Arewa Updates Academy

Call Website

Arewa Updates Academy This is Arewa Updates Academy 🎓

Prompt shi ne tambaya, umarni ko bayanin da dan adam yake bai wa AI domin ta fahimci abin da yake so ta yi masa. Duk lok...
27/09/2026

Prompt shi ne tambaya, umarni ko bayanin da dan adam yake bai wa AI domin ta fahimci abin da yake so ta yi masa. Duk lokacin da ka rubuta wa ChatGPT ko wani kayan aikin AI abin da kake so, wannan rubutun shi ake kira Prompt.

Misali, idan ka rubuta:

“Ka rubuta mini taƙaitaccen labari kan muhimmancin ilimi cikin harshen Hausa.”
wannan Prompt ne. AI za ta yi amfani da bayanan da ka bayar domin samar da amsar da ta dace.

Prompt na iya zama gajere k**ar:

“Fassara wannan zuwa Hausa,”
ko kuma ya zama cikakke ta hanyar bayyana abin da kake so, yadda kake son a yi shi, da irin sak**akon da kake buƙata.

Yadda ka rubuta Prompt yana da matuƙar tasiri ga amsar da AI za ta bayar. Idan umarninka bai fito fili ba, za ka iya samun amsar da ba ka so. Amma idan ka bayyana buƙatarka dalla dalla, AI za ta fi fahimtar abin da kake nema.

A taƙaice, Prompt hanya ce ta sadarwa tsakanin dan adam da AI. Kai ne kake gaya wa AI abin da kake so ta yi, ita kuma ta samar maka da sak**ako bisa umarnin da ka ba ta.

©Arewa Updates Academy

Kayan aikin ko manhajojin AI, suna da nau’uka daban-daban, kuma an ƙera kowanne domin taimakawa wajen gudanar da wasu ay...
26/09/2026

Kayan aikin ko manhajojin AI, suna da nau’uka daban-daban, kuma an ƙera kowanne domin taimakawa wajen gudanar da wasu ayyuka. Wasu sun fi ƙwarewa a rubutu, wasu a hoto, bidiyo, sauti, bincike ko nazarin bayanai.

Akwai AI na rubutu, wanda ke taimakawa wajen rubuta bayani, amsa tambayoyi, taƙaita rubutu da tsara ra’ayoyi. Misalansa sun haɗa da ChatGPT, Claude da Gemini.

Akwai kuma AI don aka tsara don ya ƙirƙiri hotuna da bidiyo, waɗanda ake amfani da su wajen ƙirƙira ko gyara hotuna da bidiyo. Haka kuma, akwai AI na sauti, wanda zai iya taimakawa wajen samar da murya, sauya murya zuwa rubutu ko rubutu zuwa murya.

Wasu kayan aikin AI kuma an ƙera su domin bincike da nazarin bayanai, yayin da wasu ke taimakawa wajen fassara harsuna, rubuta manhajojin kwamfuta da gudanar da wasu ayyuka na musamman.

Saboda haka, ba duk kayan manhajar AI ce ke yin aiki iri ɗaya ba. Abu mafi muhimmanci shi ne ka fara sanin aikin da kake son yi, sannan ka zaɓi manhaja wato (Application) aikin AI da ya fi dacewa da wannan aikin.

Ga wasu daga ciki da irin ayyukan da suke yi:

1. ChatGPT → Rubuta Prompt, wasika, rahoto, taƙaita rubutu, bincike da ƙirƙirar hoto.
2. Claude → Rubutu, nazarin dogayen takardu, taƙaitawa da taimakawa wajen bincike.
3. Gemini → Rubutu, bincike, nazarin hoto da takardu, da taimakawa wajen ƙirƙirar bayanai.
4. Perplexity → Binciken bayanai a internet tare da nuna tushe.
5. Canva AI → Ƙirƙirar flyer, poster, presentation, hoto da sauran graphics.
6. Midjourney → Ƙirƙirar hotuna daga Prompt.
7. Adobe Firefly → Ƙirƙira da gyaran hotuna ta amfani da AI.
8. ElevenLabs → Ƙirƙirar murya, voiceover da sauya rubutu zuwa murya.
9. Runway → Ƙirƙira da gyaran bidiyo ta amfani da AI.
10. DeepL → Fassara rubutu daga wani harshe zuwa wani.

©Arewa Updates Academy

Fasahar AI na iya taimaka wa dan adam wajen gudanar da ayyuka da dama cikin sauri da sauƙi, musamman ayyukan da s**a sha...
25/09/2026

Fasahar AI na iya taimaka wa dan adam wajen gudanar da ayyuka da dama cikin sauri da sauƙi, musamman ayyukan da s**a shafi rubutu, bayanai, hotuna, sauti da bidiyo.

AI na iya rubuta bayani, taƙaita dogon rubutu, fassara harsuna, gyara nahawu, nazarin bayanai da amsa tambayoyi. Haka kuma, tana iya taimakawa wajen ƙirƙirar hotuna, sauti da bidiyo.

Misali, ɗan jarida zai iya amfani da AI wajen taƙaita wata doguwar sanarwa, tsara tambayoyin hira, rubuta labaran kotu, fahimtar wasu bayanai ko gyara rubutunsa.

Ɗalibi kuma zai iya amfani da ita wajen samun ƙarin bayani kan darasin da yake karantawa ko yin aikin gida idan an ba shi.

Sai dai abin da AI za ta iya yi ya danganta da irin kayan aikin AI da ake amfani da shi, wasu an ƙera su ne domin rubutu, wasu don samar da hotuna, wasu don bidiyo, wasu kuma domin sauti ko nazarin bayanai.

Duk da waɗannan ayyuka, AI taimako kawai ta ke yi, ba madadin tunanin ɗan Adam ba.

Saboda haka, ya k**ata mutum ya duba sak**akon da ta bayar kuma ya tabbatar da sahihancinsa kafin amfani da shi.

©Arewa Updates Academy

Fasahar AI tana aiki ne ta hanyar karɓar umarni ko bayanai wato (PROMPT) daga mutum, ta sarrafa su, sannan ta samar da s...
24/09/2026

Fasahar AI tana aiki ne ta hanyar karɓar umarni ko bayanai wato (PROMPT) daga mutum, ta sarrafa su, sannan ta samar da sak**ako bisa abin da aka ba ta da kuma bayanan da aka horas da ita a kansu.

Misali, idan ka rubuta wa AI cewa “Ka taƙaita min wannan labari”, wannan shi ne umarnin da ka ba ta.

AI za ta nazarci rubutun, ta fahimci abin da ake nema, sannan ta samar da taƙaitaccen bayani.

A sauƙaƙe, za mu iya fahimtar yadda AI take aiki ta matakai 3 k**ar haka:

Input → Processing → Output.

Input shi ne abin da ka ba AI, Processing shi ne yadda take sarrafa bayanin, Output kuma shi ne amsar ko sak**akon da take ba ka.

Sai dai, AI tana aiki ne bisa bayanan da aka horas da ita da su, tsarin da aka gina ta da shi, da bayanan da mai amfani ya ba ta.

Wannan yana nufin za ta iya yin kuskure ko bayar da bayanin da ba daidai ba.

Saboda haka, kyakkyawan umarni yana taimakawa wajen samun kyakkyawan sak**ako, amma dole ne mutum ya duba ya kuma tabbatar da amsar AI kafin amfani da ita.

©Arewa Updates Academy

AI, wato (Artificial Intelligence), fasaha ce da ke bai wa kwamfuta damar yadda za ta iya fahimtar bayanai da aiwatar da...
23/09/2026

AI, wato (Artificial Intelligence), fasaha ce da ke bai wa kwamfuta damar yadda za ta iya fahimtar bayanai da aiwatar da wasu ayyuka wadanda a lokutan baya sai mutum ne kadai yake iya yin su.

Human Intelligence wato (HI), ita ce basirar ɗan Adam ta asali. Ita ce damar da mutum yake da ita ta tunani, fahimta, koyo daga gogewa, warware matsaloli da yanke hukunci bisa abin da ya sani da yanayin da yake ciki.

Artificial Intelligence (AI) kuwa, basira ce da ɗan Adam ya ƙirƙira ta hanyar amfani da na’ura ko kwamfuta domin ta iya gudanar da wasu ayyuka masu k**a da na basirar ɗan Adam, k**ar fahimtar umarni, nazarin bayanai, rubutu, fassara da amsa tambayoyi. A taƙaice, HI basirar ɗan Adam ce, AI kuma fasaha ce da ɗan Adam ya ƙirƙira.

Misali, AI na iya amsa tambayoyi, rubuta ko taƙaita bayani, fassara harsuna, nazarin bayanai, gane abubuwan da ke cikin hoto, da taimakawa wajen samar da hotuna ko sauti.

ChatGPT misali ne na AI, Idan ka rubuta masa tambaya ko umarni, yana nazarin abin da ka rubuta sannan ya samar da amsa bisa bayanan da aka horar da shi da su da kuma bayanan da ka ba shi.

Amma AI ba mutum ba ne, kuma ba koyaushe yake bayar da sahihin bayani ba. Yana iya yin kuskure ko samar da bayanin da ba daidai ba.

Saboda haka, musamman a aikin jarida, wajibi ne a tabbatar da bayanan da AI ya bayar daga sahihan tushe kafin amfani da su ko wallafawa.

A taƙaice, AI fasaha ce, da ke taimaka wa dan adam wajen yin wasu ayyuka cikin sauƙi da sauri, amma har yanzu mutum ne ke da alhakin tantance sak**akon da ta bayar.

©Arewa Updates Academy

Kana ɗauko rahoton kotu amma har yanzu ba ka amfani da AI?Fasahar AI na iya sauƙaƙa wa ɗan jarida fahimtar takardun kotu...
10/09/2026

Kana ɗauko rahoton kotu amma har yanzu ba ka amfani da AI?

Fasahar AI na iya sauƙaƙa wa ɗan jarida fahimtar takardun kotu, kalmomin shari’a, tsara bayanai da gina rahoto cikin sauri.

Amma akwai babban ƙalubale. AI na iya yin kuskure, ƙirƙirar bayanin da babu shi ko sauya ma’anar hukuncin kotu.

Saboda haka, ƙwarewar amfani da AI ba ta tsaya kan tambayarsa kawai ba. Dole ɗan jarida ya san abin da zai ba AI, abin da ba zai ba shi ba, da yadda zai tabbatar da duk bayanin da AI ya samar kafin wallafawa.

A wannan darasin, Arewa Updates Academy ta kawo hanyoyin da ’yan jarida masu ɗauko rahotannin kotu za su iya amfani da AI cikin ƙwarewa da taka tsantsan.

1. Ka zaɓi batu da manufar Shirin:Kafin ka fara shirin Podcast, abu na farko shi ne ka fayyace batun da kake son shirin ...
08/09/2026

1. Ka zaɓi batu da manufar Shirin:

Kafin ka fara shirin Podcast, abu na farko shi ne ka fayyace batun da kake son shirin ya mayar da hankali a kai, da kuma manufar da kake son cimmawa.

Kada ka fara Podcast kawai saboda ka ga wasu suna yi, ka tambayi kanka irin ilimi, bayani, nishaɗi ko tattaunawar da kake son kawo wa masu sauraro, da kuma dalilin da zai sa su zaɓi sauraron shirinka.

Misali, za ka iya mayar da hankali kan kasuwanci, ilimi, fasaha, al’amuran yau da kullum, rayuwar iyali, sana’o’i, tarihi, al’adu ko hira da mutane masu ƙwarewa.

Samun tak**aiman batu zai taimaka wa Podcast ɗinka ya kasance yana da alkibla, kuma masu sauraro su fahimci irin abin da za su riƙa samu daga gare ka.

2. Ka san masu sauraron da kake son isar wa saƙo:

Kafin ka fara ɗaukar Shirin Podcast, ka tantance su waye kake son su zama masu kallo da sauraron Podcast ɗinka.

Shin matasa ne, ɗalibai, ’yan kasuwa, iyaye, mata, ma’aikata, masu sana’o’i ko sauran jama’a?

Sanin waɗanda kake son kai wa zai taimaka maka wajen tsara kusan dukkan abubuwan da s**a shafi shirin.

Ka yi la’akari da harshen da s**a fi fahimta, irin batutuwan da suke sha’awa, matsalolin da suke son samun mafita a kansu da kuma kafafen da s**a fi amfani da su.

Idan masu sauraronka galibinsu Hausawa ne, amfani da Hausa mai sauƙi da misalan da s**a shafi rayuwarsu zai iya taimaka musu wajen fahimtar abin da kake gabatarwa.

Haka kuma, ka riƙa sauraron ra’ayoyinsu domin sanin abubuwan da suke son a tattauna a shirye shirye na gaba.

3. Ka tanadi kayan aiki da wurin ɗaukar shiri:

Ba sai ka mallaki katafaren studio ko kayayyakin aiki masu tsada ba kafin ka fara Podcast.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne samun sauti mai inganci, wanda masu sauraro za su iya ji cikin sauƙi.

Za ka iya farawa da microphone mai kyau, waya ko kwamfuta da kuma manhajar da za ka yi amfani da ita wajen ɗaukar sauti da gyara shi.

Wurin da za ka yi recording yana da matuƙar muhimmanci, don haka ka nemi ɗaki mai natsuwa wanda ba bu hayaniyar motoci, mutane, fanfo ko wasu abubuwan da za su shiga cikin sautinka.

Shawara: Kafin fara cikakken shiri, ka yi gwajin microphone da sauti domin tabbatar da cewa muryarka tana fitowa yadda ya k**ata.

Idan hira za ka yi da wani, ka tabbatar ana iya jin muryar kowane ɓangare da kyau kafin a fara.

4. Ka tsara yadda zai gabatar da shirinsa:

Podcast mai kyau yana buƙatar shiri tun kafin a kafe camera ko a kunna microphone.
Ka tsara abin da za ka tattauna, yadda za ka fara shirin, muhimman abubuwan da za ka bi a jere da yadda za ka rufe shi.

Hakan ba yana nufin dole ka rubuta duk abin da za ka faɗa kalma da kalma ba, amma ya k**ata ka kasance da tsarin da zai hana tattaunawar fita daga kan batu.

Idan za ka gayyaci baƙo, ka yi bincike a kansa da batun da za ku tattauna kafin ranar hira.

Ka tanadi tambayoyi masu buɗe damar yin bayani maimakon tambayoyin da za a iya amsawa da eh ko a’a kawai.

Ka kuma saurari baƙonka yayin tattaunawa domin amsarsa na iya haifar da wata muhimmiyar tambaya da ba ka shirya tun farko ba.

Ka guji katse masa magana ba tare da dalili ba.

5. Ka tsara yadda yaɗa shirinka:

Kammala recording ba shi ne ƙarshen aikin Podcast ba, bayan an ɗauki shirin, ya k**ata a saurare shi, a gyara kura kuran da s**a dace, a daidaita sauti sannan a shirya shi domin wallafawa.

Ka samar wa kowane shiri take mai sauƙin fahimta wanda zai bayyana abin da aka tattauna, tare da bayanin da zai taimaka wa mai sauraro ya fahimci abin da zai samu a ciki.

Ka kuma tsara inda za ka riƙa wallafa shirye shiryenka da yadda mutane za su gano su.

Za ka iya amfani da kafafen Podcast da kuma shafukan sada zumunta wajen kai shirin ga jama’a.
Za a iya cire gajerun ɓangarori masu muhimmanci daga cikinsa domin bidiyo ko sauti na tallata cikakken shirin.

Shawara: Abu mafi muhimmanci shi ne aiki ya kasance mai ɗorewa.

Ka tsara ranakun da za ka riƙa fitar da sabbin shirye shirye gwargwadon ƙarfinka, maimakon ka fara da yawa sannan ka daina.


Take the first step towards your academic journey at Khalifa Isyaku Rabiu University, Kano (KHAIRUN).For applications, k...
08/09/2026

Take the first step towards your academic journey at Khalifa Isyaku Rabiu University, Kano (KHAIRUN).

For applications, kindly visit:
https://admission.khairun.edu.ng/

For further enquiries, kindly contact the Admissions Office via:
+234 811 915 9989/ 806 958 9572
Or visit: www.khairun.edu.ng

08/09/2026

Ai video masterclasses held at Kano State Hisbah Board.

Tutored by Arewa Updates Academy's Sa'id Aminu Sa'id

06/09/2026

07/09/2026

Horarwa ga jami’an Hukumar Hisbah

Address

Kano
Kano
700231

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Updates Academy posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share