26/10/2026
KASUWANCI UKU (3) DA ZAKA IYA FARAWA DA NAIRA DUBU HAMSIN (50k) KACHAL
✓KASUWANCI NA UKU:
Wannan na maza ne zaka iya yi in kuma baka da girman kai. Shi ne zuwa kasuwannin kauye, zaka sha mamaki idan kana cikin birni yanda ake siyarda abubuwa da tsada. IDAN zaka dauki yar dubu hamsin dinka ka tafi kaje cin kasuwan kauye ka siyo yan kajin ka na dubu hamsin da yan sauran abubuwansu na kauye ka kawo su birni ka saida su.
Zakayi mamakin ribar da zaka ci. Zaka iya a duk rana in kana wannan ka ci ribar yar dubu biyar, dubu goma, a wata ka samu wata yar dubu dari biyu ko dubu dari uku. Ko mai aikin gwamnati bai isa ya fada maka ba. Kai ko dubu biyar, biyar ka ke samu in kaje ka ci kasuwan, idan ka lissafa dubu biyar sau talatin, dubu dari da hamsin (150k) Ka fadamun ma'aikatan gwamnati nawa ake biyansu dubu dari da hamsin duk wata.
✓KASUWANCI NA BIYU:
Shine packaging business. Wannan abu ne mai sauki in kana da wayau kuma kana da tunani. Abu ne zaka duba a unguwanku wanda mutane suke sun shi ko wata ta iya shi, ban ma ce ke ki yi ba, A'a ki nemi wacce ta iya wannan abun, kawai ke abun da zakiyi shine ki je ki siya ledoji, ko robobi, ko goruna da sticker, ki je ki siya wannan abun a wurinta ki zuba ki manna sticker ki ringa bin WhatsApp dinki kina talla, wasu ki nemi shagunan irin provision store dinnan manya ki je ki kai masu suna saida maki, ke dai kawai abinda za kiyi shi ne packaging kawai. A wannan abin , akwai wacce na taba bata shawara, ta gwada yin wannan kasuwancin da naira dubu hamsin sai da ta maidashi naira dubu dari biyar (500k). Idan kuna sun jin labarin kuyi mun comment akan labarin In Shaa Allahu zan baku labarin yanda tayi anfani da packaging business da naira dubu hamsin (50k) ta maidashi naira dubu dari biyar (500k).
✓KASUWANCI NA FARKO:
Shi ne sayar da gwanjo, ba cewa nayi kaje ka sayi dilan gwanjo ba. A'a ka nemi kasuwan gwanjo mafi kusa da unguwanku ko garin ku. Kaje akwai yanda suke yanka dilan gwanjo a na zaba. In kaje da naira dubu hamsin dinka ina fada maka zaka zaba kaya da yawa, wanda idan har kasan yanda zaka sai da su a cikin kankanin lokaci wannan dubu hamsin din zata iya koma maka naira dubu dari biyar (500k).
Ku rubuta mana naku kasuwancin da kuke ganin za'a iya farawa da naira dubu hamsin (50k) a comment section.