21/10/2023
DUK ZUCIYAR MUMINI SAI TA TAUSAYAWA SU MALAM HARUNA ABBAS ðŸ˜
SHEKARU 11 GWAMNATI NA TSARE DASU BISA ZALUMCI
ZA SU KOMA KOTU RANAR LITININ MAI ZUWA. 23/10/2023
MALAM HARUNA ABBAS ALI, MALAM IBRAHIM HUSSAIN DA MALAM ADAM SULAIMAN (Hujja).
Daga Ado Sahifa Zaria
Mu sanya su cikin addu'oin mu, shekarun su goma sha daya a tsare a gidan yari ba tare da sun aikata laifin komai ba. Ibrahim Hussain aka fara k**awa a gidan sa a garin Kaduna. Sannan sai aka Mal Haruna Abbas a airport na Mal Aminu kano a garin Kano bayan dawowar sa ziyara kasar Lebanon . an k**a Adam Sulaiman a garin Lagos inda yake sana'sa.
Su waye s**a k**a su , kuma meye dalilin k**a su.
Jami'an tsaro na DSS sune s**a k**a su. suna tuhumar su da mu'amala da hizbullah na Labanon da kuma kasar Iran. da tuhumar cewa sunje Iran da Labanon sun koyo ta'addanci zasu zo su koyar da yan uwa na Nigeria. kuma suna tuhumar su da cewa suna da taswirar ofishin Jakadancin haramtacciyar kasar Isra'ila da America. kuma suna shirin kai ma ofishin Jakadancin America da* *haramtacciyar kasar Isra'ila hari. suna so ne su Mal Haruna Abbas su amsa cewa Jagora Sayyeed Zakzaky (h) ne ya tura su domin su koyo ta'addancin*.
*Jami'an leken asiri na haramtacciyar kasar Isra'ila (MOSSAD) sun zo har Nigeria, sun gallaza ma Mal Haruna Abbas azaba sosai domin ya amsa cewa Jagora Sayyeed Zakzaky (h) ne ya tura su amma yace sam ba haka bane . Jami'an (CIA) na America suma sun gallaza wa Mal Haruna Abbas azaba mai tsanani da shocking na wutar lantarki. da sanya shi a underground cell a cikin duhu na tsawon shekaru uku da sarqa a wuyan sa da hannu. ga beraye masu cin naman mutane .basa bashi abinci sai sau daya a kowacce rana. sunyi masa azaba nau'i daban daban . s**an ce , wai saboda wannan* *mutumin yake nema ya hallaka kansa. suna nufin Jagora Sayyeed Zakzaky (h) . shi kuma sai yace akan in amsa wannan wallahi sai dai ku kashe ni. sunyi masa alkawura iri iri zasu bashi kudade masu yawa zasu gina masa gidaje a duk kasar da yake so . yace bai yarda ba. sai s**a ce tunda duk bai yarda da tayin da s**a yi masa ba . toh zasu kashe Ibrahim Hussain da Adam Sulaiman. yace suyi hakuri kar su kashe su gara dai shi su kashe shi. sai s**a ce to ga takarda ya sanya hannu zasu kaishi America guntanamo bay suyi masa shari'a a can . sai yace ya yarda. amma da lauyansa yaji labari sai yace shi bai yarda ba. a hakan dai s**a ci gaba da azabtar dashi*
*Wannan ya sabbaba Mal Haruna Abbas ya samu lalurori iri iri sak**akon azabtarwar da suke yi masa . kuma basu bashi magani kuma basa yarda a kai masa. baya ga* *lalurar hawan jini , ciwon kashi chronic asma da sauran cotuttuka sai da ya samu mummunar matsalar ciwon ido , ya zamto baya gani sosai. sai da kyar s**a yarda aka yi masa aiki a ido.*
*Da aka shigar da kara sai Amurka da Isra'ila s**a dauki lauya .kuma duk da hakan Amurka da Isra'ila s**an turo wakilan su fararen fata daga America da Israila idan za'a shiga kotun . kuma s**an zo ne a bayyane ba a boye ba. don haka yadda suke so haka ake gudanar da shari'ar. ranar da suke so a sanya ita ake sawa. kuma sun hana alkali ya saurari maganar beli. idan yace zai bada beli sai su sanya a canza kotun. haka dai aketa yi tsawon shekaru goma sha daya.*
*gashi kuma kullum rashin lafiyar Mal Haruna Abbas sai karuwa takeyi har ta kai ga baya iya tsayuwa a kotun sai dai ya zauna. wani lokaci kuma yakan yi amai a kotu saboda gwajab gwajab din motar da ake dauko su zuwa kotun. domin tantagayyar karfe suke zama a cikin motar. da handcuff idon su kuma a rufe da kyelle an daure. har rokon Alkali Mal Haruna Abbas yayi akan cewa a daina kawo shi kotun domin yana shan wahala k**ar ransa zai fita Alkali yace a'a bai yarda ba.*
*A cikin wannan hali Mal Haruna yaji labarin waqi'ar Qud's wadda Sayyeed Ahmad, Hamid da Mahmud s**a yi shahada. ya kuma ji labarin waqi'ar Buhari (l.a) inda Ali Haidar , Hammad da Humaid da sauran yan uwa s**ayi shahada. ya kuma ji labarin abinda da ya faru da Jagora (h) da Umma Zeenat. da kuma kamun da akayiwa Sayyeed (h) da Ummah Zeenat aka tsare su da harbi a jikin su ga kuma matsananciyar rashin lafiya*.
*Mal Haruna Abbas ya rasa babban yayan sa da yake taimaka masa ako da yaushe. a cikin wannan halin ya rasa yayan sa mata guda biyu. dayar da ya barta karama har ta isa aure aka aurar da ita ta haihu yar data haifa ta rasu , itama ta rasu.*
*Abin tambaya ga yan uwa shine wai yanzu a ina iyalan Mal Haruna Abbas suke. bayan anyi waqi'ar Buhari (l.a) an rushe gidan da suke haya a Gyellesu. shekaru goma sha daya fa ba kwana goma sha daya bane. ba kuma wata goma sha daya bane. toh idan iyalansa basu da lafiya wa ke basu magani ko ya kaisu asibiti. wake biyan kudin makarantar yayan sa. wake baiwa iyalansa abinci. wake kula da tarbiyar yayan sa. garemu yan uwa mu sani laifin da su Mal Haruna Abbas s**ayi duk muma mun aikata shi kasancewar mu mabiya Mal Zakzaky (h). abinda ya samu su Mal Haruna Abbas yana iya samun kowa a cikin mu.*
*Shin dan uwa ka taba taimakawa su Mal Haruna Abbas, hadimin Jagora (h) koda da addu'a ne?*.
*ko ka san suna da haqqi akanka kuwa.*
*Mal Haruna Abbas comanda ne na Harisawa k**ar yadda Jagora Sayyeed Zakzaky (h) . ya taba fadi a taron yaumusshuhada'u a filin polo kusa da Hussainiyyah Zaria cewa : comandan Harisawan Mal Haruna Abbas dole ne ku sake shi. kuma Jagora (h) ya sanya Shaheed Hamza Yawuri yayi rubutu aka sanya a jaridu cewa a saki Mal Haruna Abbas. shin Harisawa suna taimaka masa ko suna kula da iyalansa kuwa ? amsa dai anan itace A'A. toh dan uwa a matsayin ka na Haris ka sani Mal Haruna Abbas yana da haqqi akanka koda kuwa na addu'ar Allah ya kubutar dasu ne. bare kuma iyalansa ma suna da haqqi akan dukkan wani haris da dukkan yan uwa.*
*Kamar yadda muka sani Jagora (h) ke daukar dawainiyar shari'ar su Mal Haruna Abbas da iyalansa. tun kafin waqi'ar Buhari (l.a) . toh har yanzu ma Jagora Sayyeed Zakzaky (h) shike daukar takalifin shari'ar su data iyalan sa.*
*Alhamdulillah a yanzu da suke tsare a gidan yarin Kuje. Jagora (h) ya kan aika masa da suturu da kuma kayan masarufi. musamman lokutan idoji da mauludoji. a lokacin Gadir Jagora Sayyeed Zakzaky (h) ya aika tawaga karkashin Jagorancin Sidi Munir sun shiga har gidan yarin sunyi walima tare dasu. a wannan Mauludin na bana har tawagar mawakan Ittihadusshu'ara aka tura har gidan yarin Mal Nasiru Fudiyya da Nura Shahidi s**ayi majalisi da walima tare dasu.*
*domin haka idan yan uwa sun yashe su , ko sun manta dasu . toh Jagora Sayyeed Zakzaky (h) bai yashe su ba, kuma bai manta dasu ba.*
*bal akwai dai dai kun yan uwa da s**an taimaka musu a lokuta daban daban.*
*Mu sanya su cikin addu'oin mu mu karanta musu Fatiha da salatin Annabi (s), muna rokon Allah ya kubutar dasu daga hannun wadannan miyagun azzalumai . Allah ya baiwa Jagora (h) da Ummah Zeenat lafiya ta musamman daga gareshi bi haqqi Imamul hujja (atfs).*