Guidance and counseling with Aliyu

  • Home
  • Guidance and counseling with Aliyu

Guidance and counseling with Aliyu Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Guidance and counseling with Aliyu, Consulting Agency, No 1929 Sheka Gari, Mundadu Sharada phase 3, Kumbots L. Govt. Kano, .

Helping individuals achieve emotional well-being, academic success, and positive decision-making, with Counselor Aliyu Harazimi

Muna taimaka wa mutane su sami nutsuwa ta zuciya, nasara a karatu, da yanke shawara mai kyau.

22/06/2026
ZAMAN UWAR MIJI DA MATAR ƊA  PART 2  UWAR ƊA:- ki sani cewa idan kikayi hakuri kika kau da Kai wajen sa baki cikin tafiy...
19/06/2026

ZAMAN UWAR MIJI DA MATAR ƊA

PART 2

UWAR ƊA:- ki sani cewa idan kikayi hakuri kika kau da Kai wajen sa baki cikin tafiyar da harkokin cikin gidan Ɗanki, to tabbas za ki nemawa Ɗanki rayuwar farin ciki da soyayya a gidanshi, yawan shiga harkokin cikin gida da iyaye mata keyi Yana haifar da rashin fahimtar juna da lalata rayuwar auren Ɗanki idan Akai rashin sa'a hakan ya zama sanadin samun sabanin uwa da Ɗa.

A wasu lokutan iyaye Mata suna shiga lamirin gidan Auren Ɗansune, wai don su samar masa da kwanciyar hankali, nutsuwa,da Jin dadin zamanshi musamman idan matarshi ta gaza hakan, sun manta hakan shi yake kawo fitina da samun sabani a zaman takewar iyali. Mai makon sa baki kamata yai ku yi masa addua da nasiha akan ya kula da gidanshi ya sauke nauyi hakkin da Allah ya dora masa, ku kau da kai kamar yadda iyaye maza keyi karki maida matar Ɗanki abokiyar zaman ki.

UWAR MIJI KO DANGIN MIJI:- ku sani duk wata mace DANGIN MIJI CE , Kuma in muna raye nan gaba zata zama UWAR MIJI, abinda kuka yiwa yar wasu haka za ayiwa taku idan taje hannun wasu, ku zauna da yan uwanku mata da Amana ku kyautata se Allah ya sa albarka arayuwar iyalanku.

Abin yana da ciwo ko takaici a ce wata tazo haka siddan Rana tsaka ta Auri Ɗanki ko Dan uwanku Amma se yadda tayi dashi, Allah sarki!! Tarihi ne ya mai-maita kanshi, wata ta ce min: " yaranne yanzu basu da kirki, ba haka muka zauna da surikanmu ba" idan kida ya canza dole rawa ta canza, karki manta a wancan lokacin kunya ta taka muhimmiyar rawa, sannan ana ganin girama, kin tabbata wannan kunyar akwaita a idon yaran yanzu kuwa? Amsamin wannan tambayar.

Ina baki shawar ki zauna da su da sifar girma kiyi hakuri, badan tsoro ba sedan zaman lafiyar ɗanki, duk da nasan ba duka aka hadu aka zama dayaba, idan kin samu SIRIKA mai tarbiyya da kirki ki zauna da ita a matsayin Sirika ki rike Amana, kisa kunya ta gudana a tsakaninku kar kiyi sakacin da ze sa ta kawo wasa ko raini a tsakaninku.

@ Aliyu Harazimi Ishaq

ZAMA DA SIRIKA: MA'ANA UWA DA MATAR ƊAPART 1   A yau ɗaya daga cikin matsalolin da ake yawan samu a gidajen aure ita ce:...
03/06/2026

ZAMA DA SIRIKA: MA'ANA UWA DA MATAR ƊA

PART 1

A yau ɗaya daga cikin matsalolin da ake yawan samu a gidajen aure ita ce:- rashin fahimtar juna tsakanin uwa da matar ɗanta. Wasu gidaje sun rasa zaman lafiya ne saboda saɓani tsakanin waɗannan mutane biyun da ya kamata su zama tushen soyayya da haɗin kai a cikin iyali.

UWA ki sani cewa matar ɗanki bata zo don ta ƙwace miki ɗa ba, ta zo ne don ta taimaka masa ya gina rayuwarshi.

KA KEMA MATA ki sani cewa uwa ce ta wahala wajen rainon Danta, ta tarbiyantar dashi har ya zama mutum Abin sha'awa, gashi yau kin aureshi na haneki da shiga tsakaninshi da mahaifiyarshi kar ki sa ya saba mata sannan karki rabashi da Yan uwanshi.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

"KUMA KU KYAUTATAWA IYAYE."(S. Baqra 83)

Annabi ﷺ ya yi umarni da KUYI KYAKKYAWAR MU'AMALA DA MATANKU, TARE DA TAUSASAWA DA GIRMAMA SU.

Abin takaicine aga uwa tana kallon matar ɗanta a matsayin abokiyar hamayya, ko kuma wasu matan auren su dauki surukarsu a matsayin wadda take son tarwatsa rayuwar aurensu. Irin wannan tunani yana haifar da zargi, ƙiyayya da samun saɓani, ya haifar da gaba.

ABUBUWAN DA ZA SU KAWO ZAMAN LAFIYA TSAKANIN UWA DA SIRIKA

1. GIRMAMA JUNA

Ganin girman juna shi ne ginshiƙin kyakkyawar alaƙar dake tsakaninku, idan uwa ta girmama matar ɗanta, ita ma za ta girmamata. Amfani da kalmomin masu daɗi da kyakkyawar mu'amala suna kawar da matsaloli.

2. GUJEWA TSOMA BAKI FIYE DA KIMA

Ba kowace matsala ta ma'aurata ya kamata a shiga cikinta ba. Wani lokaci ki bada shawara cikin hikima ta fi tsawa da hukunci amfani.

3. YIN KYAKKYAWAN ZATO

Yawan zargi da mummunan zato suna lalata kyakkyawar alaƙa.

4. HAKURI , YAFIYA DA KAWAICI

Kowa yana da kuskure. Uwa ta yi haƙuri da sirika, sirika ma ta yi haƙuri da uwa. Haƙuri yana kashe wutar fitina, Sannan ku sani yafiya tana ƙara soyayya.

Alkamin Baban Amina
Aliyu Harazimi Ishaq Fagge

🌿ALAƘAR DA KE TSAKANIN MACE DA NAMIJI🌿   Allah Maɗaukakin Sarki ya halicci mace da namiji domin su zama masu cika junans...
31/05/2026

🌿ALAƘAR DA KE TSAKANIN MACE DA NAMIJI🌿

Allah Maɗaukakin Sarki ya halicci mace da namiji domin su zama masu cika junansu, ba masu gogayya da juna ba. Kowannensu yana da irin gudummawar da yake bayarwa wajen gina iyali da al'umma. Namiji yana buƙatar kulawa, fahimta da kwanciyar hankali, haka ita ma mace tana buƙatar ƙauna, kariya da girmamawa. Idan aka gina alaƙarsu a kan mutunta juna, gaskiya da tausayi, rayuwa kan kasance mai daɗi da albarka.

A cikin rayuwar aure ko neman aure, kyakkyawar sadarwa da sauraren juna suna daga cikin manyan ginshiƙan samun zaman lafiya. Lokacin da mace da namiji s**a fahimci cewa nasarar ɗaya tana da alaƙa da nasarar ɗayan, sai su daina neman kuskure a junansu, su fara neman hanyoyin da za su tallafa wa juna. Wannan fahimta ce da ke ƙarfafa soyayya, amana da zaman lafiya mai ɗorewa.

Manzon Allah (SAW) ya yi umarni da kyautata mu'amala ga mata, kuma ya nuna cewa mafi alherin mutane su ne waɗanda s**a fi kyautata wa iyalansu. Wannan yana nuna muhimmancin girmamawa, tausayi da adalci a tsakanin mace da namiji. Haka kuma mace ta gari tana ƙoƙarin kiyaye mutuncin gidanta da kuma taimaka wa mijinta a cikin al'amuran rayuwa.

Darasi: Alaƙar mace da namiji ba ta ta'allaka ga soyayya kadai ba; tana buƙatar haƙuri, yafiya, fahimtar juna da kuma aiki tare domin gina makoma mai kyau.

📌 Domin samun ƙarin rubuce-rubuce da shawarwari kan zamantakewa, tarbiyya, aure da zaman lafiyar iyali, ku yi Following, Like da Share shafinmu na Guidance and counseling with Aliyu.

Alkalamin Baban Amina 🖊️ 🖊️ 🖊️
Aliyu Harazimi Ishaq Fagge

Allah Ya saka da alheri.

29/05/2026
26/05/2026

Ga addu’a mafi falala a ranar Arafah kamar yadda Annabi ﷺ ya koyar:👇👇👇

لَا إِلٰهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ

LA'ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR.

Annabi ﷺ ya ce wannan ita ce mafi alherin addu’ar da shi da annabawan da s**a gabace shi s**a yi a ranar Arafah.

Sannan ana yawaita:
Istigfari
Salatin Annabi ﷺ, da
Karatun Al-Kur’ani.

Sanna kuyi addu’ar neman:
gafara
lafiya
arziki
shiriya, da
kyakkyawan ƙarshe.

Ga wata kyakkyawar addu’a ta neman alheri:

رَبَّنَا آتِنَا فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً وَفِي الْآخِرَةِ حَسَنَةً وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ

RABBANA ATINA FID DUNIYA HASANATAN WAFIL AKIRATI HASANATAN WAKINA AZABAN NAR

Allah Ya karɓi ibadunku da addu’o’inku.

Alkalamin Baban Amina
Aliyu Harazimi Ishaq Fagge
(Ala-ala)

DANA SAN HAKA AUREN YAKE GASKIYA DA BANYIBA   Yawancin masu fadin irin wannan magana suna fadin ta ne saboda wasu matsal...
22/05/2026

DANA SAN HAKA AUREN YAKE GASKIYA DA BANYIBA

Yawancin masu fadin irin wannan magana suna fadin ta ne saboda wasu matsaloli da s**a tarar a rayuwar auren, kamar:👇👇👇

🔸Rashin fahimtar juna tsakanin ma’aurata.
🔸Yawan rigima ko rashin mutunta juna.
🔸Matsin tattalin arziki da nauyin iyali.
🔸Rashin samun kwanciyar hankali a gidan Aure.
🔸Zaben abokin zama ba tare da bincike da shawara ba.
🔸Tsananin kishi, fushi, ko rashin hakuri.
🔸Wasu kuma saboda sun shiga aure da tsammani mai yawa fiye da yadda rayuwar ta ke.
🔸Saboda haka sai mutum ya fara nadama yana cewa: “Da na sani da ban yi aure ba” ko “Da ana raba mace rabi da an bani rabin.”

Amma a gaskiya, irin wannan magana ba ita ce mafita ba. Aure sunnah ne kuma wata babbar ni’ima ce idan an gina shi akan:👇👇👇

▫️Addini.
▫️Hakuri.
▫️Tausayi.
▫️Kyakkyawar fahimta.
▫️Yafewa juna.

Allah Madaukakin Sarki ya ce " ya sanya soyayya da rahama tsakaninku (ma’aurata.")

MAFITAR IRIN WANNAN HALI ITA CE:👇👇👇

▪️A rage yawan fushi da gaggawar yanke hukunci.
▪️A rika tattaunawa cikin nutsuwa.
▪️A tuna kowa yana da kuskure.
▪️A nemi shawarwari daga malamai ko masu hankali.

A kara addu’a da neman taimakon Allah
Namiji da mace su san cewa aure ba rayuwa ce ta jin dadi ba, akwai gwaji da hakuri a ciki,
Wasu lokuta mutum yana fadin haka ne cikin bacin rai ba wai yana nufin ya tsani auren ba, Idan aka gyara mu’amala da fahimtar juna, sau da yawa irin wannan magana tana gushewa.

Allah ya sakawa iyayenmu da Alkhairi mu Kuma ya karawa gidajenmu Albarka, yayiwa zuriarmu Albarka.

Daga Alkalamin:- Baban Amina 🖊️🖊️🖊️
Aliyu Harazimi Ishaq Fagge
(Ala-ala)

21/05/2026

Zaku iya turo tambayoyinku ko Damuwa da take bukatar shawara mai kyau domin warwarewa, ashafin
Guidance and counseling with Aliyu

20/05/2026

Domin warware muku wata Matsala da taki-ci-taki-cinyewa,
ku Aiko mana da da ita domin samun mafita cikin salo Mai kyayatarwa.

💥HANYOYIN BUNKASA SO DA KAUNA TSAKANIN "YAN-MATA / ZAURAWA DA MASU NEMAN AUREN SU💥Guidance and counseling with Aliyu 1️⃣...
19/05/2026

💥HANYOYIN BUNKASA SO DA KAUNA TSAKANIN "YAN-MATA / ZAURAWA DA MASU NEMAN AUREN SU💥

Guidance and counseling with Aliyu

1️⃣:- KYAKKYAWAR DABI'A:- Namiji yana son mace mai nutsuwa, girmamawa, ladabi, da iya magana, ki sani yawan faɗa, raini, ko gardama suna rage so kauna.

2️⃣:- GASKIYA DA RIKON AMANA:- Idan ya fahimci ke mai gaskiyace, kuma kina kiyaye sirrinsa, hakan yana kara masa yarda da ke a cikin zuciyarshi.

3️⃣,:- KULAWA DA KYAKKYAWAR FAHIMTA:- Ki rika nuna kina sauraronshi idan yana magana, ki tambayi halin da yake ciki lokaci zuwa lokaci cikin mutunci ba tare da kin matsa masa ba.

4️⃣:- ADDU'A DA KYAKKYAWAR NIYYA:- Soyayya mai albarka tana ƙaruwane idan kuna addu’a, ki roƙi Allah ya haɗa zukatanku idan da alkhairi Allah ya tabbatar Sannan ya baku zaman lafiya.

5️⃣:- KULA DA TSAFTA:- kamshi mai kyau, da tsaftatacciyar shigar mutunci suna ƙara burgewa sosai.

6️⃣:- GIRMAMA IYAYENSHI DA ABOKANSHI:- Namiji yana farin ciki idan ya ga mace tana girmama waɗanda yake ƙauna.

7️⃣:- KIYAYE IYAKOKIN ADDINI A SOYAYYA:- Duk soyayyar da aka gina cikin tsoron Allah ta fi samun ɗorewa da ganin mutunci juna.

8️⃣:- YAWAN YABAWA :- Namiji ma yana son a yaba masa idan ya yi abu mai kyau, kalaman ƙarfafawa suna ƙara kusantar zuciya yaji baida wacce ta fiki a zuciyarshi.

Baban Amina 🖊️🖊️🖊️
Aliyu Harazimi Ishaq Fagge
(Ala-ala)

Address

No 1929 Sheka Gari, Mundadu Sharada Phase 3, Kumbots L. Govt. Kano

Telephone

+2348092516853

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Guidance and counseling with Aliyu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Guidance and counseling with Aliyu:

Shortcuts

  • Want your business to be the top-listed Business?

Share