13/07/2026
NYSC Ta Karrama Sanata Barau Da Lambar Yabo Ta Pillar of the 10th Senate Award
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, CFR, ya sake samun wata babbar karramawa, bayan da mambobin Hukumar Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) na shekarar hidima ta 2025/2026 da ke aiki a Majalisar Dokokin Ƙasa s**a ba shi lambar yabo ta Pillar of the 10th Senate Award.
Shugaban tawagar NYSC, Abubakar Abdullahi, ya bayyana cewa an ba Sanata Barau wannan lambar yabo ne saboda irin nagartacciyar hidima, shugabanci na gari da kuma gudunmawar da yake ci gaba da bayarwa wajen bunƙasa rayuwar matasan Najeriya.
Ya ce bayan sun shafe tsawon lokaci suna bibiyar ayyukansa a Majalisar Dokoki, sun tabbatar da cewa Sanata Barau ya kasance ɗaya daga cikin jagororin da s**a fifita muradun matasa ta hanyar shirye-shiryen ilimi, bayar da guraben karatu, ƙarfafa sana'o'i, samar da ayyukan yi da bunƙasa harkokin wasanni.
A nasa jawabin, Sanata Barau ya bayyana cewa wannan karramawa ta zo ne a matsayin ƙarin ƙwarin gwiwa, yana mai alƙawarin cewa zai ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar matasan Najeriya.
Ya kuma jaddada cewa ci gaban ƙasa ba zai tabbata ba sai an ba matasa fifiko, yana mai cewa zuba jari a matasa shi ne ginshiƙin gina Najeriya mai ɗorewa da wadata.
Sanata Barau ya gode wa mambobin NYSC bisa wannan karramawa, tare da bayyana cewa zai ci gaba da sadaukar da kansa wajen yi wa ƙasa da al'ummarta hidima.