Na sha wahala sosai, na fuskanci jarabawa iri iri amma Allah baka sa na kauce daga hanyarka ba, nasamu dama dazanyi rayuwa irin wacce naga dama amma nazabi in zama AHMAD dina tareda taimakon Allah. Bayan duk wasu kalubale na rayuwa da juriya danayi bantaba mantawa da Allah ba…cikin ikonsa da yardarsa yau gani a tsaye kam da kafafu na, da kasuwancina, da jari na, iyalina sun samu rayuwa irin wacce nake mafarki, yan uwana sun samu saukin rayuwa, ga gida Allah yabani da duk wani rufin asirin da bawa ke nema duk Allah yayi mini, abubuwa sunata tafiya sannan anata samun nasara da ci gaba arayuwa Allah Alhamdulillahi. Allah duk wani mai kokarin neman na halalinsa Allah kada kabarshi da iyawarsa da wayonsa kataimakesa sannan kasaka masa albarka. Alhamdulillahi ya rabbalakal hamdu washshukhur.