29/03/2026
Uwargidan Shugaban Ζasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana matuΖar alfaharinta da Ζauna ga mijinta, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yayin da yake bikin cika shekaru 74 da haihuwa.
A yau Lahadi ne Shugaba Tinubu ya cika shekaru 74 a duniya, inda βyan Najeriya daga sassa daban-daban s**a aike masa da saΖonnin fatan alheri da adduβoβi.
A cikin wata sanarwa da ta fitar kuma ta sanya wa hannu da kanta, Uwargidan Shugaban Ζasar ta bayyana cewa tana alfahari da irin jagorancin da Shugaban ke bayarwa.
Ta kuma roΖi Allah da ya Ζara masa lafiya, Ζarfi da natsuwa, tare da yi masa fatan samun nasara wajen jagorantar Ζasar nan zuwa ga ci gaba mai Ιorewa.