19/02/2025
MATASHI, KA FARKA!
Akwai wasu nau’o’in Ayyuka guda biyu da, idan ba ka yi hankali ba, za su yi maka kisan gilla fiye da shan guba da nono. Wadannan su ne Zina da Shaye-shaye. Ba wai kawai za su kassara lafiyar jikinka ba, a’a, za su murƙushe rayuwarka tamkar Ƙatuwar Mota katafila tana ragargaza gini. Sannan za su jefa ka cikin talauci kamar yadda ake jefa guga cikin rijiya—ba a jin ɗuriyarka, ba a ganin hayaniyarka, sai dai a ji labarinka a cikin wani shiru da kayi mai cike da nadama.
Idan ba ka iya fin ƙarfin sha’awarka ba, to kuwa sai ta fi ƙarfin ka!
Matakin farko na nasarar namiji shi ne ya mallaki zuciyarsa kafin zuciyarsa ta mallake shi. Kada ka zama dolon da mata ke amfani da jikinsu wajen raba ka da kuɗin da ya kamata ka gina rayuwarka da su.
Kai wai jakin ina ne? Da zaka iya ɗaukar dubu goma ko fiye, ka bawa mace kawai don zina ta mintuna goma?
Kana zaton ka burge kanka?
Afala Ta’aƙilun? – Kai dai baka hankalta ba?
Ka san cewa sinadaran da suke fita daga jikinka yayin da ka zubar da maniyyi daga kwakwalwarka suke? Kuma su ne ke taimakawa wajen tunani mai kyau da tsara rayuwarka? Wato a takaice, kana ragewa kanka wayo da basira ne!
Kayi ƙoƙari ka koyi danne sha'awarka wallahi sai ka fi kwarjin da muhibba a idon duniya.
Afala Tazakkarun? – Kai, baka yin tunani kuwa?
A yanzu kana ganin wayo ne ka biya karuwa kuɗi, ka zubar da sinadaran kwakwalwarka a banza, sannan ka ƙara da bata lokaci? Wato kai ne "ƙaramin jaki!" (Sagirun Himarun).
Wane irin namiji ne kai wanda mata ke yawo da hankalinsa kamar agogo, suke kunna ka da sha’awa, su kashe ka da zina ta mintuna goma?
Matashi, ka farka!
Wallahi, idan har kana so ka gina rayuwarka da daraja, ka koya yadda zaka fi ƙarfin sha'awarka. Duk wani namiji da ya iya wannan, rayuwarsa sai dai a yi masa kishi!
Ka fi ƙarfin sha’awarka kafin ta fi ƙarfin ka!
Wasallam
Haris a haris
Ayi sharing.