30/05/2023
Assalamualaikum
Jiya Nayi magana akan maza masu taɓa Mata kowacce kmr tana jira, ji kake ana Juu faɗa musu dai 😒
Ja'ira yau kanki na dawo Algunguma 😒🤌 idn akazo case irin wannan gaskiya bana ganin laifin Namijin sosai, Saboda duk abinda zai faru acikin barna irin wannan laifin mace yafi yawa.
1. Na farko wasu matan su suke Fara taɓa mazan ma dakansu ko Kuma su bada fuskar da za'a taɓa su idn namiji baiga fuska ba Wlhy duk girmansa ko yawan shekarunsa babu yadda ma za'ayi har ya Fara kokarin taɓa ki,,,karyansa ne Wlhy
2. Na biyu Yana da alaqa da yanayin shigar da k**eyi
3. Na uku Yana da alaqa da yanayin da k**e Masa magana as in idn kuna ganin Juna Kuma kina Yi Masa magana cikin shagwaba wlhy ko shi ne allon da ake liqawa a masallaci wataran sai kin saka shi ya kauce hanya,,, so ba'a Hana ki Masa shagwaba ba Amma kisan wace iri zakiyi Kuma a Ina ? E get why🤷♀️
4. Na Huɗu Yana da alaqa da yawan son da k**e Masa Wanda yake Hana ku faɗawa juna gaskiyar cewa wannan abinda muke fa bashida kyau ya Sabawa koyarwar musulunci..... So zaka ga yawancin Mata idn muna masifar son saurayi mukan Bari shaidan yayi galaba akanmu muga kmr soyayya ce.
5. Na Biyar wasu sun dauki hakan wayewa ce,,, idn ma namijin baya kokarin taɓa su gani suke Yi baya sonsu akwai wacce Yake so Kuma yake taɓawa kaico 🥹 so gaskiya mostly nafi ɗora blame akan Mata idn akazo magana irin wannan,,, sbd wlhy namiji Bai Isa ya Miki Dole ba matuqar ba mijinki bane,,, ko me zai faru sai idn kece kika yarda.....
Ban cire kaina ba Kuma ban cire kowa ba...., domin kowani bawa akwai laifin daya boye a ransa kasancewar mu Ya'yam Adam Dole akwai ajizanci,,,,Ina Mana nasihar muji tsoron Allah,,, acikin maza idn kasan halinka ne taɓa yaran mutane kaji tsoran Allah kadaina Dan uwa😢 kema idn kin San kina sakar Masa jiki Yana shafaki kiji tsoran Allah kidaina....Mudaina barin so Yana rufe Mana idanuwa muna aikata sabon Allah🙏🏻
Babu amfanin soyayyar da baza'a tunatar da juna faɗin Allah ba 💔 Mu tsaftace so