13/04/2018
Watarana Umar Bn Ubaidullah ya fito zuwa lambunsa,a lokacin da yazo kusa da kofar shiga lambun, sai ya ga wani yaro a zaune a gefen lambun yana cin abinci, yaron yana cikin cin abincin sai wani kare yazo ya rika matsowa kusa da da shi, sai yaron ya dauko loma 1 ya ba karen, sannan shi ma ya ci loma 1, haka yaron ya rika cin loma 1 yana bawa kare loma 1, sai Umar ya tsaya yana kallo yana mamaki.
Sai Umar ya tambaye shi: "WANNAN KARENKA NE?".
Sai yaron ya ce: "A'A".
Sai Umar ya ce: "To me yasa naga ka ba shi rabin abincinka?".
Sai yaron ya ce: "Idan wani ya ganni ina cin abinci, to ai dole inyi masa Bisimillah".
Sai Umar ya yi mamakin yaron, sai ya tambayi yaron: "Kai ďa ne ko bawa?".
Sai yaron ya ce: "Ni ďa ne daga cikin bayin da suke aiki a wannan lambun".
Sai Umar yayi tafiyarsa, can sai ya dawo ya yiwa yaron busharar ya 'yanta shi, kuma ya ba shi wannan lambun cikin farin ciki da yarda da shi.
Sai yaron ya ce: "TO KA ZAMA SHAIDA CEWA, NA BAIWA TALAKAWAN MADINAKYAUTAR KAYAN MARMARIN DA SUKE CIKIN LAMBUN".
Sai Umar ya yi mamaki, sannanya ce masa: "YANZU KAYI WANNAN KYAUTA DUK DA TALAUCIN DA KAKE CIKI, DA BUKATUWAR DA KAKE CIKI?".
Sai yaron ya ce: "INA JIN KUNYAR ALLAH (S.W.T) YA BAN WANI ABU, KUMA IN ZO INYI MASA ROWA".
Ya tabbata a hadisi ingantacce cewa, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: "Babu wata rana da za ta bullo, face sai Allah (S.W.T) ya wakilta wasu Mala'iku guda biyu, daya daga cikinsu yana addu'a yana cewa, "YA ALLAH KA MAYARWA DA MAI KYAUTA ABIN DA YABAYAR", na biyu kuma yana cewa, "YA ALLAH KA TOZARTAR DA DUKIYAR MAI ROWA".
YAA ALLAH (S.W.T) KA BAMU DAMAR YIN KYAUTA DON ALLAH CIKIN FARIN CIKI DA ANNASHUWA.
Juma'at Kareem