04/09/2026
*KATSINA STATE SPOWER, VALUNTARY AND PART-TIME ASSOCIATION* SANARWA TA MUSAMMAN KAN MASU AMFANI DA SUNAN ƘUNGIYAR S-POWER
Muna sanar da jama’a, musamman al’ummar Concern S-Power, Voluntary and Part-time teachers na Jihar Katsina da mai girma gwamanan Katsina Malam Dikko Umaru Radda PhD. CON ya maida Malamai na dindindin (Permanent), cewa
mun lura da wasu mutane da ke amfani da sunan ƙungiyar tare da gabatar da kansu a matsayin shugabanni ko wakilan S-Power, alhali ba sune Jagororinta ba kamar yadda muka sani.
Domin haka ne muke sanar da daukacin membobin Concern S-Power, Voluntary da Part-time da sauran al'umma cewa wannan ikirari da suke basu da hurumin sa daga jagororin kungiyar mu ta Spower,
Haka zalika muna bayyana ma al'umma cewa duk wani mutum da ke zuwa wurin wani jagora ko ɗan siyasa yana gabatar da kansa a matsayin shugaban S-Power matsawar ba Shugaban fannin Secondary bane watau Akilu Aliyu ko shugaban Spower Primary Samaila Rabiu Musawa bane to baya wakiltar ƙungiyar.
Ba za mu zauna muna kallon wasu suna amfani da sunan ƙungiyar da aka assasa tare da jajircewa da ƙoƙarin membobinmu ba, suna tafiya wuraren siyasa ko ganawa da shugabanni da sunan ƙungiyar, alhali ba sune jagororin wannan ƙungiya ba. Idan aka ci gaba da irin wannan hali, za mu ɗauki matakan da s**a dace ta hanyar doka domin kare mutunci da sahihancin ƙungiyar.
Muna kuma jaddada cikakken goyon bayanmu ga Mai Girma Malam Dikko Umar Radda, PhD, wanda ya mayar da mu cikin aikin koyarwa na dindindin (Permanent Teachers) bayan shekaru da dama da muka shafe muna aiki a matsayin Spower casual workers. Wannan alheri ne da ba za mu taɓa mantawa da shi ba.
Haka kuma, muna bayyana cewa Dr. Mustapha Muhammad Inuwa uba ne kuma jagora a gare mu. Saboda haka, muna matuƙar girmama shi tare da yaba masa bisa irin alherin da ya yi mana. Sai dai wannan ba ya ba kowa damar zuwa wurinsa ko wani jagora yana gabatar da kansa da wani mukami da ba shi da shi a cikin kungiyar mu ta Spower.
SHUWAGABANNIN DA AKA SANI SUNE KAMAR HAKA:👇👇
1. Akilu Aliyu shi ne shugaban ɓangaren Concerned S-Power Graduates, Voluntary and Part-time Association.
2. Sama’ila Rabi’u Musawa shi ne shugaban ɓangaren S-Power Primary
- Waɗannan ɓangarorin s**a kaɗai muke dasu kamar yadda kowa ya sani. Saboda haka, muna kira ga duk waɗanda s**a je gidan Dr. Mustapha Muhammad Inuwa suna gabatar da kansu a matsayin shugabannin S-Power, da su gaggauta janye wannan ikirari tare da bayyana wa jama'a cewa basu bane jagororin kungiyar kuma basu ikon wakiltar ƙungiya.
Muna kira ga daukacin membobin ƙungiyar da su ci gaba da kasancewa masu haƙuri, haɗin kai da bin doka, tare da kare mutunci da martabar S-Power, Valuntary da Part-time
Mun kafa ƙungiya ne domin haɗin kai, ci gaba da kare muradun mambobinmu, ba domin wasu su yi amfani da sunanta don biyan buƙatun kansu ba.
Ibrahim Kado
State PRO
Recruited Spower Graduates, Valuntary and Part-time Association