22/05/2026
Saboda muhimmancin godiya a Al-Qur’ani mai girma, akwai surori biyar da Allah ya buɗe da godewa kansa. Allah baya amfanuwa da komai daga gare mu, haka kuma baya cutuwa da komai daga gare mu, amma yana son godiya. Har ya ce idan muka gode masa zai ƙara mana. Godiya hali ne mai kyau kuma tana kawo alheri mai yawa.
Akwai wasu kalamai da ake kira "Magic Words" in one of our nursery rhymes. Waɗannan kalaman sune:
1. Thank you
2. Please
3. Sorry
4. Excuse me
5. Pardon me
Saboda daɗin su da tasirin su ne yasa ake ce musu magic words. Duk fushin mutum idan aka gaya masa ɗaya daga ciki yakan lafa.
Amma waɗannan kalamai suna yi wa mutane da yawa wahalar faɗa. Ko abu mutum zai tambaye ka, babu please, babu “dan Allah”, babu komai. Zai zo kai tsaye ya tambaye ka kamar ya baka ajiya. Idan ka sani sai dai kawai ka danne haushi saboda amanar ilimi ka bayar.
Haka "excuse me", mutum zai gitta ka ko kallon ka ba zai yi ba. "Sorry" kuwa, idan mutum ya faɗa sai ya ji kamar tsoron ka yake ji. Sai mutum ya taka ka ya wuce wai ya ce "Bismillah". Ko ya hakan ya zama bada haƙuri ne, oho.
"Pardon me"? Ai kai ka san afuwa.
Haka "thank you". Za ka gama yi wa mutum abin da ya tambaye ka cikin rashin ladabi, idan ka gama babu godi b***e "na gode".
Idan halin ka ne faɗan waɗannan kalmomin, kuwa sai mutane su ga kamar you’re weak ko tsoron su kake ji. Saboda wannan rashin tarbiyya ya zama norm a society ɗin mu.
A 2021 na taɓa fama da migraine mai tsanani. Ina Yobe then, sai na zo Kano Premier Clinic dan ganin likita. His name was Dr. Farouq, if I recall correctly. We discussed a lot, about many things.
Bayan na gama consulting ɗin sa zan fita daga office ɗin sa sai na ce "Thank you." After saying "you’re welcome", sai ya tambaye ni:
"Amma kai ba Bahaushe bane ko?"
Na tambaye shi me yasa ya ɗauka haka. Sai ya ce min ba halin mutanen mu bane godiya, especially idan s**a ga kuɗi s**a biya aka musu service. Yace halin ƙabilu ne, how he wish our people are like this.
Na ce masa haka ne, amma a Kano aka haife ni, a nan na girma. Kawai dai upbringing ne ya bambanta. Sauka a daidaita sahu, thank you, ka aiki almajiri, thank you, someone complained about something, sorry, wani sa'in ma kai ka yi wa mutum abun kirki, na gode. Komai dai haka komai dai haka.
Ƙabila ne zaka yi wa abu, something very little to you, after many days idan ya ganka a hanya zai ce maka:
"Thank you for the other day."
Especially Igbo people.
Lokacin muna yara idan aka aike mu provision store siyan abu, idan mun gode wa mai shago abin har mamaki yake bashi saboda ya saɓa da al’ada.
Har yanzu idan na je provision store aka zo da ƙaramin yaro ko yarinya da ya fara wayo, nakan siya musu alawa. Wanda ya zo da yaron ba zai ce masa ya gode ba, shima yaron ba zai faɗa ba. Wani lokacin ma sai kai ka koya wa yaron ka ce:
“To baka ce na gode ba?”
A shekarar da na zauna a Ɗorayi, ƙani na Walidi ya je makaranta. Bayan wasu watanni ya dawo, sai ya tarar akwai wasu da nake hira da su. Kullum idan yazo kafin ya zauna sai ya ce:
"Sannun ku, ina wunin ku?"
Tunda ya ga da yayansa suke zama.
Su kuma suna ganin abin is very absurd, even uncool. Daga baya dai ɗaya daga cikinsu ya tara ƙarfin hali, (ko rashin kunya) ya ce wa ƙani na:
"Me yasa kake wani gaishe mu idan ka zo? Ni ai ko baban mu bana gaisawa da shi bayan na ce masa barka da asuba. Babar mu kawai nake gaisawa. Gaisuwa ai yawa ne, tsohon yayi ce."
Me and Walid were shocked. Our jaws practically dropped.
Na kula da wani abu a social media communities, especially Forex, Crypto da Tech. Mutum zai kawo opportunity wanda kowa zai amfana da shi, sai a cika shi da tambayoyi; lazy, stupid questions. Ya amsa, mutane su amfana, amma babu ko "thank you".
Wadanda ma s**a mora quietly, ko kallon sa ba zasu yi ba.
Opportunity ɗin da he can decide not to share. He gains $0 from sharing it, but he did anyway, sannan ƙarshen abin ya zama heartache. Some people are very addicted to receiving but too lazy to give even a thank you, that is why they'll remain poor and miserable.
Har gobe abin da yake bani mamaki shine yadda mutumin Arewa yake ganin ya fi kowa tarbiyya.
Duk da haka akwai rare people masu godiya.
Misalin su shine wannan ɗalibin nawa. Duk milestone ɗin da yayi a trading sai ya tuno ni. Withdrawal ne, payout ne, setback ne, progress ne; zai gaya min, ya yi min addu’a ni da iyayena, ya gode min.
Ba kowanne ɗalibi bane yake haka.
Ni kuma duk lokacin da yayi haka, I make sure I share helpful insights da zasu sa rayuwar sa da trading ɗin sa su ƙara kyau. Ba hali na bane gatekeeping to the right people, especially mutane irin shi.
Shi yasa bana gajiya da answering his questions, telling him what he didn’t ask, and enlightening him, bayan kusan shekara ɗaya da graduation ɗin sa daga academy. That is why he's a maestro in fundamental analysis. Yana daga cikin top fast learners a Age Fx Alumni circle. Good in technicals, even better at fundamentals.
Human beings naturally invest more into appreciative people. It's not favoritism, it's reciprocity.
Yana daga cikin ɗaliban da muka yaye a Age Fx last year, Batch 9. He is a genius. Tun kafin ya samu certificate of completion ya fara hitting 60% WR, withdrawals, har da payouts.
Yana da himma, shi yasa ya samu abubuwa da yawa a trading career ɗin sa. Kuma zai samu fiye da haka, lokaci ƙadan mai zuwa zai tabbatar da haka.
Me ya kawo haka?
Godiya da kyautata mu’amala da mentor har ya ja ka a jiki.
Ɗaya daga cikin abubuwan da s**a bambanta mentorship da tutorship shine mentorship is a lifelong journey da kuma close marking. Kana buƙatar kyautata mu’amala da mentor ɗin ka, ka masa close-marking. Amma baza ka iya hakan ba If you're I'll-mannered.
Mentorship baya ƙarewa muddin mentor ɗin ka yana raye kuma kana da hankali.
Yanzu zaka gama mentoring mutum, daga baya ya koma gefe yana zaginka. Ko kuma ya raina ka saboda ya fara samun ƴan kuɗi da glitters, yaga ya taka wani mataki da ka cicciɓa shi zuwa gare shi, matakin da kai tuni ka wuce kafin ya fara trading
Few students get sense like this one.
Again, be saying thank you. It will not kill you.
In fact, it’ll do the opposite.