Hausawa

Hausawa Entertainment

16/02/2026

Celebrating my 11th year on Facebook. Thank you for your continuing support. I could never have made it without you. 🙏🤗🎉

KA DAINA JIRAN MAI TAIMAKO... WALLAHI BABU WANDA ZAI ZO.Ina so na gaya maka wata gaskiya mai daci wacce za ta iya sa ka ...
16/02/2026

KA DAINA JIRAN MAI TAIMAKO... WALLAHI BABU WANDA ZAI ZO.

Ina so na gaya maka wata gaskiya mai daci wacce za ta iya sa ka kuka, amma kuma ita ce za ta Tseratar da rayuwarka.

Kullum kana tashi da safe kana cewa: "Ina ma wane ya taimake ni", "Ina ma Kawuna mai kudi ya bani jari", "Ina ma na hadu da wani Senator".

GASKIYAR MAGANA ITA CE:

Wancan Mai Kudin da kake kallo, shima yana fama da tasa matsalar da ta fi taka girma.
Yana fama da Lafiyarsa, ko Kasuwancinsa yana girgiza, ko wani family issue daban.
Bashi da lokacin da zai tsaya ya lura da Talaucinka domin shima yana kokarin kada ya talauce.
Duniya bata da lokacin share maka hawaye.

Sannan ka sani Masu kudi ba sa zuba jari akan Mabaraci, suna zuba jari akan Mai Hazaka.
Idan baka da komai sai Kuka da Roko, za su ba ka N5,000 su wuce.
Amma idan kana da Hikima, Fasaha, da Gaskiya, su da kansu za su neme ka.
Kada ka nemi kudi, ka nemi DARAJAR da za ta jawo kudin.

Bayan haka Ko da Allah Ya hada ka da Shugaban Kasa yau, idan Kwakwalwarka bata da abin bayarwa, gobe zai manta da kai.
Maimakon ka yi ta neman Number wayar wane, ka je ka gyara kanka ta yadda Wane din ne zai nemi number wayarka.

Ka sani :
Kai ne Mai Taimakon Kanka.
Hannunka, Kafarka, da Kwakwalwarka sune Kawunnan da Allah Ya baka.
Ka Tashi ka yi aiki.
Ranar da ka daina Jiran Wani, ranar ce arzikinka zai fara.

Allah yasa mudace🤲

IDAN KANA SON ZAMA MAI KUDI, DOLE KA YARDA KA RASA WADANNAN ABUBUWAN 10.Arziki ciniki ne... Kana bada wani abu, ka karbi...
16/02/2026

IDAN KANA SON ZAMA MAI KUDI, DOLE KA YARDA KA RASA WADANNAN ABUBUWAN 10.

Arziki ciniki ne... Kana bada wani abu, ka karbi wani.

Dan uwa,
Hanyar Arziki bata da dadi a farko. Dole sai ka biya Farashin da sa'anninka suke tsoron biya.

Ga abubuwa 10 da dole ka yi bankwana da su idan kana so ka daina talauci:

1. HAKURIN JIN DADI:
Dole ka daina biyan bukatun Yanzu-Yanzu.
Ka daina siyan waya mai tsada alhali baka da fili.
Ka koyi Saving da Investing kafin ka fara Spending.
Barin jin dadi yau, shine jin dadin gobe.

2. FITO DAGA COMFORT ZONE:
Arziki baya cikin daki mai sanyi inda babu kalubale.
Dole ka fito ka rungumi duk wata kalar gwagwarmaya.
Duk abin da kake tsoron yi kamar Business, Travel, Sabon Skill, nan ne kudin yake.

3. RAGE "SHA'ANIN MUTANE:
Idan kana son yin kudi, dole ka rage zuwa kowane biki, suna, da taron da ba zai kara maka ilimi ko kudi ba.

4. RABUWA DA ABOKAN BANZA:
Idan abokanka mutane ne da basu da Ambition, dole ka rabu da su.
Idan kana tafiya da mutum 4 marasa kudi, kai ne na 5.
Nemi wadanda s**a fi ka ilimi da kudi, su ne za su ja ka sama.

5. RAGE LOKACIN WASA:
Duk lokacin da ka bata wajen kallon Series ko wasan Game, lokaci ne ka cire daga ginin rayuwarka.
Mai neman kudi bashi da Weekend. Kullum aiki ne.

6. RASHIN TABBAS:
Aikin Gwamnati ko Salary yana da dadi saboda Tabbas shi Security ne.
Amma Arziki yana cikin Business wanda bashi da tabbas.
Dole ka cire tsoron In na yi asara fa? ka rungumi kasada.

7. RAGE BARCI:
Ba wai ka kashe kanka ba, amma dole ka rage barci fiye da mai cin albashi.
Lokacin da kowa yake barci, lokacin ne masu kudi suke karatu ko tsarawa.

8. DAINA BURGE MUTANE:
Dole ka sadaukar da ego dinka.
Ka daina siyan kaya don Deserving, ka sayi kaya don Investing.
Gwara a gan ka da tsohuwar mota amma kana da Plot 10, da a gan ka da sabuwar mota kana haya.

9. KASHE GIRMAN KAI:
Dole ka zama mai tawali'u.
Ka koyi ilimi a wajen wanda ya fi ka kudi ko da ya yi jikanka.
Ka yarda da kuskure, ka karbi gyara. Masu girman kai basu da girma.

10. HAKURI DA JINKIRI:
Arziki na gaskiya baya zuwa dare daya.
Dole ka sadaukar da Gaggawar da ke ranka.
Ka bi matakala daya bayan daya har ka kai.

TAMBAYA GA MAI KARATU:
A cikin wadannan guda 10, wanne ne YA FI MAKA WUYA ka daina?

Allah ya azurta mu da Halal🤲

Address

21road Z Close House 10 Festac Town
Lagos

Telephone

+2348169600161

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausawa:

Shortcuts

Share