05/01/2025
HANYAR ZAMA JAGORA // 05
HANNU ƊAYA BA YA ƊAUKAR JINKA
Da za a nuna maka yadda ake haɗa jinka a ƙasa kafin a cicciɓe ta zuwa inda aka tanadar mata za ka fi fahimtar maganar, amma a zamanance in aka kwatanta maka da yadda 'yan ƙwallo ke yin miƙa-miƙa da ita har su kai ga jefa ta a raga, za ka fahimci mutum guda a tsakiyar matsaloli da dama ba zai iya kaiwa gaci ba sai tare da sa hannun mataimaka waɗanda kowa a cikinsu manufarsa kenan. Shi ya sa ka ga masu manyan kamfanoni suna sayar da hannun jari, kuma suna boɗe wasu ƙofofi da wasu za su shigo a yi sana'ar tare.
Masu manyan makarantu kan yi ƙoƙarin samar da rassa a wasu wurare da suke tunanin za su ɗalibai acan.
Abinda ke sanya masu kamfanoni su haɗa hannu da wasu abokan sana'arsu duka dai wani ƙoƙari ne na haɓɓaka wuri, amma ba ya nufin jagorancin mutum ya saraya kenan, ƙarfi ne ma ya ƙara. Tunda in mutum yana sana'ar kekuna ya haɗa hannu da mai sana'ar babura, tunaninsa zai wuce na tsohuwar sana'ar da yake yi. Ko kuma yawan abinda yake fitarwa ya ƙaru, ko ya fara hurɗa da manyan mutanen da a baya bai taɓa tsammanin haka ba. Da ya tsuke kansa a wuri guda da wahala ya sami wannan matsayin.
Haɗa hannu da wasu kan ba mutum damar da zai koma baya ya huta, kuma jarinsa ya yi ta haɓaka. Ba yadda za a yi ka rasa wannan jagorancin sai in ka miƙa wuya ga wasu yadda jarinka ya gaza nasu, ko ƙarfinka a wurin bai kai nasu ba. Wannan muka gane cewar akwai buƙatar jagora ya ɗara sauran da s**a haɗa hannu da shi ta fiskoki da dama, ciki har da kasancewa a mahallin kowani lokaci, da samun yalwataccen jari fiye da sauran, da kuma aiki kan-jiki kan-ƙarfi. Shugabanci kan sulluɓewa mutum ne a lokacin da ya gaza samun tsari mai kyau.
Ilimi, lafiya, mai da hankali da kuzari na ɗaya daga cikin abubuwan da jagora ke buƙata, in dai jagora bai isa ya sa a yi ko ya hana ba, bai da ƙarfin da zai iya jagoranci. Haka in ya zamanto bai iya kallo da idonsa, ko ya ji da kunnensa, ko ya tsara da kansa sai da a haɗa komai a ba shi, nan ma