15/02/2026
Innalillahi wa inna ilaihi raji un!
Yan uwanmu 'yan kasuwar singa, muna miko sakon jajenmu gareku, da addu ar Allah ya mayar muku da ninkin abinda kuka rasa.
Tunatarwa :
Allah madaukakin sarki acikin Alqur'ani mai girma yana cewa ;"kuma zamu jarrabeku da wani abu(ibtila'i) na daga tsoro, da yunwa, da kuma tawaya daga dukiyoyi da rayuwa, harma da 'ya'yan itatuwa(marmari dana gona) a karshe Allah yace ayiwa masu hakuri albishir(bishara).
Saboda haka, ina kira da yan uwana 'yan kasuwar singa, da ku rungumi wannan jarabawa da ubangiji dama yayi alkawarin sai yayi shi, kuma kuyi hakuri kamar yadda yayi alkawarin in kukayi akwai wani tanadi da ya muku wanda baku sanshi ba.
A karshe ina muku fatan alkhairi tare da addu ar Allah yamayar muku da alkhairi yakuma kara muku karfin imani (Amin).
Ma'assalam.
Aminu Sale Yahuza
(Barr. Hujja)
It's permitted to copy in order to reach many!!!